Sashe 17
Facala Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read
Amrah ta farka daga nannauyan barcin daya ƙwashe ta, tana buɗe idonta akan mahaifiyarta da kakarta ta sauke ido ayanayin da ta gansu ya bata tsoro, don kuwa kowannensu idonsa ya kaɗa ya yi jawur, tamkar garwashin wuta kuma babu me cewa kowa komi, ta ƙarewa ɗakin kallo ta tabbatar da tana asibiti ne ta fara tariyo dukkanin abinda ya faru da kuma abinda yasa aka kawo ta asibiti, ta ji fuskarta duk atamke tamkar an ɗaure ƙunshim wanki, ta fara kuka ƙasa ƙasa Hajiya Rabi ta juyo kukanta, ta taso da saurin gaske tana ce wa" Alhamdulillah Allah abin godiya, sannu da tashi Amrah?".
sosai take kuka, ba kuma kukan komi take ba sai kukan rasa Galadima da tayi, ta tuna fa yanzu yana can da matarsa ya manta ma da ita baki É—aya, ta rushe da wani wahallan kuka tamkar an mata mutuwa.
*** *** ***
Rungume ni yayi tsam a ƙirjinsa, ya shaƙi iskar ƙamshin dake tashi akaina sannan ya ce" Rabiatu ki yafemin dukkanin abinda na yi miki, wallahi kuskure na na ɗan adam ke ɗin zumace ta Ahmad babu namijin da zai kasance dake a inuwa ɗaya yace baya son ya ƙara kasancewa dake, in sha Allahu daga yau ba zan ƙara ɓata miki ba wanda ma nayi abaya zan cigaba da roƙon Allah ya yafe min, sannan zuwa nan da ƙwana 5 za'a kammala gyara ɓangarenki komi kuma sabo za'a sanya miki kamar yadda kema kike sabuwa dal".
na ɗan saki murmushin jin daɗi sannan na ce" haƙiƙa wannan rana tana ɗaya daga cikin tarihin rayuwata, bazan taɓa mantawa da wannan lokaci da muka kasance tare ba, Allah ya ƙara mana xaman lafiya me ɗorewa sannan nima ka yafemin duk rashin kunyar dana yi maka abaya".
Rungumoni ya yi sosai har muna jiyo numfashin juna sannan ya ce" kada kiji komi ni babu abinda kika yimin idan ma kinyi min É—in na yafe Allah ya yafe mana baki É—aya".
Sosai muka farantawa juna ranar, da kanshi ya shiryani tas cikin wata atamfa doguwar riga cikin sabbin ɗinkin da basu ƙone bane suma zamana agida Ammi ta ɗinkamin su guda biyu.
na yi kyau tamkar É—awisu, daman gashi Æ´ar É—agwas dani duk da ba nida hasken fata amman fatata tana da wani irin sirri na musamman wanda Allah yayi min baiwarta, har wani shining fatata take yi daman oily skin ne dani, irin me walaniyar nan.
naci ɗaurina ture kaga tsiya, nayi kyau sosai shima ya sanya wani farin yadinsa wanda ya zauna masa das ajikinsa ya feshe mu da turaruka kala kala, ya miƙomin hijabina awanke agogo na riƙe ahannu amman bai ce in saka ba ya riƙo hannuna muka fito sai ƙamshi muke gabzawa yana jana muna wasa da dariya.
Sosai ta bani tausayi, tana zaune kan kujera me cin mutun biyu daga ita sai zani da wata t shirt fara ko ɗan ƙwali bata saka ba, kitson atach ɗinta daya daɗe ya cuccure waje ɗaya sai jelar gashi kamar wacce ta zare ko kuma ta fito gidan mahaukata, ga Nana agefenta tana wasa tibin bango tana ta aikinta gashi ta ƙure fanka sai aikinta take, idanuwanta na kan tibin waɗanda suka kaɗa sukayi jawur tamkar garwashin wuta, sai cije leɓenta take da yake fara ce tas na bilicin sai fuskarta tayi jawur tamkar an yaɓa mata yaji.
