Sashe 14
Gammon Rama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ai ba a aure dole ko? To ai kuwa yau ba zan ƙara kwana a gidan nan ba. Wallahi sai ka ba ni takarda ta, ka zauna da 'yar'uwarka wacce mahaifiyarka take son ku kasance tare." Tana gama faɗar haka ta shiga haɗa kayan sawarta, duk da a lokacin ita ma ba ta san inda za ta dosa ba, amma ji take yi gara ta bar gidan ko ta samu salama. Yadda ya ga Rakiya tana faɗar maganganu ya tabbatar da an gama ƙure haƙurinta, a shekarunsu goma da aure ba ta taɓa yin wannan fito na fito da shi kamar haka ba. A fusace ya fita daga ɗakin, bayan ya dawo ya same ta har ta saka hijabinta. Wata farar takarda ya miƙa mata, cikin wani irin yanayi ta dube shi ba tare da ta tanka masa ba. Duk yadda ta so rabuwa da Malam Hasan sai ta ji gwiwoyinta sun yi sanyi, ta dube shi muryarta tana rawa ta ce.
"Sakina ka yi?"
Bai amsa mata ba, ya ga ta É—auki jakar kayanta za ta fita. Cikin sauri ya bi ta ya ce.
"Wannan hukuncin ina ganin shi ne zai fiye mana alheri gabaÉ—aya, amma kafin nan ina son ki zo mu je gidan Kawu Sani ki kwana a can."
"Babu ruwanka da inda zan kwana, idan na ga dama na kwana a titi ma damuwa ta ce."
Rakiya ta furta tana fita, duk abin da yake faruwa Inna da Zuwaira suna tsakar gida suna ji. Saboda farinciki Zuwaira ji ta yi kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha, Rakiya ta fita ko kallonsu ba ta yi ba ta fita daga gidan. Ganin haka ya sa Malam Hasan yana bi bayanta yana kiran sunanta, ta cigaba da tafiya ko waigensa ba ta yi ba.
ABBAN FAUWAZ
Abba yana É—aga labulen É—akin ya saki salati cike da mamaki ya ce. "Tani lafiya kike kuka? Ko wani abu ne ya faru?"
Sai kuma ya waiga wurin Fauwaz da ya yi suman tsaye yana bin ta da kallon mamaki, Abba ya ce.
"Kai Fauwaz me yake faruwa ne?"
Fauwaz ya wara hannuwa a daƙile ya ce, "Abba kukan makirci take yi."
Sototo Abba ya yi yana kallonsa, a É—an faÉ—ace ya ce. "Ka san me kake faÉ—a kuwa? Ko kuwa rashin mutuncin da tarbiyyar da kake yi ka gwada mata?" Kafin Fauwaz ya sake magana Tani ta ce.
"Alhaji wallahi sai ka sake ni a yanzu ba sai an jima ba. Kamar ni ina matsayin matarka wai Fauwaz ya É—aga hannu ya mare ni, saboda Allah É—an da a haife da ace na haihu da wuri na haifi wanda ya fi shi ma." A razane Abba ya dubi Fauwaz ya sake mayar da kallonsa ga Tani ya ce, "Mari fa Tani?"
"Au tantama kake Alhaji zan yi masa ƙarya ne? Ai shi ya sa na ce gara ka sake ni don wallahi ba zan iya zama gida ɗaya da wannan yaron ba." Tani tana rufe baki a fusace Abba ya rufe Fauwaz da mahaukacin duka. Ta ko ina yake kai masa duka, tun Fauwaz yana yunƙurin kare kansa har ya faɗi a ƙasa Abba bai daina dukansa ba. Sai da ya gaji don kansa, bayan ya ga Fauwaz yana fitar da numfashi da ƙyar sannan ya miƙe yana huci. Tani da daɗi ya gama mamaye ta, ta sake kwaɓe fuska ta ce.
"Ni fa bayan wannan hukuncin dole ka san abin yi Alhaji, don yadda ka hukunta shi wallahi na san idan ya ji daÉ—in jikinsa sai ya yi mini abin da ya fi haka."
Yarfe gumin fuskarsa Abba ya yi yana huci ya ce, "Gidan horo zan kai shi, kada wani abu ya dame ki don babu abin da zai raba ni da ke Tani. Ni da na rabu da ke gara na rabu da kowa a rayuwata." Sai a lokacin Tani ta saki murmushi ta ce.
"Shi ya sa nake ƙaunarka Alhaji."
Fauwaz da ke kwance cikin mummunan yanayi ya ce, "Abba... matar nan ba sonka take ba... wallahi..."
Naushin da Abba ya kai masa a baki ne ya katse shi, bakinsa ya fashe jini ya fara zuba. Kafin wani lokaci tuni fuskar Fauwaz ta sauya gabaɗaya. A nan take Abba ya riƙo hannun Fauwaz cike da jin haushi, ya wurga shi ɗakinsa ya janyo ƙofa ya saka mukulli ya rufe.
Sai da Tani ta haɗa masa ruwan wanka, wanda ya sha miyagun turarrukan da ta karɓa a wurin malamanta sannan Abba ya shiga ya yi wanka ya fito. Zaman da ya yi yana cin abinci a nan yake ba ta labarin cinikayyar da suka yi, da biyan bashin da ya yi. Sai kuma adadin ragowar kuɗaɗen da ake bin sa. Farinciki ne ya mamaye ta, har sai da fuskarta ta gagara ɓoye halin da zuciyarta take ciki. Don haka Abba ya ce. "Amma akwai wani albishir ko labari da kika samu ne Tani? Na lura kamar kina cikin farinciki."
