← Book details Furar Danko Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 90

Sashe 4

Furar Danko Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Eh to ko zuwa yamma haka tunda ga su Khamil da iyalansa nan sun iso ko, auta ma yace min zai baro Saudiyya shi da matarsa gobe in sha ALLAH. Kaga dai ai ka sake samun masu kulawa”.

Murmushi yay mata cikin nuna gamsuwa. Dan Dada kam a wajen bama miji kulawa jaruma ce, tsaye take kan abinta ta kankane ko ina tunda ƙuruciya har girma babu wata mace data taɓa raɓar mata miji da sunan kishi. Wannan tsananin kishin nata yasa hatta matan ƴaƴanta take jin kishinsu akan ƴaƴan nata da suma take matuƙar so da ƙauna tamkar ubansu. Babu ɓata lokaci ta hau shirin wucewa Canada, dan ji take kamar ta rufe ido ta isa taga hanlin da ƴar jikarta take a ciki, saboda a nata bahagon tunani babu abinda zuciyarta ke raya mata sai kodai Smart, ko Uncle Yousuf wani ya sakema Mawaddat asiri ne.

Dai-dai lokacin da Lulu ke cika awanni goma sha ɗaya a asibitin su Dr Olivia Dada ke isowa ƙasar ta Canada. Tunda ƙuruciya an riga da an san lungu da saƙo na ko'ina, dan a duk ƙasar da suke yawan zama suna da gidansu na kansu musamman manyan ƙasashen nan masu ji da kansu irinsu England, America, France Chaina, Saudiyya, Dubai, dan da gasken gaske wannan family sunada dukiya, bayan wadda mahaifinsu ya gada a wajen nasa mahaifin ya kuma tara nasa na kansa, su kansu yaran kowanne ba ƙyalan bane wajen kuɗin, dan babu wanda ke zaune kaf ɗinsu a neman na kansu suke. Ko marigayiya Mawaddat mahaifiyar Lulu data kasance mace ɗaya tilo a cikinsu sanda tana raye tsaye take akan neman na kanta saboda haka aka gina musu rayuwa, duk da yana da dukiya kuma ya gada ne shima a wajen mahaifinsa bai yarda yaransa su zama cima zaune ba, suna ayyuka a cikin gwamnatin ƙasarsu da na wasu ƙasashe, suna kuma Business ƴaƴa da iyaye har ma da jikoki. Cab ta ɗauka tun daga airport zuwa asibiti kai tsaye, dan a ƙage take da son ganin halin da jikar tata ke ciki. Wadda har yanzu ana kan tafka rigima akan ɓoyetan da tai dan bayan ita sai Alh. Sulaiman kawai suka san ina Lulun take. Hatta da Tajuddeen sunƙi sanar masa. Ita Dada zuciyarta ɗaya ce game da ɓoye Mawaddat dan kawai ta rabata da Smart ne matsayinsa na talaka jikanta Tajuddeen ya samu. Yayinda shi Alh. Sulaiman ba haka kawai bane a tashi zuciyar, dan a yanzu haka bai fara aiwatar da plan ɗinsa bane akan Lulun sakamakon rasa inda Smart yake da yay shi kuma. Dan tun washe garin da Smart ya baro 9ja yasa malami binciko masa shi amma ƙasa ko sama babu labarinsa. Amsa ɗaya suke samu a bincikensu shine ya ɓoye kansa dan kar ya saki Lulu. Duk da dai suna zargi Uncle Yousuf ne ya ɓoyesa amma a ɗan tsukunnan sun ƙara tsananta bincike kasancewar har yanzu basu sami wani point ba akan hakan. Dan shi Uncle Yousuf ɗin ma ya sake baro Nigeria ɗin zuwa harkokinsa da ya bari bayan yayma Daddy tas da tabbatar masa da cewar ya zare hannunsa akan al'amarin Lulu, dan ya fahimci goyon bayan da Daddyn ke batane a baya ya bata lasisin biyema Dada tabar gidan aurenta. Saboda ya tabbar da babu haɗin kan Lulu Dada bazata taɓa iya ɗauketa a gidan aurenta ba harta ɓoyeta gashi ana neman wata uku kamar wasa.

*_NIGERIA_*

Sosai Daddy yana cikin wani hali na azabtuwar zuciya game da abubuwa da yawa. Na farko shine ɗan uwansa dake fushi da shi. Ƙaunar da yakema Yousuf a zuciyarsa daban ce a wannan duniyar, dan zai iya rantsuwa ko ƴaƴansa baya musu irin wannan ƙaunar har Lulun da ake kallo ya fifita. Na biyu rashin sanin inda Lulu take har yanzu, tun yana ɗaukar al'amarin wasa Dada zata dawo da ita bayan wasu kwanaki har lamarin ya fara bashi tsoro. Lokacin da yaje UK duba Baba Garko har roƙonta yay akan tayi haƙuri Lulu ta koma gida koda bazata koma gidan mijin ba, dan tabar aikinta da mutane ke matuƙar buƙatarta. Amma sai Dada ta murje idanu tai masa tas dole yaja bakinsa yay shiru dan yana ɗaga mata ƙafa kodan darajar sunan uwa da take amsawa. Sannan fa Daddy dama can Uncle Yousuf ya fishi zafi, shi dai barsa da zuciyar tsiya kamar ɗan kuturu. Abu na uku wani salon rainin wayo da Alh. Sulaiman ya ɗan fara kawo masa da nuna shi yanzu a shirye yake da shi akan komai, sai zuciyarsa ta fara bashi anya kuwa bada haɗin kan Alh. Sulaiman ɗin Dada ta ɗauke Lulu ba kamar yanda yay zargi tun farko. Idan ko haka ne to tabbas a wannan karon ya shirya duk wacce ma za'ai ayi shima. Wannan tunanin ne ya zaburar da shi yau daga gida daya fito yace driver ya wuce da shi office ɗin Alh. Sulaiman Sufi Garko. Sanda suka iso ma shi bai kai ga isowar ba, dan haka sukai zaman jiransa. Baifi mintina bakwai ba a tsakani sai gashi shima. Sai da ya shiga da kusan mintina huɗu drivern Daddy ya shiga ya nema musu iso. Alh. Sulaiman da tun shigowar Daddy cikin Companyn aka sanar masa, yana shigowa kuma ya shaida motarsa yay wata dariyar mugunta da bama sakatariyarsa umarnin shigo da shi.

