← Book details Gammon Rama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 21

Sashe 1

Gammon Rama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[10/05, 07:21] Ameerah Adam: *GAMMON RAMA*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

GargaÉ—i: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba.

Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne.

SHAFI NA ÆŠAYA

Tun da yamma ta yi, zuciyar Malam Hasan ta dare gida huɗu kwatankwacin kusurwar bangon Gabas, Yamma, Kudu da Arewa. Sakamakon kaɗuwa da mummunan tashin hankalin da ya baƙunci rayuwarsa da ta iyalinsa. Tafe yake jiki a saɓule tamkar kazar da aka jefa da wuƙa, haka ya ƙarasa kan layin gidansa hannuwa biyu suna dukan cinya. Hadari ne yake haɗuwa a garin, sassanyar iskar damuna mai saka annushuwa tana kaɗawa da ratsa jiki. Sai dai a ɓangaren Malam Hasan ba haka abin yake ba, domin wuyan rigarsa zuwa ƙirji, da gefen hammatarsa sun yi sharkaf da gumi. Har ya dafa langa-langar da ke tokare da ƙofar gidan nasa, sai kuma ya tsaya jim! Yana ƙura wa raunanniyar katangar gidan idanu tamkar yana son tantance kalar ƙasa da taɓon da aka gine dangar da su.

"Allah Ka kawo mini mafita, Allah Ka fi ni sanin halin da nake ciki Ka hore mini kada na tozarta ba don ni ba; ba kuma don halina ba."

Ya furta da wata irin raunanniyar murya, a hankali ya ɗaga ƙafarsa da ke sanye cikin matattun takalmansa da sun gama suɗewa ta ƙasa. Ya shiga cikin gidan bakinsa ɗauke da sallama, Rakiya ya hango zaune tana ba wa Fatihu abinci. Sai da ya ƙarasa gaban kwanon ya lura kwaɗon ƙanzo ne ta yi masa, wanda yake fari fat. Ba tare da ya samu sirkin ƙuli, magi da mai ba. Gishiri ne kawai Rakiya ta barbaɗa masa don ya ji daɗin ci a cikin bakinsa.
"Sannu da zuwa Mai gida, Allah Ya sa dai an dace."
Rakiya ta furta cike da damuwa, ajiyar zuciya Malam Hasan ya sauke yana sunkuyar da kai ƙasa ya ce.
"Rakiya lamarin nan sai godiyar Allah, amma sisi da kika sani babu wacce na samu rance. Kowa na tambaya da irin uzurin da zai kawo mini, daga ƙarshe ma sai na lura wasu kuɗin ne ba za su ba ni ba."

"Innalillahi wa inna'ilahir raji'un, Ya Allah ka kawo mana É—auki."
Rakiya ta furta a sanyaye, zama Malam Hasan ya yi ya ce. "Amin Ya Rabbi."

"Yanzu Malam ya za mu yi? Ka san fa Alhaji Bashari ba ya saɓa alƙawari, ba kuma ya ɗaga ƙafa. Wallahi tun da ya ce a yau sai mun bar masa gidansa, babu makawa sai ya zo ya ci mana mutumci."
Rakiya ta sake maganar cikin damuwa, hannu ya zura a koɗaɗɗan aljihun da ke jikin koɗaɗɗiyar shaddarsa. Ya ciro garin kwaki da bai fi gwangwani biyu ba, sannan ya miƙa mata wani ɗan ƙullun suga ya ce.
"Ga wannan jiƙa mana mu sha, kafin mu ga abin da Allah zai yi da mu."

