← Book details Facala Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 21

Sashe 12

Facala Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

haushi maganarsa ta bashi sannan ya ce" inason dai ka sani kai musulmi ne, sannan duk wanda ya ke neman mata zina kenan ya ke yi, sannan kafi kowa sanin irin azabar da za'a yi musu, tunda ka karanta ka gani sannan ina guje maka ranar nadama, ita zina ba abune me kyau ba idan ka kalleta ta fuskar lafiya ma, zai iya yiwuwa wata acikin waÉ—anda kakr neman su zamo masu cuta me karya garkuwar jiki, to kaga komi zai iya faruwa da kai".
da sauri ya katse sa da ce wa" Allah ya tsare ni, ni dai nasan irin waÉ—anda nake nema ai, insha Allah babu wacce zata shafamin wata cuta bi'izinillah".

suka shirya don fita aiki, captain sai tsokanarsa ya ke, wai na Ajla bada kanka asare kaje gida kace ya faÉ—i, shi dai bai ce dashi komi ba kuma dama baiyi tunanin za a amsa masa É—in ba, don yasan halin mutuminsa da mugun miskilanci irin na su na gadon sarauta.

Suna fitowa kuwa sukaci karo da Ajla abakin ƙofar ɓangarensu, da sauri ta matsa cike da tsoronsa ta koma ɓangaren captain tana gaidashi, gamida miƙo masa wani babban flask na abinci ta ce" sir daman abinci na kawo muku".
Captain ya yi saurin amsa gamida ce wa" godiya muke Ajla ke dai bakya gajiya ko"?.
ta ɗan sunkuyar da kanta alamar kunya tana ɗan sosa ƙeyarta.
Ta kalli mutumin na ta wanda tuni ya shige motarsa, bai ƙara ko da kallon inda take ba balle ya san da wata aba mutum awajen.

Ire iren wannan wulaƙancin yasha yi mata, amman na yau yafi damunta ko kallon inda ma take baiyi ba sai ma ƙoƙarin pretending ya ke, kamar ma bai san tana yi ba, haushin abin ya sanyata daburcewa gashi kuma wani iri ƙwarjininsa ke mata, shiyasa ta juya da sauri don ba kallonsa ɗin ba, ƙwarjinine dashi na musamman.

yana shiga motarsa ya dinga mannawa captain hon, ya taho yana mita yana ce wa" haba Canal, akawo mana wannan betar sannan kai kuma bakayi godiya ba, ni sai ka hanani? ai sai mu maida alkhairi da alkhairi".
Banza ya yi masa ba tare daya ce komi ba, shi haushima captain ɗin ya ke basa don sam arayuwarsa baya son zama da mutum me nacin tsiya, ya fuskanci matuƙar ya ce zai cigaba da zama agidansa komi ma zai iya faruwa, gidan da ake kawo karuwai? amman saboda wani babban abu yasa ya haƙura ya ke zaune dashi ba don ransa yaso ba, idan ma yaso a wannan garin aƙwai gidajensa da yawa zai iya zuwa ɗaya ya zauna, amman saboda wani dalili dashi kansa ya barwa kansa sani yasa ya barwa zuciyarsa ya haƙura ya ke zaune da captain.

Suna cikin tafiya Canal A, ya ce" arayuwata na kasance me tsananin kamun kai, na kasance me ɗauke idona daga dukkanin matar daba tawa ba, ban taɓa jin son wata ƴa mace ba sai akan wannan ƙanwar taka captain, ta riga da ta gama dani tun a kallon farko".
Captain ya ce"uhm ai kuwa wannan da kake ganinta nan da shekara goma ma ba lallai ne a aurar da ita ba, kawai dai abinda zan faɗa maka shi ne kayi haƙuri wannan da kake ganinta tafi ƙarfinka, sai dai ka nemo wata".
Yayi masa wani kallo sannan ya ce" uhm ina jinka? kace wai tafi ƙarfina ko? saboda ba nida abinda zan roƙa awajenka kayi min? shiyasa don na nuna inason ƙamwarka kake min wannan abin"?.

