← Book details Furar Danko Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 90

Sashe 45

Furar Danko Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

      ★A gidan su Smart kam nasarori da ƙalibalen suma dai basu tsallake su ba. Sai dai Alhmdllh a ɓangaren Ammah babu abinda zata cema UBANGIJI sai godiya. An tsaida Ranar auren Maryam da Ahmad. Yayinda ɗaukakar da ALLAH ya bama Smart ta sake fiddota a cikin ƴan uwa dama jama'ar gidan har da dangin Abbah. Smart ya dakatar da Abbah fita kasuwa duk watan duniya ya yanka masa albashi shi da Ammah a cikin albashinsa da ake biyasan duk sati-sati. Sannan Ahmad zai kawo kayan abinci bisa Umarnin sa. 
        Wannan abu na ƙara ɗaga hankalin Umma har ma da Mama. Sai dai banbancinsu ita mama kan balbale nata yaran da faɗa ne akan suma su san ciwon kansu su dinga ma mahaifinsu in ba hakaba smart zai ƙwace dukkan power ɗin su, sannan ita bata bin malamai, kishi ne dai irin na matan bahaushe da jin ƙyashin cigaban kishiya. Itakam Umma tsantsar hassada da baƙin ciki sunbi sun kanainaye mata zuciya da ruhi. Ta kasa zaune ta kasa tsaye. Duk ɗan abinda ta samu suna a yawon malamai da bokaye ita da Hajiya Naqiba aminiyarta. Aikin suke iya ƙarfinsu amma basu sake jin wani sabon abu ba bayan zaman Lulu gida. Ga malamin nata ya tabbatar mata akwai fa matsala idan aikin bai kama Smart ba shi. Dan su duka biyun akai musu ai akan su tsani juna. Wannan dalilin yasa take ta faman bibiyar al'amarin Smart dan taji shi ya wajensa yaya akan matar tasa amma ta kasa samun kowacce irin mafita. Ga lamarin Huwaila na caja mata kai. Dan ta girmi Maryam amma har yanzu babu tsayayye, saka auren Maryam kansa ya hargitsa mata lissafinta. Balle da taji cewar itama mai hannu da maiƙo zata aura. Wayyo ina wuta ta saka Ammah ne. Ta rasa wane irin sirri keda Ammah ɗin da dukkan ƴaƴanta suke auren ƴaƴan masu kuɗi. Yanzu dai abu biyu ta saka a gaba. Wato tarwatsa rayuwar Smart da rusa auren Maryam. Duk ta fige ta lalace a tsaye saboda saka wa kai musiba. Itace kullum faɗa da ƴaƴa akan su bata kuɗi, musamman ma Salim dake nuna mata shi fa ya gaji da wahalarta, mitake da kuɗi wai kamar wata ƴar caca..
      Duk abinda take a yanzu idon Ammah ƙyam yake a kanta, dan haka ta dake dagewa da addu'oi da sadaka.. Tare da kiyaye duk wani abinda Umma zata basu koda abincin gidanne yanzu ranar girkin Umma sai suka daina ci, miya Ammah ke musu mai yawa tasa a freight, duk ranar da Umma tai girki sai tayi musu abinci a a ɗaki suci, na Ummar a fitar waje aba mutane cikin hikima.. A tunanin Ammah Abbah bai san mike faruwa bane, sai dai idonsa na akan komai yana dai biye yaga iya gudun ruwan kowannensu musamman ma Ummah..

        ________★

  A garko family kam abubuwane keta ƙara tsamari. Abu na farko shine Baba Garko dai tunda ya tsallake bayan kama Sulaiman bai sake dawowa ba, sai labarin a washe garin da Dada taje gidan su Lulu suke jin cewar an ɗaura masa aure matar ma ta bisa. Ranar sunga abinda ya girmesu a wajen Dada. Dan zaman ƴan bori tayi a gaban surukai ta saki ƙaƙƙarfan ihun da ya nema girgiza ginin gidan. Ba ita ba su kansu yaran hankalinsu ya tashi, a ganinsu mi mahaifin nasu zaiyi da wani aure a shekarunsa haka, kuma abin mamaki wai ma budurwa ya aura sa'ar ƴaƴan cikinsu. Matansu kam dai wannan al'amari yay musu daɗi, sai dai suna ƙoƙarin dannewa a gaban mazan nasu.. sai an koma gefe asha gulma da dariyar Dada..

