← Book details Furar Danko Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 90

Sashe 72

Furar Danko Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

  Alhamdullah an samu nasarar dawowar Ummah dai-dai, nakan dutse ya gama kunce ƙullin daya ƙulla su Salim suka miƙashi hannun ƴan sanda batare da sun saurari bayanin da yake musu akan bafa wai Ummah ta kuɓuta bane ba ɗari bisa ɗari, dolene sauran bala'oin data saka akai mata aiki akan Smart ɗaya bayan ɗaya zasu cigaba da dawo kanta. Sai ta shirya. Babu wanda ya sauraresa, sai yan jarida da suka kafa suka tsare har sai da suka samu cikakken bayani a bakinsa. A take fa al'amarin Umma ya shiga media da duniyar yanar gizo dana kafafen ƴaɗa labarai musamman irin na rediyo. Kafin kace mi mutane da yawa sunji kuma sun sani anata ALLAH wadai da al'amarin nata tare da mata irinta.
     Ana wucewa da nakan dutse dole itama Ummahn aka kwasheta zuwa asibiti dan hawan jini ya mata biji-biji. A asibitin ma dai ƴan jarida basu barsu sun huta ba da jama'ar gari ƴan so da jin ƙwaƙwaƙwaf. Musamman ma da ya zam hotunan Ummah sun gama zagaye gari a suffar Dodo, saboda lokacin da nakan dutse ke ƙoƙarin warware asirin mutanen da suka samu shigowa musam yaran maƙwafta ɗauka suka dinga yi a wayoyi suna sakawa a shafukan su na sada zumunta. Dan danan fa sunan Ummah da Hajiya Naqiba yay amsa kuwwa a duniyar labarai da yanar gizo. Dan hatta Hajiya Naqiba basu bari ba sai da suka bibiyi al'amarinta.

      (Su Umma an zama celeb.... sai ku tayata murna🤣😂).

    A washe garin da aka wuce da Umma asibiti Smart ya buƙaci su koma gidan daya kama musu domin fara gyara wanda suke a ciki. Kusan dama a shirye suke da hakan, dan haka babu ɓata lokaci suka tattara zuwa can ɗin nan kuma aka bajeshi aka fara aiki bisa tsayawar Coach da manyan yaran gidan duk da Salim ya nuna hassadarsa a fili. (Nonon Ummah ba wasa ba ai🤣🙏).
     Suko su Mubarak farin ciki suke abinsu ganin za'a gyara musu gida. Sai addu'a da fatan alkairi suke jerama Smart. Mazansu da matansu haka suka dinga kiransa suna godiya. Duk da wasu sun gagara hakan musamman a mazan saboda baƙin ciki. Dan Mama ita kanta a wannan gaɓar Hassadarta ta gagara ɓuya. Sai da taga Abba na neman birkice mata ne fa ta kama kanta. Sai ƴaƴanta mata da suka nuna mata karfa ta tafka kuskure makamancin na Ummah. Dole ta kama kanta ta koma yaƙe da addu'a a fatar baki. Ƙasan zuciyarta kam kamar zata ƙone, a ganinsu dai ƴaƴansu ne sukafi cancanta da wannan arziƙin.

     Ni dai nace, “Hummm🥱🚴🚴”.

__________★

      A ɓangaren su Alh. Sulaiman suna tsaka da kukan targaɗe sai ga karaya ta samu. Dan kuwa dai al'amarin Nadiya ma ya bayyana wa duniya. Inda ta tabbatar da cikin jikinta na su Hon. Nakowa ne dan su duka babu da wanda bata mu'amula. Ta kuma tabbatar da cewar su ɗin manyan diloli ne na miyagun kwayoyi, dan ko ita sune suka koya mata shaye-shaye. Ta kuma tabbatar da in har sunce ƙarya ne su fito duniya su musa zancenta ita kuma zata bada manyan hujjoji a kansu. Tace bayan itama akwai yara da yawa da suka lalatama rayuwa ta hanyoyin shaye-shaye da zinace-zinace. Wasu sun jima da rasa ransu, wasu iyayensu sun koresu a gida sun shiga duniya. Wasu kuwa a gidan iyayen nasu ake lalata musu rayuwa batare da iyayen ma sun sani ba. Acewarta Bama su kawai ba, akwai manyan ƙasar da dayawa sukai suna da nisa a irin waɗan nan al'amuran, su suyi ƴaƴansu suyi. Ba kunya Uba da ɗa za'a haɗu a club ko da ƴa anama juna kallon kallo. Akwai wanda ake kaima yara ƙanana gida suyi musu fyaɗe, wasu ma harda maza sukemawa. Ta tabbatar da idan zata tona asirin mutane da yawa akan wannan al'amarin tofa manyan nan da yawansu bazasu sha ba a bisa madafun ikon da suke kai. Dan haka a rufe rufau kawai. Wannan video ya girgiza al'umma da yawa. Yayinda ya bama wasu da ke fuskantar irin raɗaɗin da Nadiya ke a ciki fitowa suma suyi magana. Fiye da yanda ba'a zato al'amari ya sake rincaɓewa. Dan kuwa a ranar kame na hauka jami'an tsaro sukayi, kuma duk yaran su Alh. Sulaiman ɗinne da Nadiya ta dinga lissafowa a faifai. Inda kuma duk akayi dacen kamasu dumu-dumu da abinda ta lissafa ɗin kasancewar dama sai da aka shirya musu talala aka saki video ɗin.
     Zuwa yanzu kam su Alh. Sulaiman sun tabbatar da akwai mai musu zagon ƙasar nan. Duk da shi zai iya bugar ƙirji akan babu ruwansa da wata yarinya a cikin garin kwano. Iskancinsa a wajen Nigeria yakeyi sai ko Lagos. Dan budurwarsa ɗaya ce tak a Nigeria kuma a Lagos take zaune. Asalinta ma ba ƴar 9ja ɗin bace shine ya kawota ya ajiye. Sai dai kalmar fyaɗe da akace akwai masu yima yara kam ya girgiza shi, dan abune da anan kam baida tacewa. Dan haka idanunsa suka fara rufewa ya dannama Daddy kira dan ya fara ji a ransa anya Daddyn baida wata rawa da yake takawa a al'amarin nan kuwa. Duk da a yanzu haka ana tsaka da masa bincike akan *_AMM_* ɗin nan da ya aiko masa da takarda da hotuna, har yanzu kuma ya kasa hasaso kowa, ba komai ya jawo haka ba kuma sai kansa dake a birkice.....

★★ Daddy na a gidansa hankali kwance dan kallon wasan su Smart ma yake tare da su twins. Da farko kamar bazai duba mai ma kiran nasa ba sai kuma dai ya ɗauki wayar. Yasha mamakin ganin Alh. Sulaiman Garko. Har ya maida wayar ya ajiye da nufin sharesa sai kuma dai ya ɗaga tare da miƙewa ya shige bedroom ɗinsa.
       Cikin wata irin gigitacciyar tsawa Alh. Sulaiman ya ce, “Isma'il mai kake tunanin ka taka ne?!”.
     Daddy ya saki murmushi mai sautin da har Alh. Sulaiman na jiyosa. Kansa tsaye babu alamar ɗar a tattare da shi ya amsa masa da faɗin,.......✍️

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣3️⃣
Chapter 72 · 0% Book details