← Book details Gammon Rama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 21

Sashe 8

Gammon Rama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kawu Sani, Inna, Malam Hasan da Rakiya ne zaune a É—akin Inna. Kusan kowannansu fuskarsa a haÉ—e take babu walwala, Kawu Sani ya dubi Malam Hasan ya ce.
"Idan na fahimce ka Hasan, tun da har zaman can ya gagara za ka dawo nan gidanka wanda ka gada daga wurin mahaifinka?"
Malam Hasan ya gyaÉ—a kai ya ce, "Kawu a can É—in ne ba a samun cinikin faskaren sosai, dakon da nake haÉ—awa da shi yanzu sai a hankali, shi ya sa ma na yanke wannan shawarar ta mu dawo nan gida."

Kawu Sani ya dubi Inna da ta cika fam ya ce, "Kulu kin ji abin da Hasan ya ce ko? Da ma kuma wannan gidan kin san gidansa ne da ya gada a wurin mahaifinsa. Don haka zai dawo tare da iyalinsa, idan na sake na ji wata magana marar daɗi daga gare ki wallahi ranki sai ya yi mummunan ɓaci."
Sai da Inna ta furzar da iska mai zafi sannan ta É—ago ta ce, "Na ji duk abin da ka faÉ—a Yaya, amma kuma ni ma ina da sharaÉ—i."
Dam! Ƙirjin Rakiya da na Malam Hasan ya buga kusan lokaci ɗaya, Kawu Sani ya dube ta yana karantar yanayinta ya ce.
"Muna jin ki."

"Ka yi haƙuri Yaya ba rashin kunya zan yi maka ba, amma dai Hasan ɗana ne. Kuma ni da kai ba ma samun kowacce irin matsala sai a sanadiyyar matarsa. Amma ƙiri-ƙiri an shanye..."

"Kulu ba na san ƙananan maganganunki marasa lissafi."
Kawu Sani ya katse ta a É—an tsawace, wani abu ne ya sake tokare Inna. Ta haÉ—iyi yawu mai É—aci ta ce.
"Sharaɗina mai sauƙi ne Yaya, don gaskiya ba zan zuba ido rayuwar Hasan ta ƙare babu 'ya'ya ba. Duk cikin 'yan'uwansa shi kaɗai ne bai samu wani cigaban ku zo mu gani ba, ga Gali nan tare suka yi aure 'yarsa Suwaiba mai shekara goma har samari sun fara tsayar da ita. Don haka na yanke shawarar a wannan karon sai ya auri Zuwaira." Da wani irin firgici Rakiya da Malam Hasan suka ɗago suna kallonta cike da zallar tashin hankali.

GIDANSU FAUWAZ

Jim Abba ya yi yana nazari, cike da gamsuwa da shawararta ya É—ago ya ce.
"Maganarki a kan hanya take Tani, domin a makarantar allo ne kaɗai zai samu tarbiyyar da muke buƙata tun da ya riga da ya raina mu. Amma ban da lalacewa ta yaya yaro kamar Fauwaz da bai wuce shekara goma zuwa sha biyu ba har ya fara bin dare yana yi mana ɗauke-ɗauke."
Tani ta saki ajiyar zuciyar farinciki, amma sai ta ɓoye jin daɗinta ta aro fuskar damuwa ta lulluɓawa fuskarta ta ce.
"Shi ne tashin hankalin, amma idan aka kai shi makarantar allo zai koyi neman na kansa har ya iya tsayawa da ƙafarsa. Ka ga a can bai ɗauki na wani ba ballantana ya janyo mana magana, amma matuƙar muka cigaba da zama da shi a haka har 'yar uwarsa sai ya koyawa."
Abba ya yi zaraf ya ce, "Wannan gaskiya ne Tani, wallahi shi ya sa nake ƙaunarki. Saboda kina da hangen nesa da sanin ya kamata." Tani ta saki murmushin jin daɗi, sannan ta cigaba da ɗora shi a kan shawarwarin da zuciyarta take saƙa mata wacce take gani ita ce hanya mai ɓille mata.