"To malam ko za ka kira shi a waya?"
Shiru Malam Hasan ya yi da jin furucinta, sai ya zaro wasu 'yan canji a aljihunsa na gaba ya ce.
"Wannan canjin da kika gani, wayar tawa na sayar wai ko Allah zai sa na samu rancan kuɗii na haɗa masa da su. Duka gabaɗaya ɗari takwas da hamsin na sayar da ita, tun da ta tsufa ta kwana biyu. Shi ne na sayo mana gari da suga, na ba wa Malam Idi biyan bashin da yake bi na. Yanzu kuɗin hannuna ko ɗari huɗu ba su kai ba, idan ya zo ya ji magiya da roƙon da zan yi masa shi kenan. Idan kuma bai haƙura ba, sai mu bar masa gidan."
Yana gama magana aka fara kiran sallar Magriba, miƙewa ya yi ya ɗauro alwala sannan ya fita masallaci. Fatihu mai kimanin shekarae biyu ya miƙe ya dafa ta cikin gwarancinsa ya ce, "Umma a kala."
Kwanon kwaɗon ƙanzon ta karɓa, ta tsiyayi garin kaɗan ta jiƙa masa sannan ta sake barbaɗa masa gishiri ta miƙa masa. Nan take ya hau ci, yana yi mata murmushi. Miƙewa ta yi ita ma ta jiƙa shi a kofi, ta yafici sugan ta zuba sannan ta fara sha a gaggauce saboda yunwa. Domin rabonta da abinci tun ɗumamen tuwon dawar da ta ci da safe.

Sai da ta kammala shan garin sannan ta ɗauki buta domin ta ɗaura alwala, a daidai wannan lokacin Malam Hasan ya shiga bayan ya dawo daga masallaci. Ganinsa ya sa ta ajiye butar, ta ɗauki dogon kofin sulbarsa na shan ruwa ta juye masa ragowar garin kwakin da ya yi saura ta jiƙa masa. Karɓa ya yi ya fara cusa wa cikinsa, duk da ba wani daɗinsa yake ji ba duba da tarin damuwar da ta cunkushe kwanyarsa. Alwala Rakiya ta ɗaura sannan ta gabatar da sallar Magriba, sallamar da za ta yi daga sallah ta yi daidai da sallamar da aka fara rangaɗawa a tsakar gidan. Kuma kusan a daidai gaɓar hadarin da ke haɗuwa ya shiga bayar da walƙiya haɗe da yayyafi sama-sama. Hakan ya sa ta yi saurin fita ta ɗauki zanen goyo ta goya Fatihu, sannan ta koma daga ƙofar ɗakinta tana kallon abin da yake shirin faruwa.

"Malam Hasan ya ake ciki?"

Alhaji Bashari ya furta a ɗage, yana bin sa da wulaƙataccan kallo. A sanyaye Malam Hasan ya dire kofin garin da ko rabi bai sha ba ya ce, "Sannu da zuwa Alhaji..."

"Riƙe sannunka, wannan ba shi ne abin da ya kawo ni ba, waɗannan kalaman idan na shiga gidana har gajiya nake da su. Ina maganarmu ta kwana? Da kuɗin ko babu?"
Alhaji Bashari ya watsa masa tambayar yana ƙure shi da ido, cike da karaya da sarewa Malam Hasan ya ce.
"Don girman Allah Alhaji ka yi haƙuri..."

"Kai Zage, Ƙaribu da Goje ku shigo don Allah ba na son ɓata lokaci ruwa ya fara saukowa."
Alhaji Bashari ya furta yana ɗaga murya, tun bai rufe baki ba matasan da ke ɗauke da siffar masu zuƙe-zuƙe suka shiga cikin gidan suna wuri-wuri da idanu.
"Allah Ya taimaki mai gida, a sa kai ne?"
Wanda aka kira da Zage ya furta yana cije gefen bakinsa, cikin isa Alhaji Bashari ya ce.
"Ku fito masa da duk wani abu na cikin gidan nan ku dire a ƙofar gida. Ku gaggauta saboda kun ga yayyafi ya fara sauka, ba na son ya taɓa ni don mura yake saka ni."

"An gama master, kai Ƙaribu sa ta sama."
Goje ya furta da muryar maye yana surar tabarma da kwandon wanke-wanken da ke gefen É—akin Rakiya.

