← Book details Furar Danko Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 90

Sashe 88

Furar Danko Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Duk yanda Smart yake kwaɗayin zama kusa da iyalinsa dole ya shirya ya koma saboda cikar kwanakin da aka bashi. Ya tafi ya barsu da kewa kamar yanda shima ya tafi da kewarsu. Haka Iya Tabawa ta cigaba da kula da Lulu. Yayinda Asma'u ta dawo nan dan gidan yay masu girma duk da an zuba ma'aikata kamar su maigadi mai gyaran filawoyi mai wanki harma da driver da mai share-share da sauransu. Sannan Huwaila ma kusan tana anan ne ita da Nadiya. Hakan ya ɗan ragema Lulu raɗaɗin rashin mijinta a kusa da ita. Sai dai akoda yaushe suna maƙale a waya ana video call. Ammah na leƙosu akai-akai, hakama aunty Saliha. A haka sukai arba'in zuwa lokacin ta gama gyagijewa. Ga gyaran Iya Tabawa tana samu mai lafiya dan ita kanta tana jinta on top. Ta zagaye dangi itace har Abuja, kafin ta fara shirin komawa dan Smart ya ishi kowa da damuwarsa. Ammah dai data gaji da yawan ƙorafinsa ta ce ta shirya ta tafi wajen mijinta kozai barsu su huta. Kunya abin ya bama Lulu ma ita. Shiko ta fahimci ko'a ƙwallar rigarsa. Tare da Asma'u suka wuce da Iya Tabawa. Mai gayya da aiki ne da kansa yaje tarbarsu airport, da mamaki yake kallon Asma'u dan bai san da ita za'azo ba. Lulu bata taɓa sanar masa ba har taima Asma'u komai-da-komai na tafiyar. Bai iya cewa komai ba ya kwashesu suka wuce yana ɗauke da yaran duka, sai da Asma'u ta amsar masa AA dan taga sun masa yawa. Tsaff suka samu gidan nasu harda abinci ya tanadar musu. Dan haka babu ɓata lokaci sukayi wanka suka baje. Asma'u ce ma dai keta faman ƙauyanci da santin gidan suko suna mata dariya. Shi dai Smart na manne da yaransa kamar wani yace zai ƙwace masa su, dan gaba ɗaya hankalinsa na kansu ne.. Sai narkakken kallon da yake bin matarsa da shi lokaci-lokaci a kaikaice wanda ita kaɗai ta fahimci abinta. Dan haka taɗan shiga tsoro dan tasan yau kam saita ALLAH wai biri a hannun bamaguje. Gashi tasha gyara kala da iri da ita kanta tasan sai tayi bayani da yaran Jiƙamshi yau kam.
      Kamar yanda tai hasashen kam ta ɗanɗana kuɗarta, yayinda Smarty ya rikice mata tare da sanya mata albarka babu adadi. Tattali kam ta shashi a wannan yinin, gashi dama babu inda ya fita dan haka suka yini a ɗaki da ƙyar yake barinta ta leƙa su Iya Tabawa kodan Asma'u dake fama da baƙunta. Yayinda ya barta da jin kunyar Iya Tabawa, shiko ko'a ƙwallar rigarsa. Bayan dawowarsu da sati uku ya fara nemawa Asma'u gurbin shiga jami'a ta fara, sai dai kullum tana manne da waya suna shan soyayyar su da Hussain ɗin ta, idan kuma ya bushi iska yakan shiryo yazo UK ɗin ya mata kwana biyu. Tayi farin ciki da hakan sosai dan ita mai son karatu ce dama. Shima AA an sakashi makaranta, sai dai ba boko bace ta addini ce da wani balarabe maƙwafcinsu ya ɗan buɗe domin yaran musulmai. Lulu ta cigaba da shayar da yaranta cikin ƙoshin lafiya da kuzari, yayinda suketa ƙara wayo da ƙyawu masha ALLAH. Kamaninsu da mahaifinsu da AA nata ƙara fitowa....

