Sashe 5
Gammon Rama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Fauwaz ya jima yana saka wa Abida ruwa a jikinta, har sai da ya ji zafin ya ragu sannan ya matse rigar ya shanya. Bacci ne ya ɗauke ta, don haka ya fita daga ɗakin yana tunanin yadda za a yi ya saya mata magani. Don har zuciya ta ayyana masa ya je ya samu mahaifinsu ya faɗa masa, amma da ya tuna irin makircin da Tani take ƙulla musu ba su cika kwashewa ta daɗi da shi ba, sai kawai ya haƙura. Ya yanke shawarar fita tsintar gwangwanaye kamar yadda ya ga abokinsa Musa yana yi. Kusan tun gabanin sallar Magriba da ya fita, ba shi ya dawo gida ba sai kusan tara saura na dare. Zuciyarsa a cunkushe take, sakamakon ya sha yawo sosai ya tsinci gwangwanaye da jarkoki, har ya sayar amma bai samu mai chemist ɗin layinsu ba. Sakamakon Peter mai chemist ya je garinsu kirsimeti, kuma shi kaɗai ne mai kemis ɗin da ke zagayen unguwarsu. Tani tana ɗaki ba ta ji shigarsa ba, Fauwaz yana shiga ɗakinsu ya samu Abida a zaune. Sai dai daɗin da ya ji da zazzaɓin jikinta ya sauka, tana ganinsa ta saki murmushi sai shi ma ya mayar mata da martanin murmushin.
"Ya Fauwaz, idan na girma zan gina mana gida mu tafi mu bar su Abba a nan."
Abida ta furta a hankali don kada Tani ta ji, zama ya yi a gefenta ya ce.
"Ai ni ne babba, ni zan fara gina mana gida mu tafi, kuma har sababbin kayan wasa zan saya miki."
Jin haka ya sa Abida ta saki murmushi har fararen haƙoranta suka bayyana.
"Fauwaz! Don Allah, koda wani yanayi da zai gifta wanda zai sauya maka rayuwarka, ka kula da ƙanwarka. Ku biyu Allah Ya azurta ni da su, ku haɗa kanku, ka ja ƙanwarka ka ji Fauwaz."
Kalaman mahaifiyarsu ne ya dawo cikin kwanyarsa ana gobe za ta rasu, idanunsa suka ciko da ƙwalla. Gudun kada Abida ta fahimci damuwarsa ya sa shi saurin kawar da kansa. Suna nan zaune Tani ta ƙarasa ƙofar ɗakin ta ce.
"Kai Fauwaz! Fito ka É—ebo mana ruwa."
Shiru ya yi kamar bai ji ba, saboda gabaÉ—aya ya É—ora rushewar faruncikinsu a kanta. A karo na biyu ta sake yi masa magana, kai tsaye ya ce.
"Yanzu dare ya yi."
Ai kuwa kamar wacca ya kwara wa ruwan zafi a hassale ta ce.
"To tun da ba za ka É—ebo ba, sai na bari idan ubanka ya dawo ya É—ebo mana."
Wani irin É—aci ya ji a ransa, cike da damuwa ya ce.
"Ki daina zagin mahaifina."
Za ta yi magana ta ji motsin shigowar Alhaji, yana ƙarasawa ya ce. "Me yake faruwa hayaniyar me nake ji?"
Tani tana jin haka ta yi zaraf ta ce, "Wai don na ce Fauwaz ya ɗebo mana ruwa yake yi mini rashin mutumci. Ni dai ina jin Alhaji zan bari ka dinga yi masa magana da kanka, don ina gudun watarana na yi masa magana ya zage ni." Fauwaz da zuwansa bakin ƙofar kenan, ya bi Tani da kallon mamakin sharrin da ta yi masa.
Tass! Alhaji ya ɗauke fuskar Fauwaz da mari har sai da ya bugu da jikin bango, da sauri Abida da ke gefe ta riƙe shi a tsorace da hukuncin da Abba ya zartar masa. Abba ya nuna shi da yatsa ya ce.
"Daga yau idan aka sake yi maka magana ka musa sai ranka ya yi mummunan ɓaci. Ka yi maza ka wuce ka ɗauki bokiti ko na tattakaka, sakarai marar mutumci."
Goge hawayensa Fauwaz ya yi, Abida ta ja hannunsa ta yi tsuru-tsuru saboda tsoro. Wani irin kallo suke yi wa mahaifinsu tamkar sun ga sabuwar hallita, domin gabaɗaya ya sauya kamar ba mahaifinsu mai sonsu da nuna musu kulawa ba. Fauwaz yana fita Tani da Alhaji suka rufa masa baya har lokacin bai daina faɗa ba. Fauwaz ba shi ya gama ɗiban ruwan ba sai kusan sha ɗaya saura don Tani har ta kwanta, a lokacin ne ya shiga kicin zai ɗebi abinci ya ci. Sai dai yanq zuwa ya ga sai burbuɗin shinkafa da ƙanzonta. Yadda cikinsa yake ƙugi ne ya kawar da ɓacin ransa, hawayen idonsa ya share sannan ya saka hannu ya kankaro ƙanzon ya zuba da mai ya zauna ya ci. Sai da ya ci ya wanke hannu sannan ya shiga ɗakinsu, a takure a can ƙarshen bango ya hango Abida a duƙunƙune tana rawar ɗari. Da sauri ya ƙarasa wurinta ya ɗago ta yana faɗin.
"Abida! Sannu zazzaɓin ne?"
Jikinta yana rawa ta gyaɗa masa kai, da sauri ya ƙarasa ya ɗauki rigar da ya shanya ya sake jiƙa ta ya shiga saka mata.
