← Book details Gammon Rama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 21

Sashe 12

Gammon Rama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk abin da yake faruwa Zuwaira tana daga ɗaki laɓe a jikin labule tana kallo. Farincii ne ya mamaye ta, don ita kanta ba ta san ya shigo ba sai hayaniyar Inna ce ta tashe ta. Sai da ta ga Malam Hasan ya shige banɗaki sannan ya fito tana yamutsa fuska, kan tabarmar da Inna ta shimfiɗa ta hau ta zauna. Cike da kissa da makirci ta ce.
"Inna lafiya kike ta faÉ—a? Ni ma bacci ne ya kwashe ni da yake ba ni da lafiya, na kira Yaya kuma ya ce mini ya yi nesa da mu ya gangara sabon titi."
Sakin baki Inna ta yi sannan ta ce, "Wato bayan cin amana har ƙarya Hasan ya koya kenan? Dole ya ce miki haka mana tun da yana liƙe a ɗakin baƙar munafukar nan." Zuwaira ta sake narke fuska ta ce, "Ai shi kenan, amma magani fa na ce ya kawo mini ɗazun."

"To idan kika mutu ai ba asara ya yi ba, tun da ba 'yar gaban goshinsa ce babu lafiya ba. Bari ya fito zai zo ya same ni..."

"A'a ki rabu da shi Inna, ni zan yi masa maganar. Idan kika masa zancan muna shiga É—aki a kaina zai huce." Zuwaira ta tari numfashi Inna, Takaici ya sake rufe Inna ta ce.
"Oh ni Kulu na haɗu da ƙaddara, wallahi da na san kalar asirin da uban yarinyar nan ya yi wa Hasan da tuni na ba wa almajiran soro sadaka sun ba yara zikiri an karya shi."
Suna nan zaune Malam Hasan ya fito ya wuce ɗaki, a lokacin da ya shiga Rakiya tana duƙunƙune a cikin zanen gado tana kuka. Sosai ta ba shi tausayi, don har a ransa yana ji su suke cutar da ita a zamantakewar da suke yi. Sannan abin da Inna ta yi masa ba don mahaifiyarsa ba ce, da babu abin da zai hana shi ɗaukar mataki a kanta. Wanne irin abin ne yake damun Inna da za ta shigar masa ɗaki a lokacin da yake keɓewa da iyalinsa? Me ya sa duk cikin 'yan'uwansa babu wanda Inna take yi wa cin kashin da ake yi masa? Me ya sa ba zai samu farinciki ba? Waɗannan tambayoyin ya shiga jefa wa kansa. Shasshekar kukan Rakiya ne ta dawo da shi daga duniyar tunani, ya zauna a kusa da ita ya riƙo hannunta. Da sauri ta fisge ta sake cusa kanta a tsakanin cinyoyinta.

A yadda yake jin tausayin Rakiya, da ace zai iya rabuwa da ita da a take zai ba ta takardarta domin ta samu salamar rayuwa. 'Idan na sake ta ina za ta je? Da su wa za ta fara rayuwa? Shin na yi mata adalci idan na rabu da ita? Ko kuwa na riƙe amanar da mahaifinta ya damƙa mini?' Tambayoyin da ya dinga ƙissimawa a zuciyarsa kenan.
'Koda babu alaƙar aure a tsakaninku, kuma koda mahaifinta bai damƙa maka amanarta ba. Kai mai zame mata uwa da uba ne, domin mahaifinta ya yi maka gatan da iyaye suke yi wa 'ya'yansu.

"Ba zai yiwu ba."

Ya furta a fili cikin suɓutar baki ba tare da ya yi tsammanin zancan zai fito ba. Sake riƙo hannunta ya yi, tana niyyar ƙwacewa ya riƙe ta tsam a jikinsa. Ya kai bakinsa saitin kunnenta cikin tattausan lafazi ya ce.

