← Book details Facala Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 21

Sashe 9

Facala Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

agaba suka sanya shi har zuwa cikin gidan.
Alhaji Badamasi ya waro ido waje, ganin ɓangaren Ahmad ɗin a ƙone amman kuma kamar an fara gyara ma, sannan kuma duk motocin gidan babu su to me ya faru kuwa? ko da yake shi labarin zuciya ai sai atambayi fuska don kuwa ga alamu nan sun nuna akan fuskar Ahmad, duk yadda akayi aƙwai abinda ya ke faruwa don gashi nan yaga ɗan na sa duk ya rame sosai, sai farin da ya ke dashi kawai da hanci duk ya lalace ya zama abin tausayi.
Malam ma dai ya yi shiru ne, amman sosai ya tsorata ganin ɓangaren ƴarsa a ƙone, gashi kuma har ana gyarawa to me hakan yake nufi? gobara sukayi kenan? amman ko kusa Rabiatu bata faɗa musu ba? duk da wannan shi ne karo na biyu daya shigo cikin gidan amman sai yaga abubuwa da yawa sun sauya ba kamar wancan ƙarnin da ya zo ba, awancan ƙarnin komi yana muhallinsa ne, ba kamar yanzu da gidan ya zama wani iri ba, duk da ba tsufa gidan ya yi ba amman kana ganin gidan kasan aƙwai matsala acikin gidan, haka Mlm ya ke da wannan baiwar idan ya shigo waje ko gida wanda ake taɓargaza acikin jikinsa ya ke jin hakan, kuma sai tsigar jikinsa ta tashi sosai.
[2/26, 6:54 PM] Ummu Maher Ce: ➡️7
…………...... suna shigowa suka iske Balaraba zaune tana kallo a tv, ta ƙurawa tibin ido tamkar zata ciro wani abu aciki ga kuma fuskarta cike da tsananin murmushi kana kallonta kasan tana cikin tsananin farin ciki.

tana ganinsu ta tashi cike da salon munafurci ta ce" sannunku da zuwa, kune atafe? bari akira adawiyyar ta fito ku gaisa".

Alhaji Badamasi ne ya katse ta da ce wa" dawo ki zauna kafin ki kirawota ɗin, aƙwai ƴan tambayoyin da zamuyi miki idan babu damuwa".?

Cike da fargaba ta fara magana muryarta tana É—an rawa "eh eh ato ai ba komi kuna da damar yimin duk tambayoyin da zakuyi".
Alhaji Badamasi ya kalle ta da kyau, irin kallonsu na manya sannan ya ce" dama tambayarki zamuyi ta ya akayi har wani namiji ya shigo gidan nan ba tare da ke kin sani ba? har abinda ya faru É—azu ya faru É—in".
Da ƙer ra haɗiye wani malulu sannan ta ce" to Alhaji idan mace tana son aikata abinta ai tasan ta yadda za tayi, har ta aikata ɗin ba tare da kowa ya sani ba sannan kuma ni aganina ai ita Rabiatun ya kamata a yiwa wannan tambayar ba ni ba, ai ba a tambayi kaza hanyar rafi ba".

Sosai kowa ya yi mamakin kalamanta, amman banda Alhaji Badamasi don ya fi kowa sanin wacece Balaraba, shiyasa tun farkon asali bai so har ta shigo cikin familinsu ba, don ba alheri bace sam musamman yadda ya ke da tarihin gidansu da duk ta'asar da ita Balaraban tayi, ajaf ƙannenta da yayyinta babu wanda ya kama ƙafar Balaraba a yawo da kuma bin maza, shiyasa komi akace zata aikata zai yarda.

Cike da jin haushinta Alhajin ya ce" ok saboda ita Rabiatun ita kaɗai ce agidan? bari in faɗa miki ma kiji babu wanda zai je ko nan da can agidan nan, dukkaninku folis za a kira suzo su ƙwashe mana ku, gayyar masifa da tsiya".

da sauri Mlm ya yi magana, ganin kamar Alhajin awuya ya ke ya gyara zamansa sannan ya ce" tashi ki kira mana Adawiyyar, sannan koma menene Allah zai bayyana mana shi wataran gari ya waye kowa ya gane inda matsayinsa ya ke".

