← Book details Furar Danko Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 90

Sashe 64

Furar Danko Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

       Duk hayaniyar da akeyi Umma na jiyosu da ga falonta, sai dai furucin Abba yasa a yanzu bata iya fitowa ko tsakar gida, dan ya tabbatar mata idan ta sake fitowa ta firgita masa iyali batare da shi yace ba a bakin aurenta. Wannan kalma na ɗimautata a duk sanda ta sake maimaita kanta a ƙwaƙwalwarta. A cikin abinda bai wuce sati guda ba duk tayi wata irin firingau-firingau da ita. Tai muguwar rama kamar mai cutar sida. Kuka kam idanu sun daina sai dai na zuciya. Tunda take ko'a labari bata taɓa sanin akwai makamancin irin tashin hankalin nan nata a duniya ba. Ita a yanzu ma neman hanyar zuwa ga malamin da yay aikin take ya karya shi amma babu hali, tsakar gida ma ya gagari mutum balle ƙofar gida har akai ga shiga mota. Abincin tana cinsa ne kawai dan tsoron mutuwa. Amma badan yunwa ba. A duk sanda ta jiyo muryar Ammah dai ta fashe da kukan baƙin ciki na tsananin jin kishi. Tana jin raɗaɗin tayaya za'ai ace Ammah taci nasara a kanta kenan? Itace fa Yahanasu mai yawan ƴaƴa maza a gidan fiye da kowa, ƴar uwar mai gidan jininsa, tafi kowa yawan ƴaƴa, ita ta fara haihuwa a gidan, tanada power ɗin juya miji a tafin hannunta koda daga baya zai suɓuce mata zata sake nemo hanyar riƙosa. Kowa a waje gani yake itace ke juya gida da miji, amma a kullum sai Hafsatu ta zama sanadin rusa mata plans nata. A kowace safiya tana ji kamar ta kashe matar nan ko zata ji sassauci na zafin tsanar da take mata. Kuka irin mai ƙona zuciya ɗin nan ya suɓuce mata, sai dai babu ɗigon hawaye a cikin idanun sai zafin zuciya da gwara ma kaita hawayen........✍️

_🥱🥱Jiya kunji shiru ko. Ina nan na dage muku da typing ne nima na ƙagara mu gama🚴🚴._

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣7️⃣

.......A gidan Alhaji Garko kam ALLAH ya sauki amarya lafiya, ta silloɓo ƴan biyunta duk maza har guda biyu masu kama da Baba Garko da ƴan uwansu. Farin ciki a wajen Baba Garko da ma'aikatan gidansa ba'a magana. Babu ko ɗar balle jin kunya ya ɗaga waya yay kiran Dada a farko. Rabon da ya kirata a waya harta manta a rayuwarta, duk da halin da take ciki jikinta har rawa yake wajen ɗauka. Dan addu'a take a ranta ALLAH yasa baƙar dagar ce ta mutu ita da cikin. Sai dai me tana kaiwa kunne kalma ta farko da ga bakin mijin nata, abin sonta da sukai ƙuruciya ga su a tsufa tare itace, “Alhamdullahi ALLAH ya sake azurtani da yara biyu MAZA masu kama da ni kamar sauran ƴan uwansu. Sai ki shirya kayan tarbar sabbin ƴaƴa Hajarah”. Da ga haka ya yanke kiran kamar dama da gayya yayi, hakan yay dai-dai da tsayawar numfashin Dada da tunda ya fara maganar yake fita dama a fisge. Yaraf ta sulale a wajen ta zube babu numfashi.....

(🥱DADA team sai ku kai ɗauki🚴).
       _________★

    Kamar kullum pharmacy ɗin cikin hada-hada da kai-kawon mutane yake. Dan babban pharmacy ne da duk kalar maganin da kake nema ko kayan anfani da ya shafi lafiya zaka sameshi. Ga shi akan babban titin da mutane ke yawaita kai-kawo sosai kuma. Ba sayen ɗai-ɗai kawai suke ba har sari suna badawa wa ƙananun camix ma. Banda ɓoyayyun masu amsar miyagun kayansu da ko yaran shagon ba kowa yasan ana harƙallar ba sai amintattun ciki da masu lura, sai dai kosun luran babu damar magana dan anfi ƙarfinsu.
          Duk da safiyace akwai mutane sosai musamman masu sari. Basu wani damu da jin dirar motocin ƴan sanda ba a ƙofar pharmacy ɗin kowa ya cigaba da abinda yake yi. Sai dai me motocin ƴan sandan na gama dira ta NDLEA suka dira suma har mota uku. Sai a lokacin hankalin mutane ya fara dawowa jikinsu, sai dai kafin yin wani yunƙuri jami'an gaba ɗaya sun rufe ƙofar pharmacy ɗin. Sauran kuma sun afka ciki. Gaba ɗaya mutanen ciki an tattaresu zuwa mota, hakama ma'aikatan an tisa ƙeyarsu cikin store ɗin wajen wasu kuma cikin pharmacy ɗin. Duk tambayar da suke akan su mi sukayi babu wanda ya basu amsa. Jikin Manager ɗin wajen har rawa yake wajen ƙoƙarin kiran layin oga kwata-kwata ya sanar masa.
     Duk da hankali Alhaji Sadi Dikko Baduku ya tashi da jin wai NDLEA a pharmacy ɗin nasa sai cikin rashin damuwa da gadarar masu arziƙi ya buƙaci yaron nashi ya bama ogansu waya. Cikin jin ƙwarin gwiwa Manager ya nufi wanda yake ƙyautata zaton ogan nasu ne ya kai masa wayar. Kallon sama da ƙasa mutumin yay masa tare da daka masa tsawar da sai da ya zabura. Ba Manager ba hatta shi kansa Alhaji Sadi Dikkon sai da ya zabura. Mamaki da al'ajabin wane ɗan iska ne wannan ya sashi yanke kiran, da sauri ya shiga neman shugaban hukumar NDLEA na Kano baki ɗaya, sai dai har wayar ta gama ring ba'a ɗauka ba. Sake kira yay aka danna masa busy alamar an yankesa. Anan ne fa hankalinsa ya fara tashi, da sauri ya shiga neman number Hon. Nakowa.....

         *_UK_*
Chapter 64 · 0% Book details