Jin takun tafiyarmu ya sanyata juyowa tana kallon inda take jin takun, daman gashi takalmina me É—an tsini ne don kusan takalma duk haka suke.
Sosai ta nuna baÆ™in cikinta, har ta gaza É“oyewa ta tashi tsaye ta nufo inda muke.............soonâž¡ï¸
MRS GREEN CE.
[2/26, 6:54 PM] Ummu Maher Ce: https://whatsapp.com/channel/0029VaEuTqi17En0eYizXq3d
Follow my whatsapps channel👆ðŸ»ðŸ‘†ðŸ»View link.
âž¡ï¸15
...................tana isowa garemu ta gaza ɓoye baƙin cikinta ta ce" uhm au idan za'a tafi unguwar ma baza'a faɗa ba? sai dai kawai muga baƙwa nan"?.
ya ƙara riƙe hannuna tamkar za'a ƙwaceni daga gareshi sannan ya ce" haba antinmu ya zamu tafi bamu faɗa miki ba? ai yanzu zamu tafi daman zamu faɗa miki kuma ashirya Nana mu tafi tare".
kamar kuwa nanan tasan me akace ta rugo da gudu ta ɗafesa, daman kuma ya saba yana mata wasa. Balaraba ta gallamin harara lokacin da Ahmad ya juya, ni kuwa na sakar mata murmushi na riƙo hannun Nana muka fito abinmu.
Turus nayi ganin sabuwar mota dal awaje, baƙa ƙirar jif tayi masifar kyau da haɗuwa na juyo ina kallonsa na ce" ya Ahmad wannan motar waye? ko ta yaya Zubairu ce"?.
ya ɗan murmusa yana ƙarasowa daf dani, ya ce" motata ce Hubbi ɗazu ɗazun nan Alhaji ya aikomin da ita wai musha amarci da ita tunda dai ni nawa duk sun ƙone".
Sosai na saki fara'a saboda ina matuƙar tausayawa ya Ahmad, saboda aikin da yake zuwa musamman ma idan zai yi tafiya sai dai yaje ya hau ta haya? abin yana taɓa zuciyata idan na tuno da hakan sai dai babu yadda zamuyi da ƙaddarar Allah tunda hakan Allah ya tsara.
ya riƙo hannuna muka wuce muna zabga ƙauna, Balaraba kuwa bata san lokacin da ta tauna harshenta ba sai zafi taji ga kuma jinin da ya cika mata baki saboda ta tauna harshen sosai.Hassada ga mai rabo taki ce inji hausawa.
muna tafiya muna hirarmu gwanin sha'awa, muka je wajen shopping sai ɗebomin kaya yake ina ce masa ya barsu haka yayi murmushi sannan ya ce" haba hubbi idan ban miki ba wa zai miki? and kuma kinga na daɗe banyi miki ba ko? jiya na samu albashi na ware kuɗin da za'a canja miki kayan ɗaki sannan sauran na siya kayan abinci yanzu kuma sauran sai mu kashesu akayan sanyawa tunda duk sun ƙone ko"?.
na murmusa ina masa godiya, ina tuna yaushe rabon da ya siyamin riga ɗaya da sunan ya siyomin, to yaushe ne ma na samu kan mijin? mijin da baya ta tawa kullum sai yawon bin mata? tunawa da wannan sai ya sanyamin wani irin ɓacin rai, nan da nan naji kamar yaudarata Ahmad xai yi bai daina neman matan ba kamar yadda yayi min alƙawari.
Tunowa da hadisin nan na manzon Allah (S.A.W) wanda yake cewa WALATAJASSU kada ku yawaita bincike,sai ya sanyani saurin mantawa da batun da zuciyata ta kawomin nayi fatali dashi gamida ajjesa a ɓangaren hagu.
muna cikin siyayyar ne na nemi Ahmad na rasa, gabana ya shiga faÉ—uwa na yi saurin kallon inda ya tsaya amman babu shi babu labarinsa, cike da tsoro na ajje kayan dana fara dubawa na shiga yawon nemansa atafkeken wajen me cike da walainiyar fitilu irin na zamani.