"Sannu kin ji Abida, É—azu na samo kuÉ—i don na sayo miki magani amma Peter ba ya nan."
Fauwaz ya furta muryarsa tana rawa, ba ta iya amsa masa ba saboda yadda take jin jiki. Ya jima a haka har ya samu jikin nata ya rage zafi, yana nan zaune rungume da Abida ya ji bacci ya ɗauke ta. Ido ya zuba mata yana kuka, yana tuna rayuwarsu a lokacin da mahaifiyarsu tana raye. Yana cikin wannan yanayin har bacci ya yi awon gaba da shi. Wani irin kakari yake ji sama-sama a cikin baccinsa, jijjigar da jikinta yake yi ne ya farkar da shi daga wahalallan baccin da yake yi. Ɗakin baƙiƙƙirin yake, sakamakon fitilar da ke ɗakin kalanzir ɗin cikinta ya ƙare. Kiran sunanta ya shiga yi a hargitse yana jijjiga ta, sai ya ji jikinta zafi zau kamar wuta. A hargitse ya fita daga ɗakin kai tsaye ya nufi ƙofar ɗakin Tani, daga bakin ƙofa ya tsaya zai fara kiran mahaifinsu. Domin tarbiyyar da mahaifiyarsu ta yi musu kenan, babu wanda yake shiga ɗakinsu ita da mahaifinsu kai tsaye ba tare da an ba su izini ba.
"Abba! Abba ka zo Abida wani abu take yi ba ta da lafiya."
Fauwaz ya furta a É—an ruÉ—e, daga can É—akin mahaifinsu ya ce.
"Kai waye nan?"
Cikin sauri Fauwaz ya ce, "Ni ne Abba, Abida ba ta da lafiya wani abu take yi."
Kamar wanda ya watsa wa ruwan zafi a hassale Abba ya ce, "To ni zan ba ta lafiyar ko yaya? Ko kuwa kawai don ka tashe mu ka katse mana bacci?"
Yana daga waje ya ji muryar Tani tana cewa, "Ni ban san mene ne matsalar yaron nan ba. Wallahi da uwarsa tana raye cewa zan yi ita take kitsa masa duk wani abu da yake aikatawa. To ban da rashin lissafi yanzu idan ya faÉ—a maka me za ka yi mata? "
"Shi ne abin da na gani, kai Fauwaz ka wuce ka tafi zuwa safiya sai a san abin yi."
Abba ya furta daga cikin É—akin, hawaye ne suka shiga sintiri a fuskar Fauwaz kamar an yi masa gorinsu. Har ya juya zai tafi ya ce, "Abba amma da Mama tana raye ba ka mana haka. Na san da tana nan haka ba za ta faru ba..."
"To ka tafi maƙabarta ka dawo ita mana." Tani ta furta da wata irin murya, shi kuma Abba ya ce.
"Lallai wuyanka ya isa yanka Fauwaz."
"Ba irin abin da nake faÉ—a ba kenan, kai ma ka ga rashin kunyarsa ko?"
Tani ta furta cike da zuga da son ƙara tunzura Abba, sai dai har Fauwaz ya fita daga ɗakin bai sake tanka musu ba. Duk da cikin dare ne hakan bai hana Abba ya cigaba da surfa faɗa ba, zuciyar Tani fes ta cigaba da ingiza shi yana hawa. Sai da ta tabbatar da ya gama cika fal da haushin Fauwaz sannan ta sake kwantar da murya ta ce.
"Ni fa Alhaji ina son faÉ—ar wata magana, amma sai ruwan tsoro ya mamaye ni."
Tani ta sauya fuska cikin alamun damuwa, hasken ƙaramar fitilar touchlight ɗin da ke hannunsa ta sake bayyanar masa da zallar damuwar da fuskarta take ciki.
"FaÉ—i mana Tani, ni a kan yaran nan tamkar mahaifiyarsu haka nake kallonki."
Abba ya furta cikin damuwa, Tani ta gyara zama ta cigaba.
"Ni fa sai nake ganin kamar ba iya abin da ya kawo Fauwaz É—akin nan ba kenan."
Cikin rashin fahimta Abba ya ce, "Ban fahimce ki ba Tani."
Tani ta sake muskutawa kusa da shi sannan ta ce, "Ni fa ina zargin sata ce ta shigo da shi."
"Sata!"
Abba ya furta da wata irin murya mai cike da zallar tashin hankali, gaban Tani sai da ya faɗi da ganin mummunan yanayin da ya shiga. Har sai da ta fara tsammanin ko haƙonta a zai cim ma ruwa ba, sai kuma ta dake zuciyarta ta ce.
"Ƙwarai kuwa, saboda ba rana ɗaya ba, ba kuma biyu ba da na taɓa ganin ya shigo mana ɗaki idan muna kwance. Don ko jiya sai da na nemi ɗari biyuna sama da ƙasa na rasa." Ganin zancan kamar yana shigarsa ya sa ta wara hannuwa tana taɓe baki ta ce.
"Ka san an ce idan ba ka iya kama ɓarawo ba, sai shi ya kama ka. Ba na son na dinga yawan faɗa maka laifin yaron nan ka ga kamar ba na ƙaunarsa, ni kuma na ga ɗa ai na kowa ne..."
"Haba Tani, amma me ya sa kika rufe mini magana mai girma kamar wannan?"
Abba ya katse ta a É—an hassale, cike da kissa ta ce.
"Ka yi haƙuri Alhaji In Shaa Allahu ba za a sake ba."
Furzar da iska mai zafi Abba ya yi, zuciyarsa tana zafi ya furta.
"Yaushe Fauwaz ya zama haka? Sata? A cikin gidana? Ina ba zai yiwu ba."