Tunda Daddy ya shigo Alh. Sulaiman da yay wata kishingiɗar iskanci a kujera yana jujjuya kansa ya saki murmushi mai ma'anoni da yawa. Yi Daddy yay kamar bai gansa ba, sai ma ya kai zaune duk da ba'a bashi damar hakan ba. “Ina fatan kana lafiya?”. Daddy ya faɗa a takaice. A gatsine Alh. Sulaiman ya amsa masa da “A office ka sameni ai ba'a gadon asibiti ba”.

“Kuma haka” cewar Daddy a gatsine shima. Batare da ya jira cewar Alh. Sulaiman ɗin ba ya cigaba da faɗin, “Sulaiman ina kuka kai min yarinyata?”.

“Ka shirya ganinta yanzu kenan?”.

Idanu Daddy ya tsurama Alh. Sulaiman cikin ɓacin rai, sai dai kafin yace wani abu Alh. Sulaiman ɗin ya ƙyalƙyale da wata dariyar mugunta yana miƙewa tsaye. Takowa yay inda Daddy yake ya ja kujerar dake kallon wadda yake zaune shima ya zauna tare da ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya. Fuska ya tsuke ya zubama Daddy dake kallonsa cike da tsana idanunsa shima. “Isma'il Ibrahim Jiƙamshi! A da kana ɗaukar duk zantukana matsayin kurari ko? Kana tunanin bazan iya illata rayuwar Mawaddat ba dan kawai tana ɗiyar ƙanwata?. To kayi kuskuren sanin waye ni, dan zamanka da ni na tsawon shekaru bakwai bai maka amfanin komai ba kuwa. Bari kaji wlhy wlhy da ace na san da wannan sirrin a hannun Mawaddat ƙanwata kafin mutuwarta, ni da hannuna zan kasheta bayan na amsa, sai ALLAH ya taimaketa ta mutu a karan kanta kafin na sani ɗin, amma duk da haka bata tsiraba ta barma ƴarta gadon laifinta. Dan haka Isma'il ina maka gargaɗi na ƙarshe, ka bani camara ɗin nan, ka kuma saka a ranka baka taɓa sanina ba har abada, in ba hakaba, a wannan karon saina wargaza rayuwar kaf family ɗinka bata Mawaddat kawai ba. Dan haka zaɓi ya rage naka....”

Murmushi Daddy yay mai ma'anoni da yawa duk da yasan duk abinda Alh. Sulaiman ɗin ya faɗa zai aikata fiye da hakan. Amma cikin nuna halin ko in kula idonsa akansa kyam ya ce, “Sulaiman kenan. Ka manta ni Isma'il ɗin wanene nima. Sannan banda haukarka a tunaninka baka camara na nufin gogewar abinda ka tafka da in kaf family naka sukaji sai sun maka tsanar da sai ka gwammaci mutuwa da rayuwa. To idan ka manta bari na tuna maka, bayan abinda Mawaddat ta ɗauka nima ai nasan komai, ko toshewar basirar taka takai ka manta cewar komai na sani tunda da bakinka ka kirani ka sanarmin abinda kayi kuma na gani da idona, hasalima tare dani ka ɗauki yarinyar ka kai ƙasan gotter ka jefar. ai ba abinda Mawaddat ta ɗauka bane kawai hujjar. Sannan na biyu Sulaiman kada ka manta a tafin hannuna kuke kai da su Alh. Baita, idan yanzu na sanarma duniya su waye ku a ƙasar nan wlhy wlhy ba dukiya ko matsayi ba sai anyi faca-faca da namanku da taimakon mahaifinka dan kafi kowa sanin irin tsanar da yay ma abinda kuke aikatawar. Ai dama na sanar maka tun a waccan ranar, sai na ɗan ɗana ma zuciyarka rayuwa cikin fargaba da zullumi fiye da yanda ƙanwarka ta ɗanɗana min a tsahon shekara ɗaya dana rayu da ita.....”

“Nima ai na tabbatar maka sai dai mu rayu a tare cikin zullumin da fargabar ko ka manta”. Alh. Sulaiman ya faɗa a zafafe cikin katse Daddy. Sai kuma ya ƙyalƙyale da dariya da faɗin, “Isma'il kenan a tunaninka kaima ban san a yanda ka rayun bane, ko cakake ban san kaima kana rayuwa bane cikin irin yanda kake tunanin ka sani a tsahon waɗan nan shekarun. Ka gaya min inba tsoro ba miyyasa ka ɗauke ƴarka daga Nigeria da ga randa na tabbatar maka saina hukunta rayuwarta bisa laifin mahaifiyarta? Miyasa kaketa kaffa-kaffa da ita fiye da sauran ƴaƴanka?. Amsar itace Tsoro ne! Kana jin tsorona Isma'il!! Hhhhh tabbas wannan tsorone!!”.

Da ƙarfi Daddy ya buga decks tare da miƙewa a zafafe.........✍️

Tofa fagen na manya ne yau🚴🚴🚴

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣
Chapter 4 · 0% Book details