        Sai da Baba Garko ya kwashe watanni kusan shida da amaryarsa suna yawan hutawa a ƙasashe sannan suka dawo Nigeria da cikinta da ya fito kowa na gani. Ƙyaƙyƙyawar mace ƴar gaye mai tarin ilimin addini dana boko. Sannan gata yarinya ƙarama, dan bazata wuce sa'ar Lulu ba ma. Da gani dai kasan kuɗi ta gani ta shige, duk da dai Baba Garko ba baya ba wajen ƙyau amma tsufa ai ya ƙwace komai sai godiyar ALLAH kawai. Wannan ciki ya saka ƴaƴansa jin matuƙar kunya, sai dai babu damar yin magana ya maka wankin babban bargo, dan shi ko'a jikinsa. Kuma yace dole su girmama masa mata. Suna son sake bashi haƙuri akan mahaifiyarsu suna jin tsoro, dole sukai gum da bakunansu.
      Washe gari Daddy da Uncle Yousuf sukaje gaishesa suma da masa murnar aure anan ne su dai suka fidda kunya da tsoron suka roƙesa akan yay haƙuri itama Dada ta dawo. Ai an mata gargaɗi. Shima Alh. Sulaiman ai masa afuwa dan ALLAH ya dawo cikin iyalinsa. Bai tanka musu ba dai, sai sakawa da yay Uncle Yousuf ya kira masa Smart a waya. Yako kira masa shi suka gaisa. Yana jin ƙaunar yaron matuƙa yanda yake bashi girma. Yay masa faɗa akan rashin kiransa su gaisa, tare da tayasa murnar cigaban rayuwa da ya samu. Yace shi ai bai sani ba sai kwanan da ya gansa ana hira da shi ya shiga mamakin kamannin har yay kiran Daddy shine fa yake tabbatar masa da shi ɗinne. Haƙuri Smart ya bashi cikin girmamawa da tabbatar masa zai gyara insha ALLAH. Cikin gamsuwa Baba Garko ya sake saka masa albarka. Sai kuma ya tambayesa yaushe ne zai zo ya ɗauki iyalinsa. Ɗan jimm Smart yay na wani ɗan lokaci, kafin ya firzar da numfashi yana jan ajiyar zuciya. Cikin tausasa harshe ya ce, “Baba yanzu ni lokacin nawa ne sai a hankali, dan gashi ana tsaka da fara buga wasan premier link ne. Sannan kuma itama bana son a takura mata har sai idan itace da kanta ta yarda zata nemeni nake ganin hakan zai fi zama masalaha, itama bazataga an takura mata ba kamar farko”. Murmushi irin na manya Baba yayi. Tare da cewa, “Shike nan shawaranka yayi sosai”. Daga haka suka ajiye wannan maganar Smart ya koma bashi hakuri shima akan maida Dada da sakin Alh. Sulaiman. Acewarsa shi ya yafe komai ya wuce a tari gaba........✍️

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣5️⃣

........Wannan roƙo nasu Smart da Daddy da Uncle Yousuf harma da Abba da shima yazo masa murnar ƙara aure akasha hira da barkwanci na tsoffin abokai bayan sati biyu Dada ta dawo. Dawowar data zame mata matsanancin jin zafi. Gashi ba abun tace bazata dawo ɗin ba ta rasa sauran damarta. Ga muzantatan da surukanta keyi na sake ɗaga mata hankali. Ta samu gida fa komai ya sauya. Hatta masu aiki kowa dai Aunty Amarya dai aunty amarya dai. Dan yarinya ta kwantar da kai tana cin garar arziƙi abinta. Ta kuma kame kowa na gidan da ƙyautatawa bayan uban gayyar Baba Garko da taima ram da zuciya yake jinsa kamar wani ɗan shekara talatin, dan more tsufansa yake hankali kwance ya manta da batun wata aba Dada... Ganin cikin amarya da Dada kejin wai-wai a bakin mutane ya sake ɗaga mata hankali ta ɓarke da kuka. Wai itace yau tsofai-tsofai da kishiya, kishiyar ma sa'ar jikokinta kai jama'a wane irin cin zarafine wannan Alhaji Sufi yay mata ne ita kam a duniya, duk wahalar da tai a ƙuruciya na hana wata shigowa gidanta sai a wannan gaɓar za'ace wai ga ɗan uba a cikin zuri'arta. Ga shi Baba Garko yaƙi ko saurarenta tunda ta dawo, duk ranar girkinta fa zai yi kamar suna tare amaryarsa bata zuwa inda yake, amma kuma bai barin itama Dadar tazo. Ko kuma ma ya ƙirƙiri tafiya. Bayan wata ɗaya da dawowar Dada yasa aka saki Alh. Sulaiman shima.....

     ______★

A ɓangaren uban gayya kam al'amura sai dai Alhmdllh. Dan komai yana tafiya fiye da yanda akai fatansa. Ya zama cikakken ɗan wasan Arsenal da yanzu duniya ke kallo ta faɗa da kiransa *_GWARZON ZAKI_* Sunan Smart Mawashi sake dilmiya yake a duniyar ƙwallon ƙafa. Dan a yanzu haka ya fara taka sabuwar rawa a sabon team ɗin nashi na Arsenal. Duk da kuwa wasanni uku kenan suka buga kacal. Sai dai aduka wasan babu wanda bai saka musu ƙwallo ba. Wannan ya sake jawo hankalin al'umma kansa tako ina a duniya. Ya zama ɗaya daga cikin matasan yara masu tashe a duniyar ƙwallon da ake faɗa ake ma kan faɗa a kowane yini. Al'amarin matarsa bawai baya damunsa bane, ya miƙama UBANGIJI al'amarinsa ne kawai da fatan cinye waɗan nan jarabawoyi kashi-kashi. Shi kaɗai yasan abubuwan da yake jurewa a irin wannan tsukun. Amma yana matuƙar begen matarsa a kusa da shi har ma da gudan jininsa takwaransa.....

        ____________★
Chapter 45 · 0% Book details