"Ba zan hana ki kuka ba, ki yi kukan idan har shi zai sanyaya abin da yake cikin zuciyarki."
Kamar Rakiya tana jira, ta sake sakin sabon kukan da kana ji ka san daga ƙasan zuciyarta yake fitowa. Bubbuga bayanta ya shiga yi, har sai da ta ci kukanta mai isarta ya ce.

"Ki yi haƙuri Rakiya, komai ya yi tsanani maganinsa Allah. In Shaa Allahu da jarina ya ƙara ƙwari za mu koma cikin gari, na sani ba a kyauta miki. Ana zalintarki kuma ana, shiga haƙƙinki, amma In Shaa Allahu zan yi bakin ƙoƙarin gyara wasu abubuwan koda ba a daina yi miki duka ba."

Muryarta a dashe ta dube shi ta ce, "Ba na son ka yi abin da zai sa ka saɓa wa mahaifiyarka, ina son ka cigaba da yi mata biyayya. Kamar yadda ka faɗa ne watarana sai labari..."

"Wai ba za ka yi ka fito daga É—akin ba ne Hasan? Ka saka mace a gaba idan ba ka fita nema ba me za a ci?"
Kalaman Inna suka katse maganarta, murya babu walwala Malam Hasan ya ce.
"Yanzu zan fito."
Daga haka ya shiga kintsa kansa sannan ya É—auki kwandon turarensa ya fita. Bayan fitarsa sai da Rakiya ta sake shan sabon kukanta, ta É—auki hijabi ta saka sannan ta fita banÉ—aki domin ta gyara jikinta. Tana fita kuwa Inna ta dasa zaginta Zuwaira ta shiga zuga ta, bayan ta fito har ta kusa shiga É—aki Inna ta ce.

"Ki sako kaya ki fito ga surfen gerona nan kwano uku yana jiranki." Cikin biyayya Rakiya ta amsa sannan ta shiga ɗaki. Kamar yadda ta amsa tana gamawa ta fita ta karɓi geron, tana surfawa Inna tana wanke ta da baƙaƙen maganganu.

A wannan ranar Malam Hasan tun da ya shiga ɗakin Zuwaira ta sha jinin jikinta, amma sai ta nuna kamar ba ta fahimci yanayin da yake ciki ba. Don ko abincinta bai ci ba, dama kuma tun da ta tsiri rashin lafiyar ƙarya ta saka Inna ta sa shi kwana kullum a ɗakinta ya daina cin abincin kirki. Bai fi ya ci cokali ɗaya ya ce ya koshi, a wannan ranar da ta tambaye shi ko kula ta bai yi ba. Yana nan kwance ya ji ta ɗora hannu a jikinsa, cikin zafin zuciya ya fuske ta gefe. Da yake ya san halinta sarai, Zuwaira irin jarababbun matan nan ne da ba su da haƙuri.

"Wai me ya sa kake yi mini haka ne, ko don ka ga na damu da kai? Kusan kullum kafin ka ba ni haƙƙina sai ka wulaƙanta ni."
Zuwaira ta furta a narke cikin damuwa, tashi zaune Malam Hasan ya yi. Ya ji tsanarta ta sake mamaye shi. Da sauri ta É—an ja baya, don ta yi tsammanin mari zai kai mata. Cikin tsana ya nuna ta ya ce.

"Ke wacce irin mai son kanta ce? Ashe kin san halin da kike shiga amma kika sa nake danne haƙƙin Rakiya? Shin kina lissafin yau kwana nawa rabon da na kwana a ɗakinta? Kullum da kalar ciwon da kike tashi da shi, saboda kin san Inna ta tsaya miki ko? To bari ki ji, tun da abin na ki haka ne ni ma daga yau babu wani abu da zai sake shiga tsakanina da ke."
Da sauri ta ɗago ta dube shi, ganin babu alamar wasa a fuskarsa ya ta miƙe ta ce.
"Ai kuwa dole Inna ta ji, don wallahi ba zan yarda ba."
Tana gama faɗa ta ɗaga labulen ɗakin, cikin ɓacin rai ya nuna ta da yatsa ya ce.

