Sashe 9
Furar Danko Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Tun daga wannan magana Lulu ta koma musu shiru-shiru a gidan, dama ga yanayin rashin jin daɗin jiki da take fama da shi, wanda zuwa yanzu take kallon hakan a matsayin zubar mata da cikin da akayi ne. Su kuma su Dada ke fassarawa da asiri Smart yay mata kawai. Duk yanda Tajuddeen ke son shigema Lulu taƙi bashi fuskar hakan. Dole ya koma baya-baya da ita amma hakan na damunsa. Bama shi ba hatta su Dadan ta tattara ta watsar kamar bata san da su a gidan ba. Ummita kawai take kulawa dan yarinyar nada hankali da nutsuwa. (Ummita ta taɓa aure harda yara biyu, sannan zata iya girman Lulu kaɗan, wahalar da tasha wajen mijinta yasa bayan ya saketa iyayenta sukace bazata zauna musu a gidaba ta tafi wajen ƙanwar mamanta a Abuja. Karatu ta koma, bayan ta kammala rashin samun madogarar aiki ya sata amsar wannan aikin zuwa Canada ta hanyar Hajiyan Shuwa maƙwafciyar ƙanwar mamanta).
Duk da abinda Lulu ke musu duk abinda tace tana so sai Tajuddeen ya fita neman mata shi a cikin garin koda yana tunanin bazai samu ba. Duk da dai ma babu abinda tafi nacemawa a yanzu kamar kunun gyaɗa da fruits. Ita kanta har mamakin kanta take akan shan kunun gyaɗar nan na ƙaddara daya sarfaceta. Dan ita a baya ba gwanar shansa bace ba, zama ta iya rantsewa a ɗan zaman datai gidan Aliyu ne ta koya shansa. Sunan Smart da yazo mata a zuciya ya sata jan ƙaramin tsaki. Ɓal-ɓal taji cikinta ya bada har sai da takai hannu samansa ta dafa. Sai kuma akai shiru. Bata kawo komai a ranta ba ta watsar da batun Smart gefe da kan faɗo mata a rai musamman idan tayi wani abu haka daya tuno mata da zaman nasu. Sannu a hankali jikinta kuma sai ya fara sauƙi, zuwa lokacin Alh. Sulaiman da Tajuddeen sun wuce wai duba Baba Garko, sai dai a baɗini shi Alh. Sulaiman nashi zuwan akwai manufa. Ganin Lulu ta samu sauƙi ta murmure sosai sai ma wata ƴar ƙiba da murjewar jiki da ta fara. Dan tayi wani irin ƙyau na farat ɗaya da haske tare da ƴar ƙiba. Zuwa yanzu babu abinda ke damunta sai ɗan zazzaɓin dare. Da zaran ance sha biyu tayi zazzaɓi zai rufeta, zuwa gabannin asubahi kuma sai ya sauka ta wayi gari garas tamkar komai bai faru ba. Shan kunun gyaɗa kam sai abinda yay gaba. Tana nan tana abunta. Tun Dada na maganar wannn shan kunun gyaɗa data laƙama suna na fitina har ma ta kawo ido ta zubama Lulun kawai.........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7️⃣
........Kwanan Dada goma sha ɗaya ta fara shirin komawa wajen mijinta. Lulu ko ta maƙale tace ƙafarta ƙafarta dan bazata sake zama ita kaɗai anan Canada ba ciwo ya halakata. Cikin lallashi Dada ta nuna mata bazai yiwu ba, ta kwantar da hankalinta ai Tajuddeen na dawowa nan ɗin duk da ba'a gidan zai zauna ba. Tsaf ta tubure cewar ai ita ko ƙasa ɗaya ma bazata zauna da shi ba. Tunfa Dada na lallashinta harta birkice mata da masifa cikin ɓacin rai. Amma hakan baisa Lulu ta yarda zata cigaba da zama a Canada ba. Sai ma cewa tai ita gida Nigeria zata koma to. Tofa babbar magana, hankalin Dada ya tashi, dan tasan taurin kai irin na Lulu sarai. Alh. Sulaiman tai kira ta sanar masa. Washe gari sai gashi ya sake dawowa Canadan. Shima balbale Lulu yay da bala'i tare da zageta tas ita da Daddy sannan ya saka Dada tattaro masa passport ɗin Lulun da komai da zai iya taimaka mata fita a ƙasar ya wuce da su harda na Ummita ma. Wannan abu ya tada hankalin Lulu, hakama Dada sai al'amarin ɗan nata ya fara bata mamaki kuma. Dan sai take ganin ya zafafa da yawa, miye na ɗauke passport kamar wasu masu son kidnapping yarinya?. Amma ta kasa iya masa magana dan harga ALLAH tana shakkar ɗan nata kasancewarsa ba kanwar lasa bane ba.
*_NIGERIA_*
Alh. Sulaiman ya koma Nigeria bisa matsawar Tajuddeen dole yakai kotu akan alƙali ya saki Lulu, amma sai ya bashi amsa da cewar sai ma'aurata duka sun gurfana a gabansa zai iya aikata hakan. Zancen ya matuƙar bashi haushi ya yayyaɓama alƙalin magana duk da kuwa suna mutunci. Shiko yay biris da shi dan yace bazai aikata abinda ya saɓaba, taya zai kama kashe aure ma babu masu alaƙa da auren kamar a garin da babu shari'a, to yace yamawa hukunci kenan. Kusan alƙalai biyu ya sake tunkara bayan na farko amma amsar duk iri ɗaya ce suma since sai ma'auratan sunzo, dan koda aka aika sammaci gidan su Smart sai akace ma nai kai takardar ai Smart bama ya ƙasar, bakuma asan randa zai dawo ba ma. Alƙalin ƙarshe ne ya bukaci ganin iyayen Smart. Koda Abba yaje sai ya nunama Alh. Sulaiman yafisa sanin takan duniya, dan cayayma alƙali ai yaron da matarsa suna tare acan turai, shi Alh. Sulaiman shirmensa kawai yake yi, yasa a kira masa Smart a waya, akayi kuwa sa'ar samunsa, sun tattauna sosai da alƙalin akayi sa'a kuma shima Smart ɗin yace yana tare da matarsa Alh. Sulaiman yana shirmensa ne kawai saboda yana son raba auren dan taƙi ɗansa. Alƙali kuwa ya samu Alh. Sulaiman yay masa tas tare da gagaɗin yabar wannan shirmen da zubda mutunci yara su rayu da juna tunda sunce suna tare, ɗanshi kuma yaje ya nema wata. Wannan makirci ya matuƙar ƙona masa zuciya, dan haka ya ƙullaci Abba a ransa da fara shiri na musamman....