← Book details Furar Danko Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 90

Sashe 70

Furar Danko Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

........ “Gaskiya Umma kin cucemu, haka kawai kin saka mutane zuwa wannan azababben wajen”. Babu dai wanda ya tanka masa a cikinsu. Wani yabiɗaɗɗen tsoho suka samu a saman dutsen jikin bukkarsa. Surutai yake tayi kamar wani zararre, yana ganinsu ya kwashe da dariya. Turus sukai duk suna kallonsa, sai ƙanwar Hajiya Naqiba da tasan haka yake ne ta zube tana masa kirarin da suke masa. Hakan ya sashi yin shiru yana saurarenta, sai da ta kammala ya sake kwashewa da dariya yana ma kansa kirari shima. Sai kuma ya tsuke fuska yana kallon su Abba kamar bashi yay dariyar ba, “To asararru, ku bazaku zube ku kwashi gaisuwar bane wajen waliyyin ALLAH?”.
       “Waliyyin shaiɗan dai. Ubanka ne zai gaisheka matsiyaci haihuwar asara” Salim da hanunsa ke masa azaba ya faɗa a fusace. Kaɗan ya rage Kawu Idi yay dariya ya dai daure. Kawu Jibirin ne ya ɗan girgiza kansa da fuskantar boka na kan dutse. Babu wasa a tattare da shi ya ce, “Muba neman wani abu mukazo wajenka ba. Hasalima baka da wata daraja a idanunmu face kasancewa a gafalalle abin ƙyama”. Ya zaro wayarsa yana nuna masa hoton Ummah, wannan matar tazo wajenka kayi mata aiki akan wasu mata da miji, tare da tabbatar mata asirin idan baici ɗaya a cikin ma'auratan ba zai iya komawa kanta anyi haka?”.
      Dariya nakan tufu ya kwashe da shi harda ƙyakykyewa. Sai da yay mai isarsa kafin ya tsagaita da faɗin, “Shegiyar kaya ai wannan tasan takan mugunta. Dan koni uban gayyar da kaɗan na ɗarata. Sai dai a yanzu haka tana can cikin bala'i hhhhh. Dama mun faɗa mata ƙaiƙayi zai koma kan masheƙiya bata yarda ba hhhhh. Asirin bai kama mijin ba matar kawai ya kama, itama kuma ya saketa hhhh. Dan haka ya dawo kanta kuma bazata taɓa warkewa ba hegiya ta shiga kamun ɗan ƙallau.”
      “Kaima yau zaka shiga kamun ALLAH ai matsiyaci. Ka tsufa har an yayyafa maka gishirin mutuwa a saman kai amma baka san Annabi ya faku ba” Salim ya faɗa yana ɗaukesa da mari. Kafin kace mi ya rufesa da duka. Da ƙyar su Kawu Idi suka riƙesa, zafin dutsen dana ranar yasa suka yayibosa zuwa ƙasa bayan Kawu Idi da Salim sun ɗaureshi. Abba dai ko sau ɗaya baice tak ba. Haka suka jefashi a mota duk da warin jikinsa ma ya ishesu suka ɗauki hanyar Kano. Da yamma liss suka iso, sun sami gida jigum-jigum baka jin komai sai nishin Ummah. Ganin boka na saman tudu ya firgita mutane da yawa. Duk da shi a cewarsa ba boka bane malami ne, dan hatta shigarsa dai ta malam ce sai dai dauɗa da warin rana ba'a magana. Ga Salim ya tunɓuke rawanin tun a can sai ƙwalelen kansa da yasha ƙwal a kwabo.....