'Dole na shiga farinciki haƙa ta, ta kusa cimma ruwa. Lokacin da zan kaɗa goge na ya zo.'
Ta raya a ranta, amma a fili sai ta ce. "Wani abu na tuno, amma ba yanzu zan sanar da kai ba sai ya tabbata In Shaa Allah."
Shi ma murmushi ya saki ya ce, "Wato kina son ki ce za ki ba ni mamaki kenan?"
"Tabbas za ka sha ruwan mamaki, don wataƙila tun da ka zo duniya ba a taɓa shayar da kai ruwan mamaki kamar wanda zan ba ka ba." Shiru ya yi ya zura mata ido, har sai da ta ji tsoron ko ya so fahimtar inda zancanta ya dosa. Sai kuma ta ga ya bagarar suka cigaba da hira, daga cikin hirar da suka tattauna har ta kai Fauwaz gidan horo. Bayan ya yi zaman gidan horo na wata biyu, daga nan za a ɗauke shi zuwa almajiranci.
Kamar yadda Tani ta tsara masa haka Abba ya É—auki Fauwaz ya kai shi gidan kangararru da ke titin Hajj Camp. Sai dai tun kafin a kai shi gidan horon suka fara da yi masa horon yunwa, don tun ranar da ya sa shi a É—aki kullum sau É—aya ake ba shi abinci da ruwa shi ma ba wani na kirki ba. A haka sai da ya shafe kwana biyar a cikin É—akin, sai dai kafin Abba ya fita ya raka shi banÉ—aki ya yi uzurin da zai yi da ya gama ya mayar da shi cikin É—aki ya kulle. Ana gobe za a kai shi gidan horon Abba ya shiga kai masa abinci, har ya juya zai fita a wahalce Fauwaz ya ce.
"Abba na san abin da ba ka sani ba, don Allah ka ba ni dama na yi maka bayani. Ba na son ka yi danasani a lokacin da bayanina ba zai yi maka amfani ba."
Dawowa Abba ya yi yana daga tsaye ya ce, "Ina jin ka, idan ka nemi yi mini shashanki ranka ya yi mugun ɓaci." Fauwaz ya ji daɗi sosai, duk da yunwa ta sa muryarsa ba ta fita amma ya yi ƙoƙarin mahaifinsa ya fahimce shi.
"Abba akwai abin da Tani take shiryawa a kanka..."
"Dakata Fauwaz!"
Abba ya katse shi yana ɗaga masa hannu, domin duk wani abu da ya danganci kushe ko laifi matuƙar a kan Tani ne ba ya ji ba ya gani.
"In dai a kan Tani ne mun dinga samun saɓani da kai kenan. Matuƙar ba za ka ɗauki Tani a matsayin mahaifiyarka ba, sai dai ni da kai mu kasance a mabambamtar inuwa." Daga haka Abba ya fita.
Tun bayan da Fauwaz ya tafi gidan horo Abba da Tani suka cigaba da rayuwa, sai dai kusan malejin rayuwa suke yi domin al'amura da dama a ɓangaren kasuwanci sun tsaya masa cak. Sakamakon yana samun kuɗi yake kai wa Alhaji Dikko a rubuta su cigaba da lissafi. Suna cikin haka har Fauwaz ya shafe watanni biyu cif a gidan horo Abba ya ɗauko shi ya dawo da shi. Duk wanda ya san Fauwaz a baya, idan ya gan shi a wannan lokacin ba zai gane shi ba a tashin farko. Ya yi wani irin baƙi ya rame, kamar ba shi ba. Haka kuma wasu daga cikin ɗabi'unsa sun sauya sosai, duk da dama can ba mai magana ba ne. Amma a wannan lokacin sai rashin maganarsa ta ƙaru, ya koyi taurin kai fiye da yadda yake da shi a baya. Idan ya ce ba zai yi abu ba, duk horo ko hukuncin da za a yi masa ba su sa ya aikata ba. Haka kuma ya fita daga sabgar Tani, ita kanta a wannan lokacin har tsoron a bar su daga shi sai ita take yi a gida. Daga ƙarshe ma sai take kulle kanta a ɗaki idan Abba ya tafi kasuwa, duk wani abu da za ta buƙata saka shi a ɗaki take yi. Sai ta ga fitar Fauwaz sai ta fito da sauri ta rufe gidan sannan ta ɗora girki, idan ta gama sai ta buɗe gidan ta shige ɗakinta ta rufe. A haka suka cigaba da rayuwa har Abba ya ɗauke shi, ya kai shi garin Gombe almajiranci.
Satin Fauwaz biyu da tafiya watarana da sassafe suna zaune aka ƙwanƙwasa ƙofar gidan, Abba ne ya fita yana zuwa ya ci karo da 'yansanda a ƙofar gidan. Gaisuwar mutumci suka yi, sannan ɗaya daga cikinsu ya ce.
"Alhaji mun zo gayyatarka zuwa ofishinmu ne, sakamakon wata tuhuma da ake yi maka."
Da mamaki Abba ya ce, "Tuhuma kuma?"
Lokaci É—aya suka gyaÉ—a masa kai, sai Abba ya ce.
"To ku je In Shaa Allahu..."
"Am sorry to say hakan ba zai yuwu ba, dole za mu tafi da kai ƙafarmu ƙafarka."
Suka ba shi amsa kai tsaye fuska babu walwala.
Jama'a za ku iya fara payment daga yau💃🻠free pgs suna gab da ƙarewa.
Naira 500 ne kacal ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan lambar 07062062624 idan littafi ya kammala zuwa document 800 ne.
Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624
[18/05, 18:15] Ameerah Adam: *GAMMON RAMA*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
GargaÉ—i: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba.