Sashe 19
Gammon Rama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
_Har yanzu na san zuciyarka tana cike da wasu-wasi a kan kalaman da na furta maka, ina son ka sani. Ni Tani dama ina tare da kai ne domin biyan buƙatar kaina, a yanzu kuma na cimma manufa ta dole na wurgar da ƙwallon mangoro na huta da ƙuda. Ina tunasar da kai da ka sani, Tanin da ka sani a shekarun baya, ita ce dai wacce ka yi rayuwar aure da ita a yanzu. Girma da shekaru ba su isa su sauya Tani ba, idan Tani ta ce sai ta yi duk daren daɗewa sai ta zartar da shi. Zan sake sanar da kai, wallahi tallahi ko kana so ko ba ka so dole ka sake ni. Ka saurari haɗuwar da za mu yi a gaba._
Abba yana gama maganar ya ji gumi ya shiga keto masa, ɗayar takardar da ke gefe ya ɗauka sai dai tun kafin ya buɗe ta ya ga a ido ta fi wacce ya gama karantawa tsufa. Yana buɗe ta bayan ya ƙura mata ido ya ji gabansa ya yi mummunan bugawa, zanen rubutun da aka yi da baƙin biron da ke jikin takardar ya tuna masa da tarun al'amauran da suka faru a shekaru goma sha bakwai da suka wuce. Da sauri ya wurgar da takardar, sai ya ji tamkar ya riƙe ruwan dalma a hannunsa. Ya kifa kansa a sama cinyarsa yana faɗin.
"Innalillahi wa inna'ilahir raji'un!"
Shiru ya yi yana jin zuciyarsa tana yi masa raÉ—aÉ—i, raÉ—aÉ—in da ya gagara tantance a mahallin da zai ajiye shi. Musammam da ya tuna shukar tsiyar da noma wa Tani a shekarun baya.
Gobe za mu gama free pages É—inmu🥳 jama'a yanzu ne za a fara naÉ—a GAMMON RAMA, kowa yasan za a sha tsami a cikinsa. Akwai tarin Æ™alubale da darussan hannunka mai sanda, kada ku yi sanya domin yanzu ne za a fara wasan.👌ðŸ»
500 ne ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan lambar 07062062624 idan ya kammala zuwa document 800 ne.
Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624
[20/05, 16:30] Ameerah Adam: *GAMMON RAMA*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
GargaÉ—i: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba.
Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne.
SHAFI NA GOMA
Abba ya jima a zaune cikin rashin daɗin yanayi, jikinsa a sanyaye ya miƙe ya shiga ɗakin su Fauwaz. Tsaye ya yi yana ƙarewa ɗakin kallo, abubuwa da dama suka shiga dawowa cikin kwanyarsa ciki har da mutuwar Abida. Sai a lokacin yake tuna irin kalaman da Tani take yi masa a kan 'ya'yansa, da irin shakulatan ɓangaro da ya yi a game da amanar da mahaifiyarsu ta ba shi kafin ta bar duniya.
"Kaico Abidata, Allah Ya sabunta rahama a gare ki da mahaifiyarki."
Ya furta a sanyaye, sai kuma Fauwaz ya faÉ—o masa, cikin nadama da danasani ya ce.
"Yanzu É—an cikina ne a almajiranci? Shin me ya faru da ni a wancan lokacin da na gagara gane gaskiyar da yaron nan yake son nusar da ni?"
Amsar da ya gagara ba wa kansa kenan, shi kaÉ—ai ya shiga surutan nadama a kan cuzgunawa su Fauwaz da suka dinga yi a baya shi da Tani.
"Ya zama wajibi na je na dawo da shi gabana."
Ya furta a sanyaye, sai kuma wani tunani ya faÉ—o masa don haka y furzar da iska mai zafi ya ce.
"A ina zan samu kuÉ—in mota?"
Saboda a wannan a gaɓar da yake hatta naira ɗari ta kansa wuya take yi masa, ganin rubuta wasiƙar jakin da yake yi ba za ta kai shi ba. Sai ya miƙe ya fito, ya shiga ɗakin kwanansu. A nan ma ɗakin ya shiga bi da kallo ganin Tani ta yashe komai nata, hularsa da ke yashe a ƙasa ya ɗauka ya saka. Tunanin zuwa gidan kawun Tani ne ya faɗo masa, don haka cike da ƙwarin gwiwa ya rufe gidan ya nufi shagon Nalami da ke bayan gidansa.
Nalami yana ganinsa ya haÉ—e rai, Abba ya saki murmushi don ya san dalilinsa na sauya fuska.
'Tabbas rayuwa darasi ce, sautari idan kana da shi mutane kowa ƙaunarka yake. Amma da zarar wata jarrabawa ta afka maka a nan ne za ka fahimci wanda zai mu'amalance ka tsakani da Allah.'
Abba ya raya a ransa, sannan ya yi sallama a shagon. A ɗan daƙile Nalami ya ce.
"Wa alaikassalam."
Abba ya É—an yi jim sannan ya ce. "Don Allah Nalami kada a gaji da ni, yanzu ma aron É—ari biyu za ka ba ni, idan aka haÉ—a da waÉ—ancan sun kama dubu É—aya." Kamar Nalami yana jira ya yi zaraf ya ce, "A gaskiya Alhaji ba za ta samu ba, waÉ—ancan ma yanzu nake shirin aika maka kuma sai ga ka."
Nalami ya ƙarasa kalamansa yana ƙara tsuke fuska.
"Alhaji kana da canjin É—ari takwas fa."
"Alhaji ka biyo ni É—ari biyar jiya."
"Kullum dai Alhaji ba ka gajiya, to an gode Allah amfana."
