← Book details Facala Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 21

Sashe 11

Facala Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mlm ya kira Ammi, tana kuka ta ce" Mlm awani hali Æ´a ta take ciki? me kuma ya ke faruwa ahalin yanzu? na yi shiru ne saboda kada inzo kuma gaka kana nan, nasan zakayi duk abinda ya dace".
Mlm ya ce" ƙwarai kuwa, sai dai nima nawa addu'ah ce amman Allah subhanahu wata'ala shi ne ya fitar da ƴarmu daga cikin matsala ta farko da ta fuskanta".

Nan ya faÉ—awa Ammi duk abinda ya faru, ai kuwa ta fashe da kuka ta ce" duk wanda ya ke bin Æ´ata da wannan mummunan sharrin Allah ya yimin maganinsa".

Mlm ya amsa da "amin mar'atussaliha".
Ammi ta ce" nima zanzo idan ka bani dama, sai kuma ayi bincike kan É—ayan sharrin da akayi mata".
Mlm ya ce" a'a ba sai kinxo ba, komi zai warware da izinin rabbi ke dai kawai ki duƙufa da yi mata addu'ah Allah ya fitar da ita".
Amin ta ce" amin yanzu ma akan sallaya nake".
Mlm ya ce" to ya yi zan kiraki duk yadda ake ciki sai kiji Allah dai ya wanke mana ita tas".
ta amsa da "amin ".
Sannan ya ajje wayar.

ya Ahmad sai kallona ya ke, cike da son keɓewa dani don yin magana amman ya kasa hakan saboda su Mlm dake wajen har muka baro asibitin.
Muna fitowa dr Na'im ya faɗa ɗakin dr Khalid, ya cukomo sa gamida ce wa" miye ka aikata haka ne? me kake son jama'ah suce gamida wannan babban abin kunyar daka aikata? waye kuma ya sanya ka yin wannan aikin? don ni dai nasan ba zaka taɓa aikata hakan bisa kuskure ba, sai bisa son zuciya da kuma son duniya irin na ka".
Dr khalid, ya yi saurin zama akan kujerarsa me jujjuyawa irin ta likitoci sannan ya ce" ni kai na na rasa me yasa na aikata abinda na aikata ɗin, amman wallahi ba ason raina na aikata hakan ba maryam ce ta takuramin akan sai na siya mata sarƙar gold, ni kuma ahalin yanzu ta rashin lafiyar Inna nake, tunda kasan yanayin ciwonta na hanta so shiyasa aduk wata kuɗin baya isa ta, ga kuma agefe ɗaya maryam ta takuramin".
cike da haushin abinda yasa ya aikata hakan ya ce" ni fa babu ruwana da wata maganar sarƙa, ai son zuciyarka shi zaisa matarka ta kaika wuta, to in banda son zuciyarka ta yaya za'ayi ka dinga biyewa mace don son zuciyarta? wannan babban kuskure ka aikata, sannan ni har yanzu baka faɗamin wanda ya sanyaka aikata hakan ba"?.
Gumi ya shiga karyo masa...................soon➡️

HANYOYIN GYARAN JIKI DA FUSKA

Hanya ta farko kayan Hadi:

♦ Extra virgin olive oil (man zaitun na asali)
♦ Lemun tsami
♦ Ruwan zafi
♦ Auduga
Da farko zaki dangawlo man zaitun da auduga ki goga a fuskarki. Ki samu ruwan zafi ki matsa lemun tsami a ciki sai ki jefa bawon a cikin ruwan zafin. Ki sa kwanon ko bahon da kika zuba ruwan zafin a kasan fuskarki ki sunkuyar da kanki sai ki rufu da zani.

Ki samu abun juyawa kina juya ruwan zafin tiririn yana bugar fuskanki.

Zakiji kin fara hada gumi, kiyi haka kaman na min biyar Sai ki samu auduga ki goge fuskarki da ita, zakiga datti a jikin audugar. Zakiyi mamakin irin dattin da zaki gani Idan ruwan ya huce sai ki wanke fuskarki da shi.

