Sashe 68
Furar Danko Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Ana kwana na biyar da kama Alhaji Sadi Dikko Aunty Bilkisu da Iya tabawa suka iso Unitet Kingdom tare da Ahmad. A ranar Smart baya gida sunje buga wasa. Sai Lulu ce taje tarbarsu duk da Ahmad yasan gidan. Sosai aunty Bilkisu da duk take a tsorace ta samu nutsuwa da ganin Lulu, cikin farin ciki suka rungume juna. Hakama Iya Tabawa yau Lulu harda rungumeta, yayinda Ahmad ya caɓe yaronsa a hannu shima. Cab suka shiga har gida, dan Lulu bata driving anan kasancewar bata da lasisi. Sai Smart kawai. Daga Aunty Bilkisu har Iya Tabawa gidan ya birgesu sosai. Sunata santi da jera addu'a ga Smart. Abincin da Lulu ta shirya musu sukaci, bayan sunyi nak Ahmad yace zai wuce can ya samu Smart. Zuwa gobe sa dawo tare ɗan ba'a ranar Smart ɗin zai dawo ba. Tafiyar Ahamd ta sake basu damar ɓararrejewa, dan ma Aunty Bilkisu ba daɗin jikinta take ji ba sai ƙarfin hali kawai. Sun ɗan taɓa hira kafin Lulu ta kwashesu zuwa asibiti dan a yau take son aunty Bilkisu ma ta fara ganin likita. Kuma ko Smart baisan da hakan ba, dan shi nashi shirin kawai sai ya dawo ya kaita da kansa.
Kasancewar Usman da Dr Lameer ne suka haɗasu da likitan basu wani sha wahala ba na ganinta. A take aka bama aunty Bilkisu gado. Abinka da inda aka san darajar ɗan adam babu ɓata lokaci suka fara mata gwaje-gwaje da duk abinda ya dace. Koda Smart yay kiran Lulu bayan sun tashi a wasan bata sanar masa suna asibiti ba. Sun dai gaisa tai masa congratulations dan ganin sunci wasan suka ɗanyi hirarsu ta soyayya sukai sallama. Da yace ta haɗashi da su yay musu barka da zuwa Iya Tabawa kawai taba tace aunty Bilkisu na barci. Bai kawo komai a ransa ba ya yarda. Sallama sukai fan yana tare da Ahamd daya sameshi a can. Da ga haka itama ta cigaba da kai kawonta tare da Dr Lameer dake taimaka mata. Kasancewar mai jiyya ba zama yake a asibitin bayan ayi mata abubuwan da duk suka dace na wannan lokacin suka dawo gida, sai bayan wasu awoyi zasu koma dubata kuma......
*_★9ja★_*
A gidan Baba Garko suna akaci na kece raini da nunawa tsara. Dan ƴan biyu kam sunyi goshi matuƙa sannan sunzo da farin jini a wajen dangi. Kai da kaga taron nan kasan da gayya akayisa. Kasancewar su kansu dangin Baba Garkon ba daɗin Dada sukeji ba yasa a wannan gaɓar suke maida murtanin bashin gaba. Dan raƙashewa akai iya raƙashewa. Ga matan ƴaƴansa da jikoki cike taf da gida. Su kansu ƴaƴan dole sukazo kowa kuma da tsarabar suna. In ba haka ba kaci ubanka hannun mai gayya mai aiki. Alh. Sulaiman ne kawai babu, amma iyalinsa duk sun zo a sace batare da ya sani ba. Dan sukam dai basu yarda sun saka kansu a cikin faɗan iyaye da ɗansu ba. Hajiya Turai kuma tsaye take akan ƴaƴanta bata basu fuskar da zasu guji kakanin nasu ba. Tace babu ruwanta suma babu ruwansu. Ko Tajuddeen dake a cikin case ɗin tsundum cikin hikima ta dawo dashi ga kakaninsa tsundum. Dan tasan abinda take yi.
A yanda Dada ta koma laƙwas sai ta baka dariya ma da tausayi. Ba komai ya jawo hakan ba kuma sai kufcewar duk wata power nata. Gaba ɗaya ta fahimci komai fa ya gudu. Dan hatta matan ƴaƴan nata da take bama gwale-gwale yanzu kar suke kallonta. Bama sa shakkar dubar tsakkiyar idonta su yaɓa mata habaici a kaikaice. Karo na farko a rayuwarta datai kuka mai yawan gaske a dalilin tuna mahaifiyar Lulu. Tasha gaya mata gaskiya akan ta rage tsananin da takema matan ƴaƴan nata, in ba hakaba watarana sai sun nuna mata sun fita iyawa. Hakama dangin babansu ta daina musu wulaƙanci musamman marasa shi ɗin nan, kada wataran a auro wata a gidan ta riƙesu su rama duk cin kashin da take musu. Amma akoda yaushe saita hantareta harma da zagi saboda takaici da baƙin cikin ta kira mata kishiya, takance badan tana kama da Baba Garko ba itako da tace an mata misayarta a asibiti ne. Iya ƙoƙari Mawaddat tayi a kanta wajen gaya mata gaskiya akan abubuwa da yawa, yau gashi bata kusa da ita balle taji mata ciwon abinda ke faruwa. Dan ta kula ƴaƴa mazan nan fa ƴaƴansu da matansu kawai suka sani, tunda gashi kowa gani yake ta tsananta da kishin amaryar ubansu, ko kunyar faɗa mata hakan basa ji. Ko yau da safe Uncle Khamil da yazo sunan shi da nasa iyalin takanas da ga Abuja sai da yay mata irin wannan ƙorafin. Hakama autanta daya aiko da shatara ta arziƙi tun daga Saudiya. Gaba ɗaya saita fahimci goyon bayan mahaifinsu suke sam bata sonta ita yanzu. Babu abinda yafi ƙona mata rai da zuciya sama da saƙon Lulu, ita sai yanzu ma take sanin wai Lulu bata Nigeria tabi mijinta, bama wannan ba, shi kansa Smart ɗin bata san ya zama wani abu ba sai yanzu.........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣0️⃣
.......Haka dai ta yini a ɗaki tana ƙulla wasikar jakai, sai wanda yaga dama yake shigowa gaisheta da jiki. Kowa yana tsakar gida yana raƙashewarsa hankali kwance harda su DJ suka saka Dan taro akai fa na gani na faɗa a harabar gidan. Ga abinci da kuɗi ana bishasha kamar ba gobe. Babu wanda ya damu dawai cewar Dada nada hawan jini bari a sassauta. To kowa sha'aninsa yake kamar ya manta da ita a gidan, sai ƴayanta ne kan ɗan leƙata time to time. A ƙarshe dole sai da likita yazo dubata. Washe gari da Uncle Khamil zai wuce ya roƙi Baba Garko ya bari ya wuce da ita Abuja ta ɗan huta. Cayay shi babu ruwansa duk ma inda zata taje. Wannan kalma ta sake sanyaya musu jiki. Yayinda Dada ta ɓarke da kuka akan ita babu inda zataje, ba komai ta tuna ba sai wahalar da tasha a hannun matar Uncle Manner. Babu yanda basu lallaɓata ba tace wlhy babu inda zataje garama idan mutuwa ce ta ɗauketa a ɗakinta yafi mata. Dole suka barta suka wuce....
(Su Dadancy anji gwale-gwale 🤣🤣🚴)
_______★