← Book details Furar Danko Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 90

Sashe 44

Furar Danko Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sosai Smart ke jin farin ciki a ransa mara misali dan harda hawayen farin ciki ganin yanda waɗan nan ɗunbin al'umma suka amshesa da taruwa domin shi. Bakajin komai sai ambaton sunansa a wajen, _Smart Mawashi, Smart Mawashi_ dai. Yanda ma suke ambaton Mawashi ɗin abin dariya. Abinda ya ƙara tabbatarwa da mutane Smart Mawashi ya amsu yanda a yinin ranar kawai an saida copy na rigar JC mai ɗauke da sunansa kawai ta kai kimanin dubu hamsin. Wannan al'amari ya matuƙar ɗaukar hankalin mutane da gidajen jaridu. Yayinda masu fashin baƙi akan harkar ƙwallon ƙafan keta nasu aiki. Gida Nigeria musamman arewaci kuma garin Kano sun shiga matuƙar alfahari da ganin ɗan su yau a wani mataki na rayuwa da sai ɗan baiwa mai Sa'a kawai ne ke takawa. Hatta da social media babu abinda ke kai kawo sai hotunan Smart Mawashi da tarihin rayuwarsa. Hatta da hotunan bikinsa ranar sai da suka dawo sabbi a yawon media. Sai a lokacin ne Lulu tasan wainar da ake toyawa. Ita kasa ma fassara al'amarin tayi sam. Cikin sauri ta shiga bincike-bincike a media. Sai ko gashi ta ga duk abinda take buƙatar. Tsabar yanda al'amarin ya dakar mata zuciya bata iya furta komai ba. Dan datace ma zata tsananta tunani ko maganar Smart ɗin matsanancin ciwon kai da tsanarsa da take ji ke dawo mata sabuwa. Dan ma Alhmdllh zuwa yanzu akwai ɗan sassauci a a al'amarin kasancewar addu'a da aka duƙufa yi babu dare babu rana. Yau ɗin ma dai ta yini da ciwon kan, dan har dare tana kwance tana fama har sai da Daddy ya shigo yay mata addu'oi....

Bayan Smart ya fito da ga stadium hirarsa da ƴan jarida ta zama abu na biyu da ya sake zama babban topic a kansa a wannan yini. Ya bada tarihin rayuwarsa da yay matuƙar taɓa zukatan mutane harda masu hawaye, dan ma ya ɓoye kaso tara cikin goma ya bayyana abinda yake da buƙatar duniya ta sani ne kawai. Ya bayyana irin yanda ya tashi da son ƙwallo a zuciyarsa da taimakon da Abdull-Hameed Coach yay masa a rayuwa da matsalolin da ya samu da ga baya. An masa tambaya akan dalilinsa na zaɓar team ɗin Arsenal duk da sauran clubs biyu da suka riƙe wuta a zawarcinsa sun sake ƙara kuɗi amma yace Arsenal ɗin dai. Sai yay murmushi da faɗin “Arsenal club ne da tun yana yaro yake matuƙar so, sannan club ne mai ɗunbin tarihi da kuma ya ajiye tarihi da tarin masoya a duniya, sannan club ne one of the best in the world. Sannan yana da ƴan wasan da yake matuƙar so da kallo a matsayin madubinsa a cikin club ɗin irinsu Terry Herry. Patrick Vieira da sauransu.......”✍️

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣4️⃣

........A ɓangaren Ummah tana shiga ɗakinta ta sake tsagewa da kuka, a haka ta hau neman layin Hajiya Naqiba.
      “Na shiga Uku Aminiya Abban Salim ne ya mutu?”. Cewar Hajiya Naqiba a rikice jin Umma na ɓarza kuka.
    “Ba garama mutuwar ba zan haƙura dole Aminiya. Ashe malamin nan yaudarata yake shima duk irin maƙudan kuɗin dana zube masa. Gonata ta gado fa na ɗaga na sayar na bashi kuɗin aikin nan amma ace wai duk a banza nayi, yau sai ga shegen yaron nan mai taurin ran tsiya a tsakkiya Turawa kamar zasu cinyesa dan soyayya. Wai wani ƙungiya na kwallo asinal yake ko uwarmi ne ma oho musu suka sayeshi da wani uban kuɗi da har yanzu ma zuciyata da ƙwaƙwalwa ta sun kasa haɗawa dai-dai, wai zai musu ƙwallo na shekara biyar. Shike nan na mutu Aminiya, duk wahalar da nake akan yaron nan dai abanza take cigaba da tafiya”.
        “Tofa babbar magana, wai shi Hydar ɗin ne yakai wannan matakin na shiga ƙungiyar Arsenal? Shin ko shine ma ɗazun Maheer ke ban labari cikin zumuɗi wai wani matashi Smart ɗan Kano ya zama babban gwaska a duniya, yanzu hakama yana nan gidan Alhaji Sammani wai suna kallo ko ana nunashi”.
              “Matsiyaci haihuwar asara shine. ALLAH ya tsinewa uwarsa ma bashi ba. Na tsani matar nan fiye da yanda na tsani mutuwata, duk irin wahala da kai-kawon da nake a kanta da faɗi tashi kullum abbanza suke tafiya. Narasa wace irin baƙar tambaya ke ga Hafsatu”
      “Humm Aminiya kar kice haka, kin manta nasarar da kikaci ta tsahon shekaru yaron nan ko filin ball bai iya shiga, ga tsanar da Abban Salim yay masa. Sannan a yanzu haka fa akwai asirin dake jikinsa wanda ya gagara zama da matarsa waje ɗaya....”
           “Na fara ji a raina asirin nan bai kama shegen yaron nan ba, matar tasa kawai ya kama dai kamar, kuma mayen yaƙi sakinta. Malam yana ɓoye mana ne kawai”.
     “Tunda dai har ya kama matar tasa ai ya wadatar damu. Ki kwantar da hankalinki dan ALLAH yanzu ma bamu makara ba. Wajen Na-zuru zamu koma tunda dama shine yay masa wancan ƙullin goron na farko, irinsa zai sake mana ko ya shiga filin ya yanke jiki ya faɗi basai muga ta ƙafafa ba. Sannan kisa ranki a inuwa, wannan maƙudan kuɗi da kikaji ba nashi bane ba, haka naji Maheer nacewa da nake masa faɗan shi miyyasa bazai zo ya koya ƙwallon ba.”
        “Kai dan ALLAH wai da gaske kike? To kudin na waye?”.
    “Ni ban sani musu ba, kamar dai yace wai ko kungiyar daya bari ne ai da kuɗin, shi za'a yanka masa nasa albashinne.”
               “Kai amma har na ɗan jin sanyi, shegiyar uwarsa sai muga ta hura hanci, ashema kuɗin na wasu ne shasha ɗan ya koma bawan turawa bata farga ba”.
     Dariya suka kwashe da shi kamar suna kusa da juma....