Hanya ta biyu:

kayan hadi:

♦ kwai

♦ xuma

♦ yoghurt.

ki sami kwanki danye ki fasa ki cire yellow din,da farin ruwan xa kiyi amfani, sannan ki xuba xuma cokali daya a kan ruwan kwai guda daya ki saka yoghurt ki juya sosai, sai ki shafa a fuskarki, sannan ki turara fuskar da ruwan xafi ko da garwashi xuwa minti goma, idan kin gama saiki bar shi ya bushe xuwa rabin awa, sannan ki wanke fuskar taki, fuskarki xatayi kyau sosai.

Hanya ta uku

Kayan hadi

Yadda za ki yi amfani dasu: â–º Ki wanke fuskarki da sabulun wanke fuska, sannan sai ki

♦ Dilke (Facial scrub)
♦ Tawul
♦ Man shafawa (moisturizer)
♦ Zuma
♦ Kurkum
♦ Madara
♦ Lemon tsami
♦ Man essential oil ko zaitun
♦ Ruwan rose (rose water)
wanke da ruwan sanyi. â–º Ki shafa dilke a fuskarki ta hanyar amfanin da tafin hannunki har na tsawon minti 2 kafin ki wanke da ruwan dumi. â–º Ki turara fuskarki da ruwan zafi na tsawo minti 5 bayan kin diga man zaitun ko man essential oil a cikin ruwan. Yin hakan zai cire miki bakaken kurajen fuska.

â–º Sai ki hada madara da lemon tsami da zuma da ruwan rose water da kurkum kafin ki shafa a fuskarki har zuwa wuya. Daga nan ki bari na tsawon minti sha biyar ko ashirin kafin ki wanke da ruwan dumi. â–º Daga nan ki goge da tawul kafin ki shafa man shafawa (moisturizer). â–º Ana so ki dinga yin hakan sau daya a sati domin samun fuska mai sheki kuma marar kuraje.

MRS GREEN CE.
[2/26, 6:54 PM] Ummu Maher Ce: _*❤️F𝘼C𝘼L𝘼 ❤️*_
{{}}Ta fi kishiya🔥{{}}

TAKU NA 2 (Book 2)

_BY_
_*©UMMU M𝘼HER(MRS GREEN)*_💚

*_AREWA WRITER'S ASSOCIATION✍️_*

*AREWABOOK$✍️*
FACALA:: https://arewabooks.com/book?id=6582a28d4ede3c5852b6cb60

*UMMU MAHER COLLECTION👛👠*
https://chat.whatsapp.com/EBmNeSHdAl9EgqmlWo3Z3C

*_SABAYA KAYAN MATA🥰_*
ko kunsan sabaya na gyara jiki🗣️ta ciko miki da ni',imarki a matsayinki na ƴa mace🗣️in har kika rasa ni'ima to tabbas kin zama saura🗣️🗣️na ce ba? kin haihu kinƙi ki koma dai dai? to wallahi ga sabaya zata gyaraki ciki da waje,ta matseki ta dawo miki da martabarki,ita sabaya bata cutarwa ko kaɗan sabida ƴaƴan itatuwa ce herberls.tana ciko da mama yayi kyau sosai.
08067329607.

➡️9
.............dr khalid ya ce" wallahi dr na'im na rasa me yasa Salma ke son takurawa rayuwata, a kullum cikin damuna take akan dole sai nayi mata abu ko da kuwa banda halin hakan, yanzu idan kajr gidana babu abinda babu amman ta dinga ƙorafi kenan, ita baya san wannan bata san wannan, ni kuma ina gudun ɓacin ranta don ko buƙatuwa zanyi da ita dai tace wai dole sai na bata kuɗi, ni kuma gashi ina matuƙar samun nutsuwa da ita,shiyasa duk abinda ta buƙata nake saurin yi mata shi".