Wannan maganar ta mlm ya sanyata jin wani irin haushin mlm ɗin, sannan ta fara tsarguwa da kanta ko dai sun gane ta ne? idan kuwa haka ne ya zamar mata dole ta ƙara yin wani shiri, don ita dai bazata taɓa son Rabiatu ba saboda yadda take jinta azuciyarta ko kishiya akayi mata ba za taji yadda take jin Rabiatu azuciyarta ba, don ita aganinta ai FACALA tafi kishiya, kuma da ma an gano tane ba zata daina yi mata makirci ba don sai taga abinda ya turewa buxu naɗi.

lokacin ne na tashi daga nannauyan barcin daya sameni wanda ban san lokacin dana fara yinsa ba.
ina fitowa daga banÉ—aki naga Balaraba tsaye akaina, tana yimin wani irin kallom hadarin kaji sannan ta ce" kije inji tsohonki".
Tana faÉ—ar hakan ta fice tana wani juyi.
na kalle ta kawai ina mamakin halinta ita akoda yaushe bata taɓa canjawa daga Balarabanta tana nan dai da halinta na rashin mutunci.
ina fitowa falon duk suka bini da kallo, sai na tsargu sosai da irin kallon da suke mini ga ya Zubair shima shigowata ya shigo, ga Alhaji da Mlm ga me gayya me aiki wato ya Ahmad.

Bayan na gaishesu ne Alhaji ya fara faɗamin wata magana, wacce ta sanyani zaro ido gamida tsorata sosai alokaci ɗaya naji ina shirin sakin fitsari saboda abinda ya tsargamin tun daga ƙwaƙwalwata har zuwa ƙafafuwana.

kuka na fara yi ina ce wa" innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wata masifar ce ta ƙara samuna bayan wanda nake ciki ya Allah ka nunamin mutuwa yanxu, saboda ƙwaƙwalwata ba zata iya ɗaukar wannan gamin ganbizar ba".
Sosai kowa ya ke nazartata ya Zubair ya ce" mlm ni fa sai nake ganin anya babu wanda ya ke mata zagon ƙasa, saboda abin fa ya yi yawa ga cikin da akace tana dashi wanda shi mijin na ta yace bai san dashi ba, to kuma sai ga wannan ma ni aganina atsaya ayi bincikr sosai don wallahi abin ya fara bani tsoro".

Dukkansu zaro ido sukayi gamida haÉ—a baki wajen ce wa" ciki kuma"!?.......

Ni dai kuka kawai nake ina sharce majinar da ta samu damar fitowa tamkar me yoyon majina, suka kasa magana saboda tsorata da al'amarin yarinyar da bata saba bin maza tana budurwa ba sai ace yanzu da aurenta rana tsaka ta farayi? wannan ma ai abin aduba ne.

Alhaji Badamasi ya yi gyaran murya ya ce" Zubairu wani asibiti kuka je"?.
Ya ce" special hospital ne".

Ya ce" ku tashi mu tafi asibitin sannan ka nuna min likitan sannan kuma agabanmu a ƙara yi mata wani gwajin, mu gama da wannan masifar kafin sai mu dawo wannan don wannan maganar har tafi wannan matsala don wannan kunyar duniya ce, har da ta lahira don idan ka haifi ɗa ubansa yana bai san da cikinsa ba ai babban tashin hankaline".

dukanmu muka ɗugunzuma zuwa asibitin. da sauri ta fito daga maɓuyarta hankalinta duk atashe, ɗan cikinta sai dawowa ƙasa ta ke yana wutsil wutsil ga khadija da ta tashi daga barci sai kuka take, amman ita ko ajikinta hankalinta da nutsuwarta baki ɗaya suna kan wayarta, tana ce wa" shikkenan tawa ta ƙare, khalid yana ganin an tsare shi zai iya tonamin asiri, amman yanzu zan yiwa tufkar hanci don bazan bari asirina ya tonu ba"........ tana faɗar hakan tana zufa tamkar wacce tayi aikin gona ko kuma wani aikin wahala.