"Wallahi tallahi kin ji na rantse miki, idan har kika sake kika fita daga ɗakin nan sai na sauke igiyar aurena uku da suke kanki. Sakarai wacce ba ta san sirrinta ba, ballantana na mijinta. Wai ganin ina yi wa Inna biyayya gani kike ba zan iya rabuwa da ke ba? Bari ki ji, daga yau za ku cigaba da raba kwana bibbiyun da kuke yi a baya. Idan kuma hakan bai yi miki ba sai na sauwaƙe miki, ƙarƙari na ɗauki matata na bar garin ba tare da kowa ya sake gani na ba."

Yadda ta ga ransa ya ɓaci jikinsa har yana rawa ya sa ta shiga hankalinta, don ta san shi sarai yana da matuƙar haƙuri amma idan ransa ya ɓaci ba ya ji ba ya gani. Jiki a mace ta koma gefen gado ta kwanta, Malam Hasan ya miƙe ya zira doguwar rigarsa ya fice daga ɗakin kai tsaye ya wuce ɗakin Rakiya. Tana gani ta gefen labule ya shiga ɗakin Rakiya, amma yadda take ƙaunar Malam Hasan ya sa ta ji ba ta shirya rabuwa da shi ba. Don haka ta koma ta kwanta tana hawaye, saboda wani irin zafin kishinsa da take ji.

Tun daga wannan ranar Malam Hasan ya raba musu kwana, kuma koda Inna ta ga haka da ta fara faɗa Zuwaira da kanta ta shiga kare Malam Hasan da cewar ita ce su cigaba da kwanansu kamar yadda suke yi saboda ta samu lafiya. Hakan ya sa Rakiya ta samu 'yancin kwana da miji, sai dai wasu ƙalaubalen da ba a rasa ba waɗanda ta yi sabo da su har suka zamwemata jiki.
An yi haka da wata biyu Zuwaira ta samu ciki, tun bayan da ta yi ɓatan wata ta fara tsiro da rashin lafiya duk da cikin mai sauƙi ta same shi. Inna tana ganin haka ta tasa ta a gaba suka tafi asibiti, sai ga shi gwaji na farko aka tabbatar da tana ɗauke da cikin wata ɗaya da sati ɗaya. Tun a asibitin Inna ta kira Malam Hasan ta sanar da shi, bayan da suka je gida a ranar wuni ta yi tana habaici da yarda wa Rakiya maganganu. Malam Hasan abu biyu ne ya haɗe masa, na farko yana farinciki da Allah ya sake azurta shi da rabo. Sai dai ya so a ce a jikin Rakiya ne, na biyu kuma yana fargabar sabon ƙalubalen da Rakiya za ta fara fuskanta daga wurin Inna. Don tun a ranar da aka tabbatar da cikin Inna ta kira Rakiya, ta kafa mata dokaki dangane da aikin cikin gidan.

"Ke Rakiya ina ce dai kin lura arziki ya ƙwanƙwanso mana ƙofa, wacce ta kasance irin albarka ta buɗe masa." Shiru Rakiya ta yi, don ba ta fahimci kalaman Inna ba.
"To ina nufin ciki Zuwaira gare ta, don haka ba kowanne aiki za ta dinga yi ba. Na faɗa miki ne domin idan kina da wani shiri ki ɗaura ɗamara, domin wannan cikin sai an haife shi lafiya kuma ya taka ƙafa shi ma ko ita ma sun hayayyafa. Domin mu gadon haihuwa ne ba juya ba."
Rakiya ta ji wani abu ya soki zuciyarta, amma sai ta danne ta saki murmushi ta ce. "Ma Shaa Allah, wannan abin farinciki ne. Allah Ya buÉ—i ido lafiya."
Chapter 12 · 0% Book details