Sashe 51
Furar Danko Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣9️⃣
.......Sai dai yana waigawa ta rufe idanun ita a dole barci take. Nasa idanun ya rufe da sakin guntun murmushi ya ƙarasa shiryawa ya miƙe. Wando yasa 3quater da ƴar riga armless yasa turare. Baice da ita komai ba ya fita domin duba mima zai bata taci ne duk da yasan halinta bawai ta damu da abinci bane. Ganin babu wani abinda zata iya so sai kawai yay mata order na gasashen kifi da abinda yasan zata iya so. Cikin abinda baifi mintuna ashirin da biyar ba aka danna bell ɗin gidan. Tashi yay zuwa ƙofar dan yasan abinda yay order ne aka kawo. Shi ɗinne kuwa. Mai kawo saƙo ɗin na ganin shine ya wani washe baki, cike da zumuɗi da farin ciki ya ce, “Smart Mawashi”.
Murmushi Smart yay masa. Shi kuma ya zaro wayarsa yace Please ya bashi dama suyi hoto ɗaya. Kai ya jinjina masa alamar babu damuwa. Ya gyara sukayi sai farin ciki yake yi. Shi kuma ya amsa kayan ya koma ciki. A falon ya ajiyesu ya nufi bedroom ɗin.....
*_NIGERIA_*
Kamar yanda ta saba a ƙarshen kowane wata take sake ƙulla silin zare ɗaya a jikin battar da malamin ya bata game da asirin da taima Smart da Lulu. Yau ma cikin nishaɗinta ta jawo battar hannunta riƙe da farin zaren kirtani tana ɗan raira waƙarta ta barmani coge alamar dai tana a cikin nishaɗi. Dan bayan Aunty Amarya da Ammah ta sanar mawa babu wanda yasan yau Lulu ta koma wajen mijinta a gidan.. Wani irin kwance-kwance ƙirjinta yay ya yanka lokacin da take jawo battar idanunta ƙyar akan zararrikan data ɗaura zube ƙasa a warware. Battar ta tukunyar ƙasa ƴar ƙarama ta wani tsage daga sama har ƙasa. Tana ɗagata ta rabe biyu tsokokin nama biyu da suka wani tsotse a waje guda tsire da allurai suka zube a ƙasa. Ƙara ta daddage ta fasa na tsananin fita hayyaci da tashin hankali batare data farga da ɓaranɓaramar da take neman yi ba. Su Huwaila dake falo suna kallone farkon shiga a ɗakin nata a gigice. Ganinta kwance wanwar a ƙasa babu numfashi ga wata ƴar tukunya-tukunyar tsafi zube a ƙasa harda allurai a jikin tsokar nama ya sasu suma fasa ƙararar data ankarar da su Ammah. Kusan a tare suka afko ɗakin tare da gayyar yaran gidan. Babu wanda idonsa bai gane masa wannan tarkacen tukunya ba idan ya shigo, har Abba da ya shigo a ƙarshe dalilin kiran da Salis yaje yay masa akan tarkacen ya fara sauke ido kafin Ummah dake kwance wanwar ana sheƙa mata ruwa amma babu alamar numfashi tattare da ita.
Wani irin harbawa ƙirjinsa yayi tare da jin kansa ya sara. Yana sake maida idonsa akan Ummah ya ga ta koma masa wata irin mummunar hallita. Da sauri ya kauda kansa yana mai ambaton sunan ALLAH. Yanda yay baya zai faɗi sai da Ammah ta tarosa tana faɗin, “Ya Salam Abbansu yi ahankali”.
Hannun Ammahn ya riƙe yana jujjuya mata kai, muryarsa na rawa ya ce, “Hafsat fiddani a ɗakin nan kaina zai fashe”.
Furucin Abba yasa gaba ɗaya hankalin sauran yaran da su Aunty Amarya dawowa kansa. Sai kuma hankalin kowa ya sake tashi ganin halin da Abba ke a ciki. Amma mi abin mamaki yana fitowa ya saki wata nannauyar ajiyar zuciya da sakin kan. Kallonsa Ammah tai da faɗin, “Yaya dai Abbansu?”.
Kamar bashi ya gama cewa kansa kamar zai fashe ba ya ce, “Wlhy Hafsat kinji kuma ya saki kamar ba'ayi komai ba.” Sosai abin ya ɗaure kanta. Bata gama fita a mamaki ba kuma sai ga yaran na fitowa da ɗaɗɗaya hannayensu dafe da kansu. Wasu ma a guje suke faɗin, “Dodo! Dodo!!”. Cikin ƙanƙanin lokaci gida ya gama rikicewa. Kowa ya fito a ɗakin Ummah, da kuma sun fito sai su jisu sakawai kamar an zare musu komai. Umma da hayaniyarsu ta sakata farfaɗowa cikin tashin hankali tabisu da kallo ganin yanda suke fita a guje. Ganin babu kowa sai taga damace ta sameta ta tattare kayan nan. Da sauri ta tattarasu jikinta na mazari ta ɗaure a ɗan kwali ta tura ƙarƙashin gadonta. Sannan ta fito cikin ƙarfin hali. Tana sakko ƙafarta waje yaran suka shiga yanka ihu suna kwasa da gudu zuwa ɗakunan iyayensu da faɗin, “Wayyo Umma ta zama dodo! Ummah ta zama dodo!”. Ba yaran kawai ba sai ga su Aunty Amarya suma duk sun rufta ɗakunansu. Abba ma har tuntuɓe yake na barin wajen sai Ammah ce ke kallonta da ambaton addu'oi a bakinta. Dan itama kam yanzu a wata irin mummunar siffa mara ƙyan gani tane kallon Ummahn. A nutse ta nufi nata ɗakin itama aka bar Umma ita ɗaya a tsakar gida cikin tashin hankali da mamaki. Sai kallon jikinta take taga minene sukema gudu amma bataga komai ba. A take jikin nata ya kama rawa. Ɗakinta ta koma ta jajibi waya tai kiran Hajiya Naqiba....
*_★UK★_*