da sauri Ahmad ya dakatar da ita gamida kiran sunan, tayi saurin jiyowa tana kallonsa ta cire niƙab ɗin dake fuskarta ta kyalkyale da dariya, Ahmad ya tsaya yana kallonta da mamaki ya buɗe baki zai mata magana kawai sai yi saurin dakatar da shi, gamida haɗe fuskarta tamkar dai ba ita ce take dariya ba ta ce" Ahmad kenan, mijin Rabiatul Adawiyya matar malam badamasi wato ka ɗauka zaka gujemin ne? ai duk inda kake Ahmad ina nan maƙale da kai, kiran da nayi maka awaya rannan dafatan dai baka manta dashi ba, domin kuwa zuwa zanyi gidanka in tare sai na haife cikin da kayi min, sannan in damƙawa matar son naka Rabiatu ta riƙesa, domin ba zaku sha banza daka kai har ita ba wato kaje ka shirya da matarka, saboda ni ka shirya wulaƙantani ko? to kuyi asannu daka kai har ita saboda kai kasan nasan komi na sirrinku, kuma zan iya tonasa kowa ya sani kai bama iya Nigeria ba duk duniya sai na watsa sa wallahi".
ta faÉ—i hakan tana turo cikinta gaba wanda tuni ya fara fitowa kana ganinsa ta cikin abayar da ta sanya.
hannunta ya riƙo da sauri, suka shiga wani ɗan ɗaki domin yasan matarsa zata iya fitowa nemansa yana riƙe da hannunta bai saki ba, ta janye hannunta tare da yi masa wani wulaƙantaccen kallo sanman ta ce" Ahmad kenan wato kana tsoron matarka ko? to ka sani ko ka yarda ko kar ka yarda wallahi agidanka zan haife wannan cikin".
ta nuna cikin tana ƙara kallonsa da mugun kallo.
Sosai ya zaro ido don jin abinda ta faÉ—a, cike da rarrashi ya ce" haba Ajla me yasa kike son tada zaune tsaye ne? ni fa wallahi ba wai bana son ki bane, ki yarda dani dake na saba kuma dake na rayu kibi komi asannu sannan don Allah ki zubar da cikin nan".
wani wulaƙantaccen kallo tayi masa sannan tayi wata irin shewa da hannunta tana gyara mayafin abayarta ta ce" amman ban taɓa sanin mugun ɗan rainin wayo bane sai yau, ni zaka kalla kace in zubar da ciki? nayi maka kama da irin banzayen matan daka saba harka dasu kana zubar musu da ciki? to buɗe kunnenka ka ji ni? ni Ajla Mas'ud Tafida ba irin waɗannan kucakan matan bane, gaba da gabanta aljani ya taka wuta ka shirya karɓata ako da yaushe".
tana faɗar hakan ta fice ba tare dako waiwayansa ta ƙara yi ba.
Ji yayi tamkar ya janyo ta ya shaƙe ta, amman sai ya tuna aƙwai CC camera komi zai iya faruwa shiyasa yayi wata muguwar ƙwafa ya fito, yayi sharkaf da gumi to mara gaskiya ko aruwa yake ai sai yayi gumi.
yana fitowa kuwa mukayi kiciɓus abakin ƙofar ɗakin, Ina riƙe da Khadija wacce take ta miƙo masa hannu amman bai kula taba sai ma gaba da yayi jikinsa duk gumi tamkar wanda aka tsoma sa aruwa.
kallon mamaki na bisa dashi, sai dai bance komi ba na bisa don indai yana cikin wani hali ban fiya tsaurara masa tambayoyi ba? barinsa nake har sai ya nutsu tukunna, daman kuma haka duk wata mar'atussaliha take aduk sanda taga mijinta cikin wani hali ki san ta yadda zaki biyo masa ba wai ki ishesa da tambayoyi ba, garin tambayar wani ma sai ya zageki.
na bisa tamkar zare da abawa, yaje ya biya kuɗin kayan ƙarshe ma dai ni ce na riƙo kayan duk yawansu, ga kuma Nana ahannuna wacce ke ta ƴan koke kokenta saboda rashin ɗaukarta da uncle ɗinta yayi.