← Book details Gammon Rama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 21

Sashe 3

Gammon Rama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kasancewar hanyar fili gare ta fetal, ya sa suka gagara samun wurin da za su fake. Da yake babar hanya ce wacce take ɗauke da gwazazzaɓai sai ruwan saman ya fara taruwa a cikin ramuka har ba ka iya bambamce rami da kwata. Da sun yi taku ɗaya-biyu sai dai ka ji taɓal sun faɗa cikin ruwa, ganin hanyar tana sake malalewa da ruwan duba da yadda ruwan sama kamar da bakin ƙwarya yake zuba. Ya sa Malam Hasan ya dubi Rakiya ya ce.
"Rakiya ga gidan kallo can a gefen kwalbatin can mu tsaya a can."
Rakiya ba ta iya amsa masa ba, saboda yadda Fatihu yake tsanyara kuka duk ya gigita ta. Gidan kallon duk da ya kasance da rumfa, amma haka feshin ruwan ya dinga jiƙa su. Suna nan tsaye, da takaici ya cika Rakiya sai kawai ta saka kuka. Malam Hasan sunkuyar da kansa ƙasa ya yi, yana jin kukan nata har cikin ɓargon jikinsa. A sanyaye ya riƙo hannunta ya shiga matsawa alamar rarrashi ba tare da ya iya tanka mata komai ba. Sai da ca ji kukanta mai isarta, sannan ta share hawayenta tana jin rabin baƙin cikin da ke cushe a ranta ya faɗa mata. Sun kusan tsaiwar minti ashirin, sannan ruwan ya fara tsagaitawa. Iskace take kaɗawa, sai walƙiyar da ake yi jifa-jifa. Shiru Malam Hassan ya yi, yana bin babbar hanyar da kallo, musamman yadda ya ga babbar hanyar ta shafe da ruwa. Kusan dama haka hanyarsu take, matuƙar damuna ta shigo haka suke fama da matsalar hanya. Wannan dalilin ne ma ya sa duk nisan hanyar masu abin hawa ba sa yarda su shiga, ko fasinja suka ɗauka sai dai su ajiye shi daga gefen titi.

Rakiya ce ta gaji da tsaiwar, don haka ta sauko Fatihu daga bayanta tana ƙare ruwan rigar jikinsa. Ganin yana rawar ɗari ya sa ta yi saurin lulluɓa masa ɗankwalin da ta rufe shi duk da shi ma a jiƙe yake. Jigum-jigum suka yi kowannensu da abin da yake saƙa wa zuciyarsa, suna cikin haka har Malam Hassan ya lura da ruwan da ke tafiya a hanyar ya fara ja baya. Don haka ya dube ta ya ce.
"Rakiya mu bar wurin haka, mu ƙarasa kada dare ya yi mana kin ga yanzun ma duhu ya yi."
Malam Hasan ne ya fara tsoma ƙafarsa a ruwan, ita ma Rakiya ta biyo bayansa. Sai dai bisa tsautsayi ta ji ƙafarta ta taka wani abu mai kaifi, silar haka ya sa ta gurɗe ta kifa cikin ruwan. Fatihu da ke hannunta ya zame, ganin haka ya sa ta saki ƙara mai ƙarfi. A hargitse Malam Hasan ya shiga lalubensu ita da Fatihu, don ita kanta ji ta yi ruwa yana ƙoƙarin fisgarta. Fatihu kuwa sautin amonsa suka ji sau biyu, daga haka ba su ƙara jin amonsa ba.

"Fatihu" Fatihu! Fatihu!"

Rakiya ta furta a haukace tana rarrafe haɗe da laluben cikin ruwan, haka shi ma Malam Hasan ya shiga lalube yana kiran sunanta da na Fatihu. Riƙo hannun Rakiya ya yi, sai ya ji kamar su ma yana fisgarsu, cikin tashin hankali ya janyo ta suka koma saman dakalin gidan kallon.

"Ka ƙyale ni na ɗauko Fatihu malam, na ji kamar kukansa don Allah ka bar ni kada ruwa ya tafi da shi."
Rakiya ta furta a haukace cike da zallar tashin hankali, a É—an tsawace Malam Hasan ya ce.
"Me kike yi haka ne Rakiya? Ki dakata na duba shi mana, idan kika biyo ni sai ranki ya ɓaci."
Yana gama faɗar haka ya sauka daga cikin rumfar ya shiga lalube da hannunsa yana kiran sunan Fatihu kasancewar babu haske a hannunsa. Sai da ya zura ƙafarsa a wani wuri, ya ji ruwa yana bin hanyar da rami a wurin. Wanda hakan ne ya sa ya ji gwiwarsa ta yi sanyi, lakar jikinsa ta mutu. Ƙwarin gwiwarsa ya tarwatse, jarumtarsa na neman rikiɗewa zuwa rauni. Cike da zafin nama ya cigaba da laluben a yunwace, jin ruwa yana niyyar jansa zuwa ramin ya sa shi yin baya cike da ɗacin zuciya.

Cikin rumfar ya koma, Rakiya tana ganinsa ta miƙe zumbur ta ce.
"Ina Fatihun?"
Sunkuyar da kai ƙasa Malam Hasan ya yi ya ce. "Mu ɗauki dangana Rakiya, ina ji a jikina mun rasa Fatihu..."

