← Book details Furar Danko Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 90

Sashe 18

Furar Danko Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

     Dada ta iso ƙasar Canada kamar yanda taima Dr Olivia alƙawari, sai dai a ranar babu damar ganinta dan bata duty kamar yanda ta sanar mata. Kai tsaye gida ta nufa inda ta samu tarba a wajen Lulu ta musamman. Zuciyarta ta mata sanyi ganin yanda jikar tata ta saki jikinta a yau ba kamar yanda suka rabu ba. Sai dai duk motsin Lulun idonta na'a kan cikinta ne, amma batace komai ba dan Alh. Sulaiman yace mata kartace ma Lulun komai har sai ya iso. Tsaf Lulu na lure da ita amma ta basar sai ma tambayoyi data shiga jero mata akan yaya jikin Baba Garko. Dada ta amsa mata da cewar, “Ai jiki yayi sauƙi dan yanzu haka ma an sallamemu muna gida, har shi yana ma batun komawa Nigeria dan ya gaji da zaman turan”. Murmushi Lulu tayi cikin tsokana ta ce, “Dada kawai dai yana son ya gudu ne saboda tsoron kar sanyi ya ƙarasa rugurguza miki shi.” Ranƙwashi Dada ta sakai mata amma sai ta kauce da sauri tana dariya. Haka sukai hirarsu yau cikin nishaɗi har Tajuddeen ya iso. Anan ɗin ma Lulun ta basu mamaki dan bata tashi ba kamar yanda takeyi a duk sanda ya shigo gidan. Koda ya gaisheta ma sai ta amsa masa harda cewa “ykk?”. Duk da ataƙaice ta tambayi lafiyar tasa wani irin sanyi da shauƙi ne suka riskesa a lokaci guda. Ya saki wani irin lallausan murmushi da sauke ajiyar zuciya. Ƴar sakewar Lulun ya sashi kwana a gidan yau, washe gari sun wayi gari da zuwan Alh. Sulaiman tamkar a ƙasar ya kwana. Shima Lulu ta gaishesa sama-sama yana binta da wannan shegen kallon nasa ƙasa-ƙasa. Yayinda shima Tajuddeen ke ɗan binta da kallon mamaki musamman cikinta da yaga ya turo. Dukansu Lulu a hankalce take dasu, dan cikin ma ta saka rigar da zata bayyanashi ne garesu su gani da ƙyau saboda neman magana. Sai kuma wani salon yamutse-yamutse takeyi na ƙularwa ita a dole mai ciki (😂Lulu problems kenan🤣👏).

Abinda Lulun keyi ya matuƙar sosa zuciyar Alh. Sulaiman, dan kasancewarsa gogaggen mutum mai huɗɗa da jama'a a fannoni da dama ciki harda matan banza. Ya fahimci da wani manufa yarinyar ke nuna musu ciki su tabbatar yana nan. Ya cije lips ɗinsa a hankali tare da miƙewa yana kallon Dada. “Zan ɗan je na wani waje na dawo Dada. Kai Tajuddeen ka jirani dan zamuyi magana”.
       A tare suka amsa masa da adawo lafiya, yayinda Lulu da ke shan kunun nata na fama ta ɗan laɓe baki hankalinta a television kamar bata san mi suke ciki ba. Har ya fice bata tanka ba kuma, sai a zuciyarta take ayyana (Kuyi duk ku gama ƙulla makircin naku ina biye daku har a gaba danan dan inaji a jikina za'a samu canjin wajen zama in har akwai abinda kuke shirin)...
Alh. Sulaiman na fita asibiti ya nufa wajen Dr Olivia, kusan a tare suka iso da ita cikin asibitin. Koda suka ƙarasa cikin Office cikin tsatstsareta da idanu ya ce, “Ya akai cikin yarinyar can bai fita ba? Bayan na baki duk abinda kika buƙata da ga gareni?”.
      Ɗan murmushi baturiyar likitar tayi mai cike da ma'ananoni. Kafin ta ɗago tana kallonsa cikin ido. “Ciki kam na zubar da shi, kuma na saka amata wankin ciki da gwaji domin tabbatar da fitarsa. Sai dai in wani ta sake samu kum.....”
          “You are vary stupid Olivia. Kalleni da ƙyau na miki kama da bakar fatar da zaki rainama hankali ko ki kalla wawa?. Niba likita bane, kuma banda ilimin likitanci, dan haka yaya akayi?!! Ciki bai fita ba!!?”.
    Yanda yay maganar a tsawace da buga tebirin ya sata ɗan zabura kaɗan. Sai kuma ta watsa masa harara ta koma cikin kujerarta ta lafe. Sosai ransa ya sake ɓaci matuƙa, zuciyarsa sai zallo take da tuƙuƙi a cikin ƙirjinsa. Ya nunata da yatsa da faɗin,........✍️