_________★

        Sosai bashi da lafiya. Ya wani irin fita a hayyacinsa tare da yamushewa kamar wani tsoho dan ko Baba Garko bazai nuna masa tsufa ba a yanzu al'amarin zammamaki. Duk wanda yasan Sulaiman ya ganshi a yanzu zai iya dire rantsuwa da bada tabbacin bashi bane. Ya bushe a tsaye ƙwarai da gaske. Tunda aka gama shari'arsu aka kaisa wani mugun jail sau ɗaya Hajiya Turai taje dubashi, ba komai ya kaita ba ma sai amsar takardar sakinta. Dan amaryarsa ita ta samu nasarar amsa tun randa aka yanke musu hukunci. Da ƴaƴansa duka taje, duk da da ƙyar ta samu Tajuddeen ya bita. Ganinsu ba ƙaramin tayar masa da hankali yayi ba ya dinga kuka har suka taho. Sai Daddy dake dubashi duk bayan watanni biyu, amma ƴan uwansa da Baba Garko tun randa aka kamashi basu sake waiwayarsa ba.
       Abinda Daddy ya gano a bincikensa saboda hankalinsa ya tashi da ganin yanda Sulaiman ɗin ya takwarkwashe a cikin watannin da basu gaza goma sha uku ba shine allurar guba akai masa da ke cinyesa a tsaye. Ba kowa bane kuma ya harba masa wannan tsiyar sai abokan huɗɗarsa turawan nan. Dan takanas suka zo Nigeria domin hakan garesa, acewarsa amfaninsa ya ƙare garesu kuma. Wannan allurar ce keta faman cin jikinsa a tsaye batare da kowa ya fahimta ba sai su waɗan da aka haɗa kai da su sukai masan. Tun ciwon na cinsa a tsaye har takaisa ga kwanciya a cikin asibitin jail ɗin. Watansa kusan takwas yana wahalalliyar jiyya kafin ALLAH ya amshi rayuwarsa. Rasuwarsa ta zagaya kowace kafar yaɗa labarai, wasu na masa addu'a wasu na ALLAH wadarai da faɗin sai aje kuma a fuskanci kamun ALLAH. Tsakaninsa da Rasuwar Dada wata biyu ne, dan tunda aka sanar musu sanadin mutuwar Sulaiman bata sake lafiya ba, da ga ƙarshe dai itama sai da ta bisa. Garko family sunji wannan rashi matuƙa. Dan Baba Garko yasha kuka shima har sai da ya kwanta asibiti. Lulu ma tazo, sai dai daga ita sai twins tazo. Satinta uku ta tattara ta koma.

     (Sai muce ALLAH ya gafartama Dada da iyayenmu baki ɗaya 😭👏).

*_YEARS LATER_*

          Barcinsa yake hankali kwance kansa a saman cinyarta. Yayinda ita kuma ta nutsu a masa gyaran kansa. Da farko hira sukeyi a hakan. Sai dai tunda taga barci ya ɗaukesa ta canja akalar gyaran gashin zuwa kitso kasancewar ya tara suma sosai a kan nasa. Sai dai normal askine a kansa ba irin na rashin mutuncin nan da aka san ƴan ƙwallo da shi ba. Tsaff tai masa kitso guda takwas tana kwasar dariya. Hakan bai mata ba ta zame kansa a hankali zuwa saman filo taje gaban mirror ta kwaso kayan kwalliya. A hankali ta zane masa fuska ya fito ras kamar wani mace. Sannan ta fara zuba masa hotuna. Kukan autanta da take jiyowa da ga falo ya sata ajiye wayar ta fita. Ilai kuwa shi ɗinne dan a hanya suka haɗu yana kuka.
      “Kai kai waya taɓa min Ubana haka?” ta faɗa tana riƙosa yaron da bazai wuce shekaru uku ba zuwa jikinta. Cike da shagwaɓa ya ce, “Ba aunty Hafcy bace ba. Wai dan nace mata Hassatu shine ta mintsineni da rankwasar min kaina”.
     Daƙyar Lulu ke danne dariya, dan kowa a gidan yasan masifar Hafsat ta dabance. Sam bata gado Ammah ba itakam. Gaba ɗaya a hallaya ita ta biyo. Sannan bata yarda a kitata Hafsatu ba. Tace sunan mutanen da ne ita Hafcy gayu take so.......✍️

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣6️⃣ 🔚
Chapter 88 · 0% Book details