← Book details Facala Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 21

Sashe 4

Facala Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

➡️3
............tun daga nesa Hj Rabi ta ƙare mata kallo, sannan ta ce"Asabe lafiya kuwa? naga alamar kamar kin yi kuka?".
da sauri ta goge hawayenta sannan ta gama ƙarasowa wajen, ta ce" daman dana shiga ne na samu ashe tana barci bata tashi ba, to shi ne na ce bari in shigo in faɗa miki ko zaki shiga da kanki ne sai ki tashe ta, don ta sanarmin idan tana barci bata son ana tashin ta".

ɗan murmushi tayi wanda hausawa ke cewa yafi kuka ciwo, tasan ƴar gidan nata ƙin fitowa tayi don tasan halin Amrah nesa ba kusa ba, ta wayance ta ce da ɗan gidan sanata" kaga Faisal bari inje da kai na in tashe ta".
da sauri ta tashi tun kafin ma ya yi wata magana. amman aransa mamaki ya ke da har wata mace take juyasa haka kamar wainar masa, amman babu yadda zaiyi burin mahaifinsa zai cika, don tabbas Amrah tana cikin matsala tunda har ta shigo gonar mahafinsa, shi kuma sai yasan duk yadda zaiyi ganin itama ta shiga cikin matsala kamar yadda ta sanyashi, sannan kuma har da mahaifin na tama za a haÉ—a ba ita kaÉ—ai ba.

tana ganin mahaifiyarta ta gimtse fuskarta, gamda juyawa ta cigaba da waya da ƙawarta tana ce wa" yesmin kinga ki fito bakin titi xan zo in ɗaukeki sai mu tafi".
Hj ta tsaya har ta gama wayar sannan ta ce" idan kin gama wayar kixo Faisal yana jiranki, tsabar wulaƙanci ai na aiko Asabe tazo kiranki amman da yake ke bakida kunya har kuka sai da kika sanyata".
wani kallo ta yi mata tamkar dai ba mahaifiyarta ba, sannan ta ɗan ja fasali ta ce a shagwaɓe gamida turo baki" Momeeeeeee ni fa sam banason Faisal ɗinnan, amman naga ke sai takuramin kike akan inje wajensa, so ana aure dole ne? Ni nace bana sonsa bana kuma ƙaunarsa, don Allah momi ki barno in hutawa rayuwata pleaseeeeee".
ta faÉ—i hakan tana me haÉ—a hannunta waje É—aya, sannan ta cigaba da waya da Yasmin.
galla mata harara tayi sannan ta ce" ke wai wacce irin mahaukaciyar yarinya ce ne? ke kullum sai abinda kike so shi za'ayi? To wallahi ki sake in ƙarawa dawowa baki fito ba, ranki zai yi mummunan ɓacin da ko ubanki ɗin da ya ke ɗaure miki gaba bai isa ya hanani hukunci akanki ba".tana faɗar