Dr na'im ya ƙura masa ido, cike da takaicinsa ya ce" gaskiya ka bani mamaki wallahi, taga kana zulamartane shiyasa take gasa maka aya ahannu, yanzu tsabar rashin imani irin na wasu matan don mijinki zai buƙace ki har sai ya biya ki kuɗi? saboda tsabar rashin tsoron Allah? to wallahi ina me ja maka kunne tun wuri gwara ka yiwa kanka ƙiyamal laili, idan ba haka ba ta kanta wuta kaima ta kai ka".
Sosai jikinsa yayi sanyi, ya ce" in sha Allah bazan ƙara maimaita kuskuren danayi abaya ba, kuma don Allah ka rufamin asiri kada wani yaji wannan babban saƙon dana aikata, bansan da wani irin ido zan kalli waɗanda suka yarda dani ba, suke ganina amutumin arziƙi ashe ba haka bane, mutum ne ni me son zuciya in sha Allah zanje har gida don in nemi yafiyar waɗannan bayin Allahn".
dr na'im ya ce" good mutumina, na gode daka ganeni da wuri Allah ubangiji ya shiryar damu baki É—aya,maganar matarka kuma kai kasan yadda za kayi mata, don ta gane dukkanin kuskuren da tayi maka".

ya É—an murmusa don yasan ta inda zai gano lagon mutuniyar tasa, ya É—an juya kan kujerarsa zai yi maganinta dai dai abinda ta daÉ—e tana aikata masa na rashin tsoron Allah.

Sukayi sallama kowa ya koma kan bakin aikinsa.

*** *** ***
cike da takun nan nasa me matuƙar tafiya da zuciyar ƴammata ya ƙarasa kusa da ita, ba zai ce yana ƙin jininsa ba ko
babu komi Amira ƴar uwarsa ce, saboda haka zai kula da ita bisa amana amman ba zai iya ɗaukar wasu alƙwarurrukan daya san ba zai iya cikawa ba, ciki kuwa harda ƙwana ɗakinta ba zai iya hakan ba don ko da ya ƙwanta ma ba zai taɓa ganinta amatsayin mace ba, shi dai macen nan guda ɗaya tak da ta tsaya azuciyarsa ba xata taɓa ficewa ba.

ajje mata ledar daya shigo da ita ya yi, sannan ya ce" ni zan wuce sai da safe". ya faɗi hakan agajarce yana me miƙewa zuwa babban ɗakinsa wanda ya gaji da haɗuwa, yaji komi na ado na more rayuwa kai tsaye ya yi wanka sannan ya yi alwala gamida zuwa kan sabuwar kyakkyawar sallayarsa, sannan ya dinga addu'o'i gamida karatun alqur'ani me girma, sannan ya ƙwanta ya yi nisa cikin tunaninsa har ya tafi tunanin wani labarin daya shuɗe fiye da shekara biyu.

TUNANI
Sosai ya shagala da kallonta, har abokinsa ya fuskanci haka ya ƙwace laptop ɗinsa daga hannunsa, yana me saukowa daga kan gadon ya ce" wai miye haka ne canal? ka sanya yarinya agaba kana kallonta? ƙanwata ce"?.
Canal A ya ce" eh nasan ƙanwar taka ce a'i, shiyasa ma na ƙurawa wannan kyakkyawar fuskartata ido, gani nake tamkar ba zan iya dena kallonta ba, gaskiya wannan ƙanwar taka ta tafi dani".
Captain ya ce" uhm kai dai abinka har mamaki ya ke bani wallahi, mutumin da ko kallon mata baya yi? Amman yau shi ne da kallon wannan ƴar ta tsitsiyar yarinyar? dako ƙirgen dangi bata gama ba?".
bai ce dashi komi ba, har sai daya tashi sannan ya ce" uhm ai ko ƙirgen meye ni dai ahaka na ganta nace inaso, sannan ni awaje na ai tafi waɗannan banzan karuwan da suke cikawa mutum gida, da sunan sunxo tayaka hira".

Captain ya ce" oho dai ni bani nace suzo ba ai,amman duk wacce tazo ga waje nan idan da halima ko ƙwana za tayi ni bazan hanata ba, ai baƙonka annabinka".
Chapter 11 · 0% Book details