     Niko na ce, “Hummm!”.

  ★Sosai abinda Umma tayi ya tsayama Abba a rai, har ya shiga dogon nazari akanta. Sai dai baicema kowa komai akan hakan ba. Itama baice matan ba. Ya dai ɗauki ɗammarar saka ido a lamarinta domin tabbatar da abinda ransa ke raya masa...

           ★Ammah kam ko'a jikinta, dan ita zuwa yanzu lamarin Ummah bai wani damunta sosai. Face dagewar da tai da addu'a ita da zuri'arta domin kariya da ga sharrinta. Dan duk yanda Gwaggo Sa'adah taso ɗaukar mataki ta hanata, acewarta su jira sakamako na zuwa akan kowa.....

         *_6 MONTH'S LATER_*        

     Abubuwa da yawa sun faru masu tafiya da nasarori da kalubale a cikin waɗan nan watanni da suka kasance kusan tara da haihuwar Lulu. Ƙalubalenta na farko mai kuma girman gaske shine shiga tsakaninta da mijinta uban ɗanta da akai ta hanyar sammu mai ƙarfi. Nasararta ta farko komawa islamiyya neman ilimin addini tuƙuru tare da maida hankali matuƙa duk da ta koma bakin aikinta. Sai wannan gaɓar ta kuma samu nasarar kafa ƙungiyar da take buri data samu tallafin ƙarfafa gwiwa da ga iyayenta da kakanta har ma da ƴan uwan haihuwar makaifiyarta. Nasara ta uku kafa business ɗinta data jima tana buri na turare, tana kawosu daga ƙasashe daban-daban, ana kiran ƙaton shagonta da suna *_LULU's ƘAMSHI_*. Nasara ta huɗu ƙyaƙyƙyawan yaronta da kamaninsa ke ƙara fitowa dana mahaifinsa nata ƙara wayo gashi cikin ƙoshin lafiya da kuzarinsa. Alhamdullah kuma yana a cikin kariyar UBANGIJI shikam. Dan duk da irin hare-haren da su Umma suke kawo masa ALLAH ya kiyaye abinsa yaron nan ko gezau. A yanzu haka ya fara miƙewa ya ɗan dafa kujera alamar dai yana son taka ƙafa. Ana kaisa wajen Ammah ya yini abinsa, kasancewar yana shan koko kuma gashi baida damuwa akwai haƙuri yasa sai ya yini lafiya sannan a maidosa. Itama su Asma'u kanzo su yinin mata anan. Su aunty Bilkisu kansu kan zo suga AA da gasiheta lokaci-lokaci. Itama kuma tana zuwa gidajensu har ta yini. Can gidan ne dai bata iya zuwa. Dan kota gwada hakan baya yiwuwa. Wannan abu na cimata rai dan tana so da ƙaunar Ammah a ranta. Wannan soyayyar da ga ALLAH ce. Shiyyasa itama Ammahn kan leƙosu lokaci-lokaci musamman idan ance AA na mura haka ta haƙora. Sosai shaƙuwa ta shiga tsakaninta da dangin Smart. Dan hatta samarin su Mubarak sukan zo gareta a ɓoye batare da sanin iyayensu mata ba. Duk watan duniya kuɗi kan shigo account ɗinta da ga Aliyu, sannan akan kirata da number ƙasar England. Sai dai kota ɗaga ba'a magana, sai ita zata dinga hello-hello da ga ƙarshe a yanke kiran. Takan ji haushi tace bazata sake ɗagawa ba. Amma da an kira bata iya haƙuri sai ta ɗaga ɗin...
Chapter 44 · 0% Book details