Hawaye bibbiyu ne suka shiga sintiri a saman fuskar Fauwaz, a hankali ya ja ƙafa ya shiga wurin Abida da har lokacin take cikin mawuyacin hali. Ba shi da wata mafita, domin bai san kuma abin da zai yi mata ba. Don haka ya rungume ta ya fashe da kuka yana jin kewar mahaifiyarsa. Jikinta zafi ya ji shi zau kamar wuta, bakinta yana rawa cikin sanyin murya ya ce.
"Yaya... mutuwa... zan yi."
Girgiza kansa ya yi cikin kuka ya ce, "Ba za ki mutu ba Abida, da safe zan sai miki magani da kudun da na samo."

Idanunta a lumshe suke don ko iya buɗe su ba ta yi, ta ɗago hannu tana laluben fuskarsa. Da sauri ya riƙo hannun ya ce, "Me kike so Abida?"

"Ya... ya... ba na son na mutu na bar ka a wurin Aunty, yanzu Abba ya daina sonmu."

Fauwaz ya kwantar da kansa a fuskarta ya ce, "Ba za ki mutu ba kin ji Abida, Abba kuma ba daina son mu ya yi ba Aunty ce take faÉ—a masa laifinmu. Shi kuma duk abin da ta faÉ—a sai ya yarda da shi.

"Zan sha ruwa."

Ta furta masa a galabaice, sai da ya kwantar da ita sannan ya miƙe da sauri ya ɗebo mata ruwa. Ta sha ruwan sosai, ragowar kuma ta ce ya shafa mata a jikinta don ta ji daɗi. Cikin hukuncin Ubangiji ya ji zafin jikin ya ragu da ya zuba mata ruwan, don haka yana zaune yana gyangyaɗi shi da ita bacci ya ɗauke su, ba shi ya farka ba sai da aka fara kiran sallar asuba.
Lokacin da ya tashi idon Abida biyu, a wannan karon jikinta babu zafi sosai. Sai dai numfashinta da take fitarwa sama-sama, sai da ya yi mata sannu ta amsa a hankali sannan ya miƙe domin ya ɗauro alwala don ya tafi masallaci. Har ya je bakin ƙofa ta ɗaga masa hannu, don yadda numfashinta yake fita ya sa ta gagara furta sunansa da ƙarfi.

"Yayy... yaya."

Ta furta a sarƙe ganin har zai fita bai ganta ba, da sauri ya koma ya ce.
"Ga ni Abida me kike so?"

"Na yi mafarki... da Umma, ta ce... ka kusa daina wahala... da ni."

Ta furta a wahalce, sai ta cigaba da cewa.
"Ta... kuma ce na gaishe ka."
Murmushi mai sauti Fauwaz ya saki cikin jin daɗi ya ce, "Allah da gaske Abida? Na ji daɗi sosai, ni kuma tun da Umma ta rasu sau biyu na taɓa mafarki da ita."
Murmushi ta sakar masa, sai ya sake miƙewa zai tafi masallaci ta sake riƙo hannunsa.
"Yaya ina son... na yi kuÉ—i... don mu koma wani gidan... Aunty ta daina ganinmu."

"In Shaa Allahu idan na girma na samu kuÉ—i zan gina mana gida mu koma can."
Ya furta mata kalaman har cikin zuciyarsa, sai a lokacin ya fita daga É—akin ya je ya É—aura alwala. Yana gama alwala ya ga mahaifinsa ya fito shi ma, babu wanda ya yi wa wani magana har suka fita. Suna hanyar masallaci Abba ya ce.

"Ya jikin Abidan?"

Kamar Fauwaz ba zai amsa ba, sai ya danne zuciyarsa ya ce.
"Da sauƙi."
Daga haka suka ƙarasa masallaci, sai da aka idar da sallah Fauwaz ya jima yana yi wa Abida addu'ar Allah Ya ba ta lafiya sannan ya fita. Kai tsaye wani ƙaramin asibiti ya nufa da ke Unguwa Uku da ƙafarsa, har lokacin da ragowar duhu a gari don haka yawancin babban titin Na'ibawa babu ƙananan motoci sosai sai manya. Kasancewar da ƙafa yake tafiya lokacin da ya ƙarasa Unguwa uku gari ya yi tangaran har rana ta fito, ƙaramin asibitin na kuɗi mai suna Farha Clinic ya shiga. A reception ya samu wata mata wacce da alama ba bahaushiya ba ce, sai da ya gaishe ta sannan ya miƙa mata kuɗin hannunsa gabaɗaya sannan ya ce.