"Don Allah Alhaji ka rufa mana asiri kamar yadda Allah Ya rufa maka, don Allah ka ba ni iya yau kaɗai wallahi gobe gari yana wayewa za mu bar maka gidanka." Malam Hasan ya furta yana dafa ƙafarsa, da sauri Alhaji Bashari ya janye ƙafarsa kamar wanda kashi ya sauka a kanta. Cike da tsantsani ya ce, "Kada ka sake taɓa ni da wannan hannun naka Malam Hasan, ina fatan ka gane. Wallahi a yau babu abin da zai hana ni rufe gidan nan, zancan banza ma kenan. Mutane idan kuka samu gidan mutum kamar gadon iyayenku, dubi duk yadda kuka lalata mini gida. Ji gefen katangar nan yadda ta zube, kalli ƙofar banɗaki ita ma rawa take za ta faɗi. Ai wallahi ɗan baƙara na sake ba wa matsiyaci gida babu gaira babu dalili. Kai Ƙarubu, ku yi ku fito da kayan ɗakin mana."
Alhaji Bashari ya furta cikin kumfar baki yana baza babbar rigarsa, a sanyaye Malam Hasan ya tashi. Don tun da yake a rayuwa kusan ba a taɓa gasa masa maganganun da suka ci zarafinsa kamar wannan ba. Ba tun ranar ya san Alhaji Bashari mutum ne mai wulaƙanci ba, amma bai taɓa tsammanin wulaƙancinsa ya kai haka ba.

Rakiya da ke gefe goye da Fatihu ban da hawaye babu abin da take gogewa, suna nan tsaye carko-carko su Zage suka ciro yaƙunanniyar katifarta suka fita da ita. Cikin ƙanƙanin lokaci suka fitar da komai na gidan, da yake dama ɗakin Rakiya ba wani kayan kirki ne da shi ba, saboda ba wasu kayan ɗaki gare ta ba. Daga katifa, tabarmu, Ghana Must go ta kayan sawarsu, labule, kwandon wanke-wanke da kujera 'yar tsugunno. Sheƙeƙe Alhaji Bashari ya dubi Malam Hasan ya ce, "Malam Hasan za ku iya fita, tun da a yanzu dai ni da kai babu kare bin damo. Kuma ba mu haɗa iri ba ballantana ka ce kana da gado a kaina."
Malam Hasan da baƙincikin duniya ya mamaye shi ya dubu Rakiya ya ce, "Rakiya mu je, In Shaa Allah, ina da yaƙinin Allah ba zai tozarta mu ba."
Kamar Rakiya tana jira sai kuwa ta fashe da kuka ta ce, "Abin da ka yi mana Allah Ya yi maka kai ma, In Shaa Allahu yadda ka wulaƙanta mu sai Allah Ya tozarta ka."

"Dama ai tsiyar matsiyaci kenan, duk rufin asirin da na yi muku na ba ku mahalli kuke zaman haya ba ki gani. Ban da irinmu masu tausayi, waye zai ɗauki gida ya ba wa faƙirai faƙara'u alal lalurati gidan haya."Alhaji Bashari ya furta wa Rakiya.

"Kada na sake jin bakinki Rakiya."
Malam Hasan ya furta mata, harara ta wurga wa Alhaji Bashari sannan suka fita daga gidan. Malam Hasan yana fita Alhaji Bashari ya sa su Goje suka rufo ɗakunan guda biyu. Sannan suka fito waje ya datse ƙofar gidan da mukulli, a daidai wannan lokacin yayyafin da ake yi ya fara ƙarfi. A ɗan ruɗe murya tana rawa Rakiya ta ce.
"Malam ina za mu saka kayan nan?"
Damuwa ɗauke a fuskarsa ya ce, "Bari na ƙwanƙwasa gidan Malam Ado ko ya dawo."
Tun ba ta yi magana ba Malam Hasan ya matsa gidan ya fara bugawa, ya É—an jima a haka sannan aka buÉ—e masa. Ganin Malam Hasan ya sa shi É—an tsuke ta ce.
"Malam Hasan ne?"
Malam Hasan ya gyaÉ—a kai ya ce, "Eh ni ne, Dama Wani taimako na zo ka yi mini."
Chapter 1 · 0% Book details