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣4️⃣

.......“Look Olivia, kin san dai zan iya aikata miki komi ko? Ciki harda datse jijiyar numfashinki. Kin sanni na sanki ciki da bai, ki faɗa min yanda akai ciki bai fitaba?”.
         “Mi kake so na sanar maka bayan wanda na faɗa?, Na faɗa maka iya abinda na sani ai, kasan irin haɗarin dana saka kaina wajen maka yanda kake so bayan kauce ƙa'idar allurar daya kamata nai mata. Kaifa ka kawo allurar nan kuma na cika umarninka nai mata, a gabanka komai ya faru kuma ko balle kace na yaudare ka”.
     “Ƙarya kike Olivia, sai dai idan fakar idona kikai kika canja allurar dana baki. Dan babu macen da aka taɓa gwada wannan allurar a kanta hakan ta kasance kema kin sani. Sannan ƙarya kike bakuyi mata wankin ciki ba”.
          Shiru tai kamar bazatace komai ba, sai hucin ɓacin rai takeyi kamar yanda shima yake yi. Wayar landline ta jawo tai kira, kai tsaye ta bada umarnin a sameta a Office. Mintuna baifi uku ba wani nurse baƙin fata ya shigo. Cikin girmamawa yayma Dr Olivia barka da shigowa tare da ɗagama Alh. Sulaiman hannu a taƙaice. Dr Olivia ta dubesa bayan ta zaro wani file a gefenta ta miƙa masa. Amsa yay cikin rashin sanin mizaiyi da shi.
     Ta ce, “Buɗe”.
   Babu musu ya buɗe tare da ɗan duddubawa, sai kuma ya ɗago yana kallon doctor. Kafin yace wani abu ta tareshi da faɗin, “Ban sakaka yima mai wannan file ɗin wankin ciki ba a ranar data samu miscarriage?”.
         Ɗan jimm yay alamar tunani, sai kuma ya dubeta yana cewa, “Ƙwarai anyi haka doctor, sai dai kuma an samu akasi ai a ranar bamuyi mata ba saboda yanayin mahaifarta mukace bayan kwana biyu su dawo sannan ta huta saboda sun matsa a sallameta....”
         A zafafe Alh. Sulaiman ya yunƙuro zaiyi magana Dr Olivia ta girgiza masa kanta. Ita ta ƙara fuskantar Nurse ɗin da faɗin, “Amma miyasa baka sanar min ba? Sannan da baki ka faɗa musu ko'a rubuce?”.
        Kai tsaye yace, “Nazo sanar miki sai na samu kin fita. A rubuce kuma muka basu gaskiya, kuma ita muka bamawa ma a hannunta ai”.
    “Okay zaka iya tafiya”.
  Ɗan rissinawar girmamawa yay tare da ajiye mata file ɗin ya fice. Yana rufe ƙofar ya saki murmushin mugunta, a zuciyarsa yace (Ƴan iska ai dama nayi alƙawarin saina kuɓutar da yarinyar nan. Wankin ciki kuma ina kan sani naƙi yinsa bayan nai mata allurar tsaida jini da sauri ta yanda cikin bazai fita ba. Ina Musulmi baƙar fata bazan taɓa bari a cutar da wani musulmi ba in sha ALLAHU in dai ina asibitin nan. Tunda har naji hirarku dama nai alƙawarin taimaka mata dan na fahimci zaku cutar da ita ne bada saninta ba).
         A ciki kuwa shiru Office ɗin ya ɗauka. Da ga Alh. Sulaiman har Dr Olivia kowa ya kasa cewa komai. Sai can ta nisa da ƙyar ta katse shirun da faɗin, “Yanzu ka yarda na maka aikinka ko? Sannan babu kuskurena a ciki na turata inda za'a mata wankin ciki, kaga kuma sun basu damar su dawo amma baku dawo ba, hakan na nufin yarinyar bata son rasa cikinne ko wani dalili daban.....”
       Cikin wani irin baƙin ciki da zafin zuciya Alh. Sulaiman ya furta, “Dalilinta na banza. Ciki kuma dolene a zubar da shi”.
     “Gaskiya bazai yiwu ba, inba haka ba kuwa komai zai iya faruwa kamar yanda na faɗama Mrs Garko. Ciki kuwa harda rasa ranta. Ni kuma bazan iya gangancin aikata haka ba a wannan gaɓar dan zai zama taka doka, cikin wata biyar da kusan sati biyu, taɓashi da niyyar zubarwa ai kowama yasan ganganci ne. Kawai ku barta ta haihu tunda tana son abinta”.
       “Ashe zan kashe yarinyar nan kuwa!!” Alh. Sulaiman ya faɗa a wani irin kausashe jikinsa har ƙyarma yakeyi. Ita Dr Olivia ma duk sai tsoro ya kamata. Nurse ɗin nan ne yay knocking ƙofar ya shigo, cikin girmamawa ya aje wani file a gaban Dr Olivia a yanayin dafa tebirinta, hakan ya bashi damar zare ƙaramar wayar da ya ajiye batare da sun lura ba saboda rufewa da idanunsu sukayi. Daga haka yay ficewarsa yana ɗan murmushi....
Chapter 18 · 0% Book details