"Gaskiya ne Alhaji, ni fa duk unguwar nan na fi jin daɗin cinikinka, saboda ko babu komai mutum zai ƙaru da 'yan canji."
Abba ya tuna ire-iren kalaman Nalami a baya, a lokacin da kuÉ—i yake gara masa idan ya zo sayayya wurinsa. Don a wancan lokacin canji indai ba mai yawa sosai ba ne bar wa masu shago yake, musamman Nalami da ya fi kusa da gidansa. Amma shi ne a kan dubu É—aya Nalami yake É—aure wa fuska har yana nuna masa iyakarsa.
'Marar shi ba ya zuciya.'
Abba ya sake raya wa a ransa, don haka ya ce.
"Don Allah ka taimaka mini Nalami, zan yi ƙoƙari na haɗa maka kuɗin cikin ƙanƙanin lokaci."
"A gaskiya wannan ne na ƙarshe indai ba ka kawo wani abin ba na gama ba ka rancen kuɗi."
Nalami ya furta sannan ya zaro ɗari biyu ya miƙa masa a wulaƙance, idanun Abba ne suka ciko da ƙwalla. Ganin a kan ɗari biyu ana ƙoƙarin cin zarafinsa, ɗari biyun da yake ganin ba komai ba ce a wurinsa. Karɓa ya yi ya masa godiya ya tafi, a wancan lokacin da yake kuɗi suna da daraja. Ɗan achaɓa ya tara ya nufi unguwar Sheka gidan Kawun Tani.
A lokacin da ya ƙarasa Dattijon yana zaune a kan bencinsa ƙofar gida, cikin girmamawa Abba ya russuna ya ce.
"Barka da yamma Baba."
FaÉ—aÉ—a fara'arsa Dattijon ya yi ya ce, "Barka dai, au Lawan ne da yammacin nan?"
Abba ya É—an sosa kai ya ce, "Eh ni ne Baba, ya mutanen gidan?"
Baba ya nuna masa tabarmar da ke gefen bencin ya ce, "Ga wuri ka zauna mana, ya su Tani?"
Abba har ya miƙe domin ya je ya zauna, sai ya ji gwiwarsa ta yi sanyi da tambayar da Baba ya yi masa. A saɓule ya zauna ya yi shiru ya faɗa tunanin wurin da Tani ta tafi, har sau biyu Baba ya yi masa magana bai ji ba. Sai da ya taɓa shi bayan Abba ya amsa Baba ya ce, "Lawan ko wani abu ne ya haɗa ka da Tani? Ina fatan dai lafiya ko?"
Abba ya shafo gemunsa ya ce, "Eh to gaskiya ba lafiya ba Baba..." Duk abin da ya faru Abba ya kwashe ya ba wa Baba labari, sannan ya É—ora da cewa.
"Shi ya sa na ce bari na zo nan, don na san duk garin nan babu wanda take da shi sama da kai. Da har zan je gidan abokin mahaifinta, sai na ga nan ne ya dace na zo tun da ka fi kusanci da ita." Gyaran murya Baba ya yi ya ce.
"Eh kam tabbas haka ne, ni na fi kusanci da ita a kan Alhaji Harisu, tun da a lokacin da muka yi zaman Shagamu da mahaifinta Alhaji Harisu bai zo garin ba sai dab da mahaifinta zai rasu. Ni da shi bacci ne yake raba mu amininsa ne ƙud da ƙud."
Da É—am rashin fahimta Abba ya ce, "Baba kana nufin kai ba yayan mahaifinta ba ne?"
"Yayan mahaifinta? Ita Tanin ce ta ce ni ne yayan mahaifinta?"
Baba ya furta da sauri, Abba ya gyaÉ—a kai ya ce.
"Eh haka ta ce mini bayan haÉ—uwarmu, shi kuma Alhaji Harisu abokin mahaifinta."
"Tirƙashi! Lallai yarinyar nan makira ce, ashe haka ta iya yaudara? To wallahi yaro babu abin da na haɗa na jini da Tani, ni ban san ma yadda aka yi ta lalubo gidana ba. Ta zo da kukanta wai aurenta ya mutu ba ta da wurin zama, ganin irin zaman mutumcin da muka yi da mahaifinta ya sa na ba ta ɗaki. A lokacin har zance ta tafi dangin mahaifinta ko mahaifiyarta, to sai na ga kamar ba za ta ji daɗi ba tun da ta san da can ɗin ta taho wurina." Baba ya ƙarasa maganar yana sakin ƙwafa, sannan ya ɗora da cewa.
"Ni ban san lokacin da Tani ta lalace haka ba, kodayake tun haɗuwarta da wani ɗan iskan yaro a shekarun baya duk ya lalatata. Allah dai ya kwashe masa albarka, duk ya gurɓata tunanin yarinyar nan."
Shi dai Abba zuru ya yi kamar an jiƙa ɓera a buta, haka kawai jikinsa yake ba shi kamar shi ake kwashe wa albarka yana zaune.
"To yanzu Baba a ina kake ganin zan iya ganinta?"
Abba ya tambaye shi cike da damuwa, cikin sauri Baba ya wara hannuwa ya ce. "Allah masani Lawan, don wallahi ba na ce ba. Ka leƙa gidan Alhaji Harisu ƙila ko can ta nufa, ni kuwa dama ta gama zaman gidana don ba za ta haɗa mini masifa da kafirar ƙaryarta ina zaune ƙalau ba." A sanyaye Abba ya miƙe har zai saka takalminsa ya ɗan sunkuyo ya ce.
"Amma Baba ya sunan yaron da ka ce ya cuce ta ya gurɓata mata tunani..."
"Kai da ka zo neman matarka ina ruwanka da wani ƙato?"