← Book details Facala Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 21

Sashe 21

Facala Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sam kallon Adawiyya yake mata, har ya fara zaucewa ya manta da wacce ya ke tare da ita har ya me afkuwa ta afku daman gashi yana mata kallon Adawiyya masoyiyarsa a wannan daren ne Hafsa ta zama cikakkiyar matar aure tamkar yadda kowacce mace me lasisi take zaune agidanta na sunnah.

wani irin kukan takaici take, ga kuma wata irin azabar da take ji ta kasa banbance wani irin kuka za tayi, na baƙin cikin kalamansa na ɗazu ko na wannan cin mutuncin da yayi mata? duk ta yadda zata fasalta wacece wannan muguwar Adawiyyar da ta juyawa mijinta ƙwaƙwalwa ta kasa, da zata ga wannan shaiɗaniyar Adawiyyan da babh shakka sai anyi kare jini biri jini da ita......

oh su Hafsa kishi lol😅

shi kuwa da ya dawo cikin nutsuwarsa ya gane me ya aikata kasa zama yayi aɗakin, ya wuce zuwa ɗayan ɗakin nasa tamkar yayi kuka tsabar baƙin ciki, shikkenan wannan yarinyar ta gama ƙare masa kallo ta rainasa.

Autar momma kuwa da ta gaji da jira sai ta tashi ta wuce ɓangarensu da niyyar an jima ta dawo.

OH SU AUTA GULMA FON SUTO😒😅
[2/26, 6:54 PM] Ummu Maher Ce: ➡️20

................bayan mun dawo gida kai tsaye ɓangarena na koma, ga tunanin halin da mijina ya ke ciki domin haryanzu bai farfaɗo ba ga kuma rasuwar Nana, ni da kaina jikina duk ciwo yake haka saitin zuciyata tamkar an ajje min wani ƙaton malulu, banda ma Ammi na tausar zuciyata da bansan halin da zan shiga ba.

Bayan an kai Nana ina ƙwance kan cinyar Ammi, sai ga Hajiyarsu ya Ahmad ta shigo gabana yana dukan uku uku na ɗago da kaina wanda yake masifar saramin na buɗe bakina da niyyar yi mata sannu da zuwa........ ko kafin inyi magana tayi caraf ta ce"to ɗiyar mayu, kinxo kin cika mana gida babu ciki balle haihuwa shiyasa kike son cinyemin jikoki ko? to wallahi bari Ahmad ya farfaɗo, ko kina so ko bakiso sai kin bar gidan nan domin kaf zuri'ar gidanmu babu maye".

Ammi ta tashi tsaye cike da mamaki ta ce" yanzu don Allah bakiji kunyar kalamanki ba? kun kasa yarda da ƙaddara akan abinda ya faru sai kace ba musulmai ba? alhali kunsan Allah shi kaɗai yake da alhakin ɗaukar ran kowa? kuma ɗanki yana gadon asibiti bakiji tausayin halin da yake ciki ba har kike faɗar duk abinda yazo bakinki? to wallahi ki jira ranar da xata zo Allah ya tambayeki dalilinki na faɗar hakan".

Mama uwar gida dake wajen ta ƙwaɓe fuska sannan ta ce", yo ai wannan duk borin kunya ne an kashe yarinya har lahira kuma adinga wani batu, yo ai daman ba tun yau aka fara ba daman hausawa sunce rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya tak ta me kaya, gashi yau kunyi maitar taku inda ba xa'a barku ba".
Umma tayi saurin tashi tsaye itama daga zaunen da take ta ce" wai wannan wani irin hali ne domin Allah? kun sanya yarinya agaba kuna zagi kuna ce mata mayya, ke Mama uwar gida har dake ake faɗar wannan batu? to in har Adawiyya mayyace ai ƴaƴanki ma duk mayu ne, tunda duk wanda ya ganta yasan ƴar gidan Malam ce saboda haka kika ƙara cewa tak awannan batun wallahi sai na shaidawa malam cin mutuncin ƴarsa da kike yi".

Hajiyar Ahmad ta ce" ke don Allah sauran mayu, har kina da bakin magana? tunda an gama dake an bada kuruwarki? ai dole kiyi magana tunda ke ayanzu gawa tafe ce".

Nan da nan waje ya hargitse, can sai ga Balaraba da muƙarrabanta sun iso, sai zage zage suke suna rashin mutunci, Balaraba kuwa ta zama tamkar mahaukaciya domin ganin yadda aka gyaramin sashe na, sai taji dama bata yi abinda tayi ɗin sashena ya ƙone ba, domin har ya tattaka da haɗuwa kujeruna saiti biyu danƙara danƙara, masu kalar orange da fari labulayen ma duk farare, waɗanda suka sha ado na kece raini ga kafceciyar tibin bango, ga danƙareren stand firiza wanda ya gaji da haɗuwa fari sol dashi komi dai na falon ya tsaru sosai, nima abinda yasa ban lura da komi ba saboda tashin hankalin dana ke ciki ne, ni dana lura ma sai naga har nafi Balaraba shiga tashin hankali, domin ni ko magana bana yi ita kuwa sai haƙilo take tana masifa domin wata masifar ma dama ta baka, in har da gaske kana cikin wani yanayi maganar ma wahala take maka.