Captain ya ce" ai ni awaje na kafi ƙarfin ka roƙeni wani abu na hanaka, sai dai idan har banda iko akan wannan abin, saboda haka ka bar wannan maganar kawai daga baya ma yi ta".

Bai sake magana ba shima, saboda captain ɗin ya fara bashi haushi idan ba don kada ma ya yi wani saɓo ba da sai ya ce ko shi ne yake son ƙanwar tasa, shiyasa ya ke ɓoye masa hakan to amman tuno da wani abu yasa ya kori sheɗan, don yasan wa baya taɓa son ƙanwarsa.

wani aiki sukayi awani ƙauye, da ƴan sansanin gudun hijara suke don basu gudummawar abinci, sosai Canal ya tausaya musu don gasu nan da ƴaƴansu da jikokinsu, wasunsu ma an kashe musu ƴan uwa wasu kuma an kashe musu mazajensu, duk dai abin ba daɗi sai dai Allah ya kawo mana ƙarshen ƴan tada ƙayar baya aduk inda suke, idan kuma masu shiryuwa ne Allah ya shiryar dasu.

sai yamma liƙis sannan suka dawo cikin quater's ɗinsu, captain ya gaji sosai ya ƙwanta kan kujera tree seater sannan ya ce" kai gaskiya na gaji wallahi, ace yadda na gaji ɗinnan in samu wata ƴar girl ta tayani hutawa".
Banza yayi masa, gamida wucewa kitchen ya haɗa tea sannan ya soya ƙwai guda biyu, ya dawo falo ya zauna yana cin abinsa amman hankalinsa duk yana can wajen da sukaje yanzu wajen ƴan sansanin gudun hijira, yanzu wa zai basu irin wannan abincin da ya ke ci, wancan abincin ma da suka kai musu su suka haɗa kuɗi don kai musu wannan tagomashin, ba don gwamnati bata yi musu ba, a'a tayi musu dai dai gwargwado amman ba kalar abincin da suke so ba kuma ba wani isar su ze yi ba.

yana cikin wannan tunanin ya jiyo mutumin na sa yana ce wa" mutumina gaskiya rayuwarka tana burgeni sosai, yanzu ko aure kayi matarka ta huta da dafa maka abinci tunda naga kai babu abinda baka iya ba, ga shi kuma ko ba a faÉ—amin ba nasan daga babban gida ka fito, saboda yadda kake tafiyar da rayuwarka sai naga kamar ma kai É—an sarauta ne, saboda ana ganinka an san daga gidan sarauta ka fito saboda komi naka da wannan shirun naka irin na su ne".
Banza yayi masa, sai ga captain ya sako hannu yana kurɓar ruwan tea, yana wayancewa da ce wa" oh gaskiya kaji daɗinka wallahi, irin wannan girki haka tunda nake ban taɓa cin suyar ƙwai irin wannan ba".
Tun bai yi niyyar yin magana ba har da ya ce" to naji kai me ya hanaka iya wa? naga dai nima namiji ne kuma iyayena duk suna sona, kai ma kuma haka to me ya hanaka koya É—in"?.
Captain ya ce" uhm kai dai ayi sha'ani wai ɗan birni ya cuci na ƙauye, kasan wanene ni kuwa agidanmu? ɗan gatan Hajiya kenan ake faɗa maka, don wallahi ko da wasa bata bari taga raina ya ɓaci, gashi kuma ina da ƙannai mata su suke min komi ni dai babu abinda na iya sai barci, idan naje hutu kuwa kar kaso kaga yadda Hajiyata ke mini, tamkar ita kaɗai ce ta haifeni".

ya É—an murmusa, yana son bashi asalin labarin waye shi? kuma yana tunanin faÉ—a masa, saboda sam baya son duk inda yaje asan waye shi, don yafi son ko mi zakayi masa ka yi masa domin Allah, ba don kuÉ—insa ko don mulki ba amman yana son faÉ—a masa waye shi É—in ko zai sa captain É—in ya dawo sai ti.