__________★

   A bisa umarnin Lulu Ummita ta shiga binciken gidan su Nadiya ta hanyar yaranta na shagon saloon da yanzu ƙanwarta ke riƙe da shi. Da farko yaran nata sunji tsoro sunƙi faɗa saboda gargaɗin da akai musu. Sai da Ummita ta dinga musu magiya sannan suka faɗa mata gaskiyar a inda Nadiya take yanzu haka. Acan cikin wata tsohuwar makaranta ce da rufunta ya kwaye a ruwan bana. Hankalin Ummita ya tashi matuƙa da ganin Nadiya duk da bata santa ba kafin yanzu, sai hotonta data gani a wajen Lulu. Tayi baƙi ta lalace sai uban ciki haihuwa yau ko gobe. Wasu ƴan shaye-shaye dake zama wajen ke bata abinci da kayan shaye-shayen. Hankali tashe Ummita ta kira Lulu a video call. Da farko Lulu cewa tai bata yarda Nadia bace, sai da ta fashe mata da kuka cikin ƙarfin hali ta rantse mata cewa itace. Gaba ɗaya sai Lulu ta sake birkicewa da tashi hankali, itama ta fashe da kuka. Da ƙyar ta iya cewa Ummita sukai Nadia asibiti, amma ta kira Uncle Yousuf a waya. Koda Ummita tai kiran Uncle Yousuf ta sanar masa babu ɓata lokaci ya iso wajen shi da ƴan sanda da ambulance. An ɗauki Nadiya zuwa SHIRA'S HOSPITAL. Babu ɓata lokaci likitoci suka rufu a kanta, kamar jira cikin nata keyi dama sai naƙuda ta tashi. Doctors sun tabbatar bazata iya haihuwa da kanta ba, dole akai mata cs. Ana shiga da ita ɗakin theatre Uncle Yousuf ya nema gidan iyayenta. Sai dai koda yaje babu wanda ya sauraresa duk da ya sanar musu tana can a asibiti an shiga da ita theatre basu saurarensa ba. Haka ya baro gidan ransa a ɓace, sai bayan tahowarsa ƙanwarta ta biyosa asibitin a sace bisa umarnin mahaifiyarsu......

(ALLAH sarki Uwa kenan😭🙏).

        *_★UK★_*

       Fuskarsa ɗauke da murmushin zancen Iya Tabawa ya tura ƙofar bedroom ɗin a hankali ya shiga bakinsa ɗauke da sallama, zuciyarsa cike da ɗokin san ganin sahibar ruhin nasa.. Cak kalaman bakinsa suka tsaya sakamakon tozali da ita zaune fuska share-share da hawaye ta zubama waya idanu...
      “Mawaddatan-warahmah!”.
  Ya kirayi sunanta cikin wani irin salon taushin murya mai amo da ratsa zuciyar mai saurare. A bazata ta ji saukar muryar tasa duk da a tsumayen isowar tasa suke. Dan hatta kwalliyar da taci yau a cikin skert da riga na atamfa da sukai mata ƙyau tayine da shi. Harda kwalliyar da hawayen tausayin Nadiya suka gama batawa. A hankali ta ɗago idanunta da suka kaɗa harda ɗan kumburowa. Sai ya samu kansa da lumshe nasa da sake buɗe su a kanta ya ware mata hannayensa alamar tazo garesa. Babu musu ta taso da ɗan gudu-gudu ta shige jikin nasa ya maida hannayensa ya naɗe a nata jikin. Wani kukan da ya sakashi runtse idanu da ƙarfi ta sake saki tare da ƙara ƙanƙamesa. Komai baice mata ba, bai kuma hanata tayi kukan ba har tsawon mintina biyu. Sai da ya tabbatar tayi ya wadaceta sannan ya ɗagata cak zuwa saman gado. Kwantar da ita yayi tare da kishingiɗa a gefenta ya tokare hannunsa da tallafo kansa ta yanda zai iya mata runfa. Ɗayan hannun kuma ya tallafo fuskarta ya zuba mata ido. Itama kallonsa take tana jan ajiyar zuciya. Karo na farko ya sakar mata murmushi mai sanyi da saka babban yatsansa ya ɗauke mata hawayen.
       “Waya taɓa Final Choice ɗin Aliyu Mawashi? Maman Aliyu Mawashi? Kin san kuwa yanda nake jin ƙunar zuciya a duk sanda naga hawaye na sauka akan ƙyaƙyƙyawar fuskar nan taki. A gaɓa ɗaya kawai nake son naga waɗan nan hawayen da rakinki, amma ba'a banza haka ba okay”.
      Hawayen ne suka sake ciko mata idanu, a hankali ya shiga girgiza mata kansa alamar kar tayi. Haɗiyesu ta shiga ƙoƙarin yi, sai kuma ta juya ta sake rungumeshi. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali tare da ɗago fuskarta ya manna mata kiss a goshinta da hancinta ya sakko saman lips ɗinta. “In sha?”. Ya faɗa cikin raɗa yana nuna mata lips ɗinta da yatsa. Murmushi ta sakar masa a karo na farko da hawaye. Shima sai ya murmusa da kai nasa lips ɗin saman nata. A hankali suka lumshe idanu a tare kowanne na sauke ajiyar zuciya, daga haka tsarin ya canja zuwa wani fage daban...
Chapter 70 · 0% Book details