ɗaki Ammi ta tura ni, itama ta shiga ɗakin sannan ta sanya mukulli, ɗakin ma ya sanyamin kayan ɗaki masu matuƙar kyau da ƙawa farare tas tas gwanin ban sha'awa masu adon golden da ash ɗin labulaye masu kyau.

Sai kuka nake akan cinyar Ammi, ita kuwa haƙuri take bani tana tofamin ayoyin ƙur'ani da kuma tofamin duk addu'ar da tazo bakinta, nan da nan sai wani wahallan barci yayi awon gaba dani, acikin barcin ne na dinga mafarki da mutumin da muka haɗu ɗazu, yana ta bina ni kuma ina guduwa ga wasu yara ƙyawawa sai bina suke ni kuma ina gudu.

**********
bayan yayi wanka yasha adonsa tamkar babu abinda ya damu zuciyarsa, sai walwali yake yana sheƙi ya fito a asalin angonsa a gaggauce ya shirya ya wuce zuwa wajen Amira, don tunowa da ta'asar daya aikata, yasan yanzu tana cikin wani hali duk da shi kunyar ma zuwa yake sai dai dole ne ya sanyawa idonsa ƙwalli yaje, saboda shi mutum ne me matuƙar tausayi musamman mace da ƙananan yara.

ƙamshi yake busawa me masifar tafiya da zuciya, ya shiga ɗakin na ta cike da rangaji wanda ya zamar masa tamkar jiki kuma hakan sai yake ƙara masa kyau da kuma ƙwarjini.

a takure ya same ta kan kado, tana lulluɓe da blanket me kuliya me masifar tsantsi da kyau ya daɗe tsaye kanta, tausayinta ya tsarga masa gashi babu abinda yaƙi jini irin kukan mace, jin kukan nata yake har ransa ko da baya sonta bai kamata yazo mata ayadda yazo matan ba.

ya ƙarasa bakin gadon sai dai bai zauna ba, ya zube hannayensa acikin aljihun farar jallabiyarsa me matuƙar kyau da sheƙi irin ta asalin larabawa, me irin kaurin nan da gajeren hannunta me kyau.

ya buɗe bakinsa me tsada ya ce" nasan bai kamata in aikata abinda na aikata ɗin ba amman kiyi haƙuri akan abinda nayi miki kuma in sha Allah bazan ƙara taɓa ko da jikinki ba".

maganganunsa sun zo mata da ɗan ƙwarin gwiwa, sai taji ta ƙara sonsa da ƙaunarsa cike da kulawa ya shiga banɗaki ya haɗa mata ruwa me ɗan zafi a jakuzi sannan ya dawo ya kalle ta ya ce" ki daure ki shiga banɗaki ga ruwa can na haɗa miki".

ganin irin tafiyar da take yasa ya ɗauke ta ya sanyata cikin ruwan, daurewa take har ta gama shiga yana ganin zata fara wanka ya fito da sauri ita kuwa ta rintse idonta tana kukan zabar da take ji, ga wani irin bala'in zazzaɓin daya rufeta, ta saki kukan baƙin ciki da iya abinda yayi mata ne ba zata damu ba tunda tasan Allah ne ya halasta masa, to amman sunan macen da yake ambata ne ya ƙona zuciyarta tabbas ko wacece wannan Rabiatun sai ta nemo ta.

yana fitowa kai tsaye ya wuce cikin wani ɓangare agidan, shima dai ɓangarensa ne saboda haka ba shida shamaki awannan sashen baki ɗaya falon hotunan Rabiatu ne, wasu tana barci wasu kuma tana zaune tana cin abinci, ga fuskar Ahmad ɓaro ɓaro ajikin hoton, takaici ya ishesa ya ƙarasa jikin hoton ya dinga yaga hotunan Ahmad yana tattakawa, wasu zafafan hawaye suna yanko masa shi kaɗai yasan irin azabar daya keji acikin zuciyarsa, yana masifar kishinta baya son kowa ya raɓe ta da sunan soyayya idan ba shiba yana tsananin sonta.

kai tsaye ya wuce fridge ɗinsa da yake ajje kayan shaye shayensa ciki sai yaji an riƙe masa hannu gam, alamar wani ne tsaye akansa.........

****
Sosai yake kallon Fulani mahaifiyar Galadima, ganin irin tashin hankalin da ta shiga daga jin ance za'a haÉ—a aure tsakanin É—anta Galadima da Æ´ar gidan Alhaji Mawashi Æ´ar aminiyarta Hajiya Rabi.

Me martaba ya ce" amman sai naga kin shiga wani hali, ko bakison auren ne"?.

bakinta yana kakkarwa ta ce" ka...ka....ka....kada ayi auren nan aƙwai matsala babba".

ta faÉ—i hakan a É—am tsorace, Me martaba ya tsare ta da idonsa tamkar mikiya yana hango abubuwa da yawa acikinsu.........

*WANNAN SHI NE ƘARSHEN LITTAFI NA BIYU, WATO TAKU NA BIYU SAI MUN HAƊU ATAKU NA UKU WANDA SHINE NA ƘARSHE IN SHA ALLAHU, DUK WACCE TA KARANTA BATA SIYA BA NA BARTA DA ALLAH*.
Chapter 21 · 0% Book details