ya buɗe ƙasaitaccen bakinsa ya ce............soon
[2/26, 6:54 PM] Ummu Maher Ce: _*❤️F𝘼C𝘼L𝘼 ❤️*_
{{}}Ta fi kishiya🔥{{}}

TAKU NA 2 (Book 2)

_BY_
_*©UMMU M𝘼HER(MRS GREEN)*_💚

*_AREWA WRITER'S ASSOCIATION✍️_*

*AREWABOOK$✍️*
FACALA:: https://arewabooks.com/book?id=6582a28d4ede3c5852b6cb60

*UMMU MAHER COLLECTION👛👠*
https://chat.whatsapp.com/EBmNeSHdAl9EgqmlWo3Z3C

*_SABAYA KAYAN MATA🥰_*
ko kunsan sabaya na gyara jiki🗣️ta ciko miki da ni',imarki a matsayinki na ƴa mace🗣️in har kika rasa ni'ima to tabbas kin zama saura🗣️🗣️na ce ba? kin haihu kinƙi ki koma dai dai? to wallahi ga sabaya zata gyaraki ciki da waje,ta matseki ta dawo miki da martabarki,ita sabaya bata cutarwa ko kaɗan sabida ƴaƴan itatuwa ce herberls.tana ciko da mama yayi kyau sosai.
08067329607.

➡️10
. .......captain ni ɗinnan da kake ganina ɗawisu ne awajen iyayensa, suna sona tare da tattalina da kuma nunamin yadda zanyi rayuwa me kyau anan gaba, ni ɗinnan ni kaɗai ne namiji awajen mahaifina haka ma ɓangaren mahaifiya, duk nine ja gaba agidanmu sai dai wannan ƙaunar da suke nuna min bai sanyani na canja hanya daga layin da suka ajje ni ba, babu aikin da bana taya mahaifiyata ni da ita tamkar wa da ƙani muku, haka ma da mahaifina wanda ya kawo ni duniya, saboda haka don iyayenka sun shagwaɓa ka ba abune da zai amfanemu ba daga mu har iyayen namu, sai dai ma hakan ya kawo mana wata tawaya ta rayuwa, don ni ɗinnan duk inda naje zan zamo abin ƙwatance ba wai yabon kai ba, sannan abu na gaba da zan faɗa maka ni ɗinnan ni ne Yarima me jiran gado, na babbar masarautar da kowa ya santa, indai har mutum aƙasarmu nigeria ya ke, har ma da wasu ƙasashen."

da sauri captain ya ce" daman kai ne Galadima Aliyu me jiran gado? lallai kai É—in mutum ne nagari,maras girman kai wanda ya cancanci yabo gaskiya".

Ya yi murmushi sannan ya ce" meye amfanin girman kan da ba zai amfanemu ba? dukkaninmu zamu mutu, yadda mukazo tsirara haka zamu koma aranar da kowani ɗan uwanka kuma masoyinka zai zubar da hawaye, ranar da zata zo sai yadda aka juya ka zakayi, mutanen dai da kake musu girman kan dasu za'a tashe ka babu kuma yadda za kayi, domin a wannan ranar dukkanin wani girman kanka zai ƙare, kazo babu sutura zaka koma yadda kazo".

Sosai jikin Captain ya yi sanyi, ya ce" haka ne Yarima wallahi sai yanzu ne ka ƙara wayarmin kai sosai, bisa yadda wasu iyayen suke shagwaɓa ƴaƴansu da sunan soyayya ƙarshe sai kaga yaran sun lalace, domin daman ance kaso naka duniya taƙishi ka ƙi naka duniya ta so shi".

Haka dai suka cigaba da hirarsu, wanda duk hirar tasu akan duniya ce dama duk ɓarnar dake cikinta.
Sosai jikin Captain ya yi sanyi har ya ɗan fara hawaye sannan ya ce" tabbas zama da kai alkhairi ne, don kuwa ba don kai ba da babu abinda zai sa in dena halina na neman mata, saboda haka ni ayanzu ma bazan ƙara kallon wata mace da sunan sha'awa ba, har sai wanda na aura".
Chapter 12 · 0% Book details