← Book details Furar Danko Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 90

Sashe 61

Furar Danko Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

.......Da kallo kawai ta bishi zuciyarta na wani irin rawa da mamakinsa. Gaba ɗaya ya juye mata a kammanin da ta sanshi tun farko na dakewa da rashin son ɗaukar raini. Gaba ɗaya sai taji ma shakkarsa ta shigeta. Kusan minti uku tunaninta ya fara zurfi sai kuma ta miƙe, dan ganin ɓacin rai a tare da shi kuma duk sai take jin itama nata zuciyar babu daɗi. Bedroom ɗin ta shiga da sallama ƙasa-ƙasa, inda yake tsaye yana saka bathrobe a jikinsa ta nufa, dan har ya cire kayansa. Sallamar kawai ya amsa mata batare da ko kallonta yayi ba harta iso gabansa. Fuskarsa da ke kicin-kicin ta zubama ido, ganin bazai kalletan ba yasata kai yatsanta manuniya ta ɗan takaleshi a kafaɗa. Kautar da jikinsa yay, ta ƙara lakatoshi a hannu, ya sake kaucewa kamar wani ƙaramin yaro, sai kawai ta matsa ta rungumeshi ta baya ta ɗora kanta a saman bayansa tare da zagayo hannayenta saman cikinsa tana wasa da igiyar bathrobe ɗin kamar zata kwance. Idanunsa da ya lumshe saboda jinta a jikinsa ya ɗan ƙanƙame jin ta zagayo hannunta saman cikinsa, a hankali ya firzar da iska yana cije lip ɗin sa na ƙasa kaɗan da ƙoƙarin yana ƙoƙarin zame hannun nata amma sai ta sake ƙanƙamesa.
       “Fushi kayi?”.
    Ta faɗa a hankali. Shiru kamar bazai ce komai ba, sai kuma ya ɗan sake sauke numfashi da kama hannun nata ya zagayo da ita gabanshi. Mayatattun idanunsa ya zuba mata kamar yanda itama take kallonsa cikin tsakkiyar ido. Gira ta ɗan ɗaga masa tare da kanta, “Fushin dai?” ta faɗa tana kai yatsarta ƙirjinsa a saitin zuciyarsa ta shiga zagayawa da faɗin, “To ki huce hajiya zuciya”.
Harararta yay da buge mata hannu yana sake ɓata fuska kamar wani AA. Sai kawai ta ƙyalƙyale da dariya da faɗawa jikinsa ta sake rungumesa.
         “ALLAH in kana shagwaɓa kamar AA najin yunwa fa”.
    Duk yanda yaso cigaba da riƙe kansa ya kasa. Murshi yayi yana ɗan lumshe ido da dungure mata kai, sai dai baice komai ba. Dan haka ta fara masa cakulkule. Dole ya fara dariya da ƙoƙarin janye jikinsa amma taƙi barinsa, sai ma baya yake tana binsa har suka faɗa saman sofar ɗakin. Bata daina ba duk rokon da yake mata sai da ta tabbatar ya jigata sannan ta barshi tare da faɗawa kansa suna dariya su duka.
        “ALLAH ke muguwa ce”.
    Ya faɗa yana ja mata hanci. Amsa ta bashi da “Ai kai ka koya min dan kaine malamin koya mugunta ma”. itama tana dungure masa kai. Sai suka sake ƙyalkyalewa da dariya.
            “Kin fara nauyi ALLAH, ɗaga ni karki fasa min ciki”.
         Fuska ta ɓata da duban kanta, sai kuma ta hararesa da faɗin, “Ta ina na ƙara ɗin? Ni ALLAH bana son sharri”. Kallo ya bita da shi irin a ɗan ɗagen nan, sai kuma ya nuna mata yana gimtse dariya. Inda ya nuna ɗin ta kalla. Da sauri tace “ALLAH zai saka min” tana kai masa duka da filo. Ƙoƙarin riƙewa yake tana dariya da faɗin, “Daga faɗar gaskiya. To shikenan na yarda baki ƙaraba. Ƴar ƙanwata na nan yanda take ƴar sawalwala abinta cas-cas”. Sauka tai da ga jikin nasa ciki nuna irin nayi fushinnan, shima sai ya miƙe da sauri ya riƙota tare da ɗagata gaba ɗayanta suka fice a ɗakin. Tana zille-zille da faɗin ya sauketa bai kulata ba ya fita ta baya inda swimming pool ɗinsu yake. Direta yay a bakin ruwan ya cire bathrobe ɗin jikinsa yay hanging a kan ɗan ƙarfen da aka saka domin hakan kawai dama. Da sauri ta kauda idanunta da ga kallonsa, dan har yanzu ta kasa iya daina jin kunyarsa, duk da bawai haka nan yake ba akwai ƙaramin boxer jikinsa bazata iya jurar kallon nasa ba kai tsaye a haka. Shima komai baice mata ba sai murmushi da ya saki kawai, cike da kwarewa yay tsalle da sufa irin na masu wasa da ruwa cikin ruwan. Yanda ya fantsama ciki sai da ruwan ya tarwatso mata a jiki har a fuska. Fuskar ta kwaɓe tana kallonsa kamar zatai kuka, shi baima san tana yi ba sai da ya kai ƙarshe zai juyo ya kula. Dariyar mugunta ya kwashe da shi, sai kuma yay ƙasa cike da kwarewa ya sake dawowa gabanta ya miƙe tsaye yana dariyar da ɗibar ruwan a hannu ya sake watsa mata a fuskar. Lulu ba haƙuri idan akai saita rama. Hannu takai itama zata ɗibo danta rama ya fisgota ta faɗo ciki. Kokawa suka fara a ruwan yana kunnata da dariya, sai kuma yay mata gwalo yay ƙasa cikin ruwan. Itama da sauri ta nutse ciki ta bisa saikace wasu kifaye...
      Sun jima a cikin ruwan suna nishaɗin su kafin suka fito saboda tunawa da AA shi kaɗai a ɗaki. Bathrobe ɗin da yazo da ita ta saka, sannan taje ta ɗakko masa wata shima. Tun shigarta ɗakko masa rigar ta samu AA ya tashi, dan haka bata zauna jiransa ba ta juya ciki. A ɗakin ya sameta tana cirema AA kaya, yana ganin shi ya shiga miƙa masa hannu dan yanzu ya daina masa ƙiwa. Shima cikin farin ciki ya ɗauki abunsa yana mai sumbatarsa da faɗin, “Oh oh Baban Ammah ya tashi kowa ya ɓoye kayansa kafin a cika musu aiki”.
Cikin dariya Lulu tace, “Aikam dai, dan yanzu zai fara haɗa gwaramar tasa”.
“Ai ke ya gado, dan Uncle Yousuf ya cemin kema kina ƙarama hummm”.
A shagwaɓe ta ce, “Shi Uncle You ɗin ya faɗa, ni dai ALLAH babu ruwana salaha da ni, sai dai kai dan dama Ammah tace tasha rashin jin ka”.
Shima fuskar ya ɓata da faɗin, “Sharri ba haushi zanji ba ai” daga haka ya nufi bedroom da AA a kafaɗa domin yimasa wanka. Dan yanzu in har yana gida kusan komai shikema yaron, acewarsa yana koyane koda ta haifo ƴan uku basai sunje neman Nanny ba. Takan hararesa kawai idan yace hakan.....
Chapter 61 · 0% Book details