"A'a ba ka duba da kyau ba, ni zan nemo shi da kaina."
Rakiya ta katse shi, sai ta miƙe cikin zafin nama tana ɗingisa ƙafarta saboda har lokacin wani irin zugi take yi mata. Sai dai firgicin da take ciki shi ya hana ta fahimtar yanayin da take ciki.
"Kada ki fita Rakiya, Allah Ya fi mu sanin dalilin da ya sa ya ƙaddara mana haka."
Malam Hasan ya furta yana riƙo hannunta, duk yadda ta so fisgewa haka ya riƙe ta tsam a jikinsa. Cikin wani irin yanayi na kewa da shaƙuwa ta fashe da wani irin gunjin kuka, kukan da sauraronsa zai iya raunatar da zuciya har ya saka zubar hawaye. Kuka take tamkar ranta zai fita, dalilin haka ya sa duk dakiya da ƙarfin zuciyar Malam ya fara zubar ƙwalla. Sun ɗauki dogon lokaci a wannan yanayin, har suka ji wasu masallatan suna kiraye-kirayen sallar Isha'i.

Tsirarun mutane ne suka fara wucewa, jin irin kukan da Rakiya take yi har lokacin ya sa wasu magidantan maza guda biyu da za su wuce, suka hasko wurinsu suna tambaya.

"Malam ne yake faruwa? Lafiya?"
Cike da ƙarfin hali Malam Hasan ya ce, "Lafiya ba ƙalau ba."
Duk da hanyar ba ta da kyau, amma ta cikin ragowar ruwan da ya kwanta mutanen suka naɗe ƙafar wando suka ƙarasa, a karo na biyu suka sake wurga masa tambaya musamman yadda suka ga Rakiya tana kuka kamar ranta zai fita.
"ÆŠan mu ne tsautsayi ya faÉ—a masa..."

Malam Hassan ya kwashe duk abin da ya faru ya sanar da su, lokaci É—aya suka É—auki salati cikin tashin hankali. ÆŠaya daga ciki ya ce, "Wannan ba maganar da za a zauna a yi ta kuka ba ce, mu gayyato jama'a."
Yana gama faɗar haka ya tafi da sauri yana yekuwa da shela, a hankali maza suka fara fitowa. Tsirrarun mata kuma suka dinga leƙowa da fitilu suna haske-haske, sai dai yawanci babu wani abu da suke iya gani duba da nisan da ke tsakaninsu da wurin da su Rakiya suke.
Kafin wani lokaci maza sun taru sosai, wasu suka shiga ba wa Rakiya da Malam Hasan baki, yayin da wasu suka shiga haske-hasken wurare. Amma duk haske-hasken da suka yi na kusan tsawon awa biyu babu Fatihu sai iya ɗankwalin Rakiya ko zanen goyonsa ba a gani ba. Da ƙyar da suɗin goshi aka ba wa Rakiya baki ta daina kukan da take yi, wani mutum daga cikin mutanen ya ce su zo gidansa su kwana kafin zuwa wayewar gari a sake fitowa duba gawar Fatihu.
ÆŠaki guda aka ba wa Malam Hasan da Rakiya, sun lura matar gidan mace ce mai karamci ce. Sai da suka yi sallah sannan ta kai musu abinci, fir Malam Hasan ya kasa cin abinci. Amma sai ya shiga rarrashinta yana ba ta baki a kan ta ci, cikin zubar hawaye ta ce.

"Malam kana tsammanin zan iya tauna ƙwayar hatsi a bakina, a ranar da na yi bankwana da Fatihu? Fatihu fa ya tafi ya bar ni shi kenan."
Ta sake fashe wa da kuka, jikin Malam Hasan ya yi sanyi. Cike da lallashi ya ajiye abincin a gefe ya janyo ta jikinsa ya ce.
"Ki yi haƙuri Rakiya, Allahn da ya ba mu Fatihu, Ya fi mu sanin dalilin da ya sa ya ɗauke shi a daidai wannan gaɓar. Kada ki yi fushi da lamarin Ubangiji, domin ta yuwu mutuwar Fatihu a wannan gaɓar ta fi zame mana alkairi a rayuwarmu."
Malam Hasan ya jima yana yi mata nasiha, Rakiya ta tsagaita da kukan sai hawayen da ke zuba daga idonta. Kusan kwanan zaune suka yi, sai gab da asuba bacci mai nauyi ya yi awon gaba da Rakiya. Koda aka kira sallar asuba bai tashe ba, sai da suka fita masallaci shi da mai gidan da suka kwana suka gabatar da sallah. Bayan sun dawo ya tashe ta ta yi sannan, a wannan lokacin masallatai suka shiga shelar abin da ya faru. Limanan ya ce idan gari ya yi haske a fita domin duba inda gawar Fatihu take. Bayan da Rakiya ta idar da sallah gari bai ƙarasa haske ba ta ce za ta je neman Fatihu, duk yadda Malam Hasan ya so hana ta fir ta ƙi hanuwa. Don haka mai gidan ya buɗe musu ƙofa suka fita gabaɗaya har shi, tun suna haske cikin caɓalɓalin da guntun ruwan saman ya kwanta har gari ya yi haske 'yan unguwa suka fito suka haɗu ana duba shi. Cikin hukuncin Ubangiji ba a tsinci gawar Fatihu a ko ina ba, sai a gefen wata ƙatuwar kwalbati. Shi ma dalilin da ya sa aka gan shi wani ƙaton dutse ne ya tokare shi, saboda girman kwatar maza uku ne suka shiga suka ɗauko shi fatar jikinsa duk ta kumbure da ruwa. A cikin buhu aka saka shi, jiki a sanyaye cike da karyewar zuciya suka miƙa wa Malam Hasan. Wani abu ya ji ya daki zuciyarsa, a daidai lokacin Rakiya ta ƙarasa ta ce.
"Ya mutu ko Malam?"
Shiru Malam Hasan ya yi, ganin buhun hannunsa yana ɗigar da ruwa ya sa ta yi saurin fisgewa tana duba ciki. Wata irin gigitacciyar ƙara ta saki, sai kuma ta saki buhun ta fashe da wani irin gunjin kuka.
Chapter 3 · 0% Book details