"Don Allah magani za ki ba wa ƙanwata, tana zazzaɓi sosai. Sannan mamana kafin ta mutu ta taɓa kai ta asibiti aka ce ƙodarta na ciwo ban sani ba ko ciwon ne ya tashi."

Yadda yake maganar za ka fahimci kalaman daga zuciyarsa suke fitowa, sai dai da yake ba ta jin hausa sosai ya sa ta kira wani abokin aikinta wanda ya kasance bahaushe. Matashi ne siriri, fuskarsa a zagaye da baƙin gashi. Fari ne fat sai dai yana da ɗan ƙaton kai, sai da ya gama sauraronsa ya ce.

"Ina mamanku ko babanku?"

Muryarsa tana rawa ya ce, "Mamanmu ta rasu."

"Babanku fa?"

Ya sake jefa masa tambaya, ya lura da sauyin fuskarsa, sai ya kawar da tambayar da ya yi masa ya ce.
"Likita don Allah ku ba ta magani tana jin jiki sosai, ko kuÉ—in ba su kai ba wallahi zan yi gwangwan na cika sauran." Tausayin Fauwaz ya kama shi, sai ya dafa kafaÉ—arsa ya ce.
"Abokina nan asibiti ne, asibiti kuma ba sa bayar da magani kai tsaye har sai sun binciki marar lafiya, an yi masa gwaje-gwajen da ya dace sannan likita ya rubuta masa magani. Ka je gida ka samu wani babba ku kawo ta asibiti, idan likita ya duba ta sai ya ba ta maganin da ya dace ka ji."

Tun bai dire kalamansa ba idanun Fauwaz suka ciko da ƙwalla, cikin damuwa ya gyaɗa kai don idan ya ce zai amsa masa kuka zai iya ƙwace masa. Ya karɓi kuɗin da ya ba su sannan ya juya ya tafi zuciyarsa cike da ƙuna, yana kuma fargabar halin da zai sake samun ta a ciki.
A ƙasa ya ƙara komawa har Na'ibawa, har zai wuya 'yan lemo ya hango kemis ɗin Maman Junior tana ƙoƙarin rufewa don ya lura da alama abu ta ɗauka domin ba ta buɗewa da safe.

"Maman Junior a ba ni magani."

Ya furta yana miƙa mata kuɗin hannunsa, cikin gurɓatacciyar hausarta ta ce.
"Wone yiri magani?"

"Ƙanwata ce take zazzaɓi, kuma kwanaki an ce ƙodarta tana ciwo."

Zazzaɓin da ya ambata ta fi riƙewa, saboda yau da gobe da ake yawan sayen maganin zazzaɓi da sauran gama-garin cutuka a wurinta. Kemis ɗin ta buɗ ta shiga, sai ta haɗo masa maganin zazzaɓin maleria ta miƙa masa ragowar canjinsa. Gudu-gudu sauri-sauri a haka ya ƙarasa layinsu, tun daga farkon layin ya hango tsirarin yara a ƙofar gidansu.

"Ikon Allah Ya wuce gaban komai, shekaran jiya fa Abida suna tare da Sumayya da ta gaishe ni ta ce min aikenta aka yi. Wai ita ce yau ta amsa kiran mahalicci, koico rayuwa tsakaninta da mahaifiyarta shekara guda kenan."

Kalam maƙociyarsu da take shirin shiga gidansu suka daki kunnuwansa, waɗanda suka yi daidai da bugun zuciyarsa wacce take barazanar tarwatsewa.

Share Pls

Ummou Aslam Bint Adam 🌚
07062062624

[13/05, 18:20] Ameerah Adam: *GAMMON RAMA*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

GargaÉ—i: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ba tare da izinina ba.
Chapter 8 · 0% Book details