*** *** ***
Yarima ne zaune ga su Shamaki su santali da wambai, da ya ke duk abokansa ne kuma kusan kansu É—aya ma, amman ko kusa babu Aamiru balle me kama dashi don tunda abin nan ya faru tsoron ma haÉ—a hanya ya ke da Galadima É—in.
Shamaki sai dariyar ƙeta ya kewa Galadima ya ce" to yallaɓai lokaci fa ba jira ya ke ba, kai gidanka zamu rakaka mu kuwa gauraye gida zamu dawo komin dare, saboda haka ka tashi mu rakaka gidanka idan ba haka ba kuma mu koma mu ƙwanta, don wallahi duk agajiye muke".

Galadima duk yana jinsu, amman ya kasa ce musu uffan shi kaɗai yasan halinda ya ke ciki agameda auren nan da akayi masa, ya yarda ne saboda babu yadda zaiyi amman da yana da yadda zaiyi da babu abinda zai sa ya amshi wannan auren, don zuciyarsa ta riga da ta yi saranda ga wata mace can daban, wacce tayi ƙawanya a ƴar ƙaramar rayuwarsa wacce yake riritawa, sai dai babu yadda zaiyi ko yana so ko baya so dole da Amira zaiyi rayuwar aure, wanda ko kusa baya son haɗa wata da gimbiyar mata sarauniya ta cikin zuciyarsa,wacce ya sanya makulli ya rufe saboda baya son haɗa soyayyarta da kowacce mace, babu yadda zaiyi dolensa ya tashi ya kalli su Shamaki ya ce" zaku iya komawa inda kuka fito, tunda dama bani na gayyato ku ba".
yana faɗar hakan ya wuce abinsa, shamaki dasu wambai suka tuntsire da dariya sukace, eh munji kace haka mana tunda kai yanzu kafi ƙarfin layinmu muma da za'ayi mana wannan auren gatan da munji daɗi".

Amira ce ƙwance akan cinyar Hafsah sai kuka take, tana ta bata haƙuri da ta gaji ta ce" munafuka kawai, kina son abu kina kaiwa kasuwa naga da kanki kika ce kina sonsa kuɓa shi ne yanzu zaki yi wani kuka".
Amira ta É—aka mata duka acinyarta, autar momma ta ce"eh kya dakeni mana tunda ke yanzu antina ce ke, sai yadda kika yi dani ai Allah yasaka min".
Amira ta fara dariya tana goge hawayenta ta ce" eh nima ai matar yayana ce ke".
tuni taji wani irin abu ya tsarga mata acikin zuciyarta, ta sanya hannunta dai dai kam zuciyarta, tana ta bugawa da sauri sauri son Aamiru ne damƙe azyciyarta amman tana son koyawa kanta rashinsa, sai dai hakan ya faskara saboda tana sonsa ne bilhaƙƙi da gaskiya, jiya ma tana ganin misscalled ɗinsa taƙi ɗaga wayar, haka ya dinga danno mata kira yafi sau shurin masaka amman tayi burus dashi, sannan ya dinga turo mata saƙo shima taƙi karantawa sam taƙi buɗe ɓangaren message baki ɗaya, so take ta ciresa baki ɗaya amman ta kasa hakan saboda ya riga daya gama dilmiyar da ita kogin sonsa.
da sauri ta kama hannun Amira, ta wayance ta ce" yanzu shikkenan kinyi aure kin barno besty? Shikkenan mun dena zuwa shan icecream tare"?.
Haba tuno da wannan da sukayi abinka da yarinta ai sai suka fashe da kuka tamkar Æ´aÆ´an mage.

Tsaye ya ke akansu, yana ganin yadda suka rungume juna suna ta faman kuka, tausayinsu ya tsarga masa azuciya sai dai hakan beyi tasiri azuciyarsa ba, ya yi musu gyaran murya gamida haÉ—e fuska tamkar hadari.
Chapter 9 · 0% Book details