← Book details Furar Danko Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 90

Sashe 57

Furar Danko Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

    Sosai tasha barci, dan ko da lokacin salla yayi da ƙyar ya iya tashinta tayi ta sake komawa. Bata tashi ba sai gab da la'asar. Yana falo suna kicimilli da ɗansa ta fito. Tsaye kawai tai tana kallonsu har bata san tana murmushi ba. Mayataccen ƙamshinta ya fargar da Smart kasancewarta a wajen. Zaune ya tashi da ga kwancen da yake yana ɗaga AA dake sukuwa a saman cikinsa. Cikin lumshe ido da sakar mata murmushi ya ce, “Kin tashi?”. Cikin falon ta ƙarasa takowa tana marairaice fuska. Hannunsa ya miƙa mata alamar tazo garesa. Babu musu ta ƙaraso, ya riƙo hannunta ya zaunar gefensa yana mai rungumota ta gefen jikinsa kanta a saman kafaɗarsa. AA dake neman haye mata jiki ta dungurema kai batare da tayi magana ba. Smart dake kallonsu da murmushi ya shafo fuskarta da faɗin, “Yaya jikin naki?”.
       “Ba sauƙi”.
    Ta bashi amsa cikin tura baki.
Sosai ya waro idanunsa waje. “Ba sauƙi fa Nooru Nisa”.
      Fuska a gimtse ta ce, “Eh mana dan ni dai jikina ciwo yake mun har yanzu”.
     “Kai Madam bansan ragwantaka fa. Ni da nake shirin yanzu a sake tafiya yaƙin ƙasa da ƙasar again.”
           “Dawa?!”.
      Yanda tace dawa ɗin cikin waro idanu da ƙwaɓe fuska kamar zatayi kuka ya sashi kwashewa da dariya. Mintsini mai zafi ta sakar masa tana miƙewa. Ya riƙe wajen da sauri yana yamutse fuska da faɗin, “Wai ALLAH na! wannan zalincin fa? Kefa kin iya mugunta”.
    Gwalo ta masa tana dariya, ta ce, “Mugayen ai da yawa kai ne malamina”. Tai wucewarta kitchen Dan yunwa takeji.
        “Haka kika ce ko? Ba komai zan rama ne”.
    Dariya ta shige tanayi, babu jimawa ta fito ɗauke da apples data yayyanka a ƙaramin bowl. Ƙasa ta zauna dan taji daɗin miƙe ƙafa. Smart dake binta da kallo ya ce, “Badai wannan ne abincin ba?”.
        Muryarta a marairaice da shagwaɓa ta ce, “ALLAH bakina babu daɗi, ina son naci kozai washe. Sannan wannan ɗin ma ni kam ya isheni”.
     Idanu kawai ya tsira mata yana kallonta. Ta ɗan hararesa da faɗin, “Kallon fa?”. Murmushi yayi da janye idanun nasa cikin yin luuu da su. Sai kuma ya sake zuba mata su cikin yanayin kasala. “Yarinyar nan anya kuwa?”.
             “Anya kuwa mi?”.
        “A'a ni bance komai ba. Kawai dai dama sai nake ga kamar fa wannan karon ma kin amshe ne, kin san fa ni bana saɓa saiti a zahirin fili wasa da na ɓoye”.
     Da farko bata fahimci mi yake nufi ba. Sai da tai ɗan shiru sai kuma ta dago ta hararesa. Dariya ya ƙyalƙyale da shi, zai sake magana ta tura masa Apple ɗin data tsiro a bakin tana sake harararsa. “Kai dai ALLAH ya shiryeka wlhy”.
         Murmushinsa ya cigaba da yi shi dai, koda ya shanye apple ɗin data saka masan sai ya sake matsowa da buɗe baki wai ta ƙara masa. Kafaɗa ta maƙe alamar anƙi ɗin. Ya bata fuska cikin yanayin shagwaɓa. “Kina sha, kina bama AA ni kuma sai a wareni. ALLAH sarki nima da Ammah na kusa da banga haka ba. Bari na kirata na faɗa mata”.
      Da sauri ta fisge wayar ta tura ƙasan ƙafafunta. Sannan ta tsiro apple ɗin ta tura masa abaki tana harararsa. “Mai kwaɗayi, kai yanzu in an barka saika faɗa?”.
         “Sosai kuwa. Harma da Daddy da Abba duk zan kira, ince tunda kika zo baƙya kula da ni.”
     “Sharri Master kenan. Daka kasheni dan ina jin kunyar Abba sosai ALLAH.”
     “Ni kuma baƙya jin kunyata ko?”.
Murmushi tayi tana sakama AA da ke tsaye jikinta yana wasa da gashinta apple ɗin a baki. Cikin basar da zancensa ta ce, “Da kai Daddy ya haɗa baki kuka kawoni nan ko?”.
            Kwance ya kai yana ɗora kansa a saman cinyarta, sai da yay ƴar dariya da tsokano AA ya ce, “Nikam babu ruwana. Daddy ne yay miki wayonsu na manya saboda yana jin tausayina. Shekaranjiya dai muna magana da shi yake cemin akwai saƙo da zai aiko min da shi, idan kuma ya samu shigowa London to, dan zaije Manchester city ne”.
     “Lallai ma Daddy nice saƙon yake nufi ko mi! Sai kace wata kayan wanki”.
   Dariya sosai Smart ke ƙyalƙyalawa har AA na faɗawa jikinsa shima yana tayashi. Sai kawai Lulu ta zuba musu ido tana kallo. Sai da sukai mai isarsu ya jiyo yana kallonta. Ganin yanda ta zuba musu ido ya ɗan ɗage gira da faɗin, “Kallon fa Madam”.
            “To ba dole na kalleku ba naga kun zare. Wai nikam dama kana dariya har haka? Amma da kaita tsuke fuska kamar wanda akaima saƙon mutuwa!”.
     Kansa kawai ya shafa yana murmushi baice mata komai ba. Itama sai ta share ta cigaba da shan Apple ɗin ta. Lokacin-lokaci tana saka masa a baki shi da AA da ke saman jikinsa yana wasa da ƙasumbarsa.......✍️

_🚴Ya kamata mu taya Ummah da Addu'a 🥱🥱🥱_

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣3️⃣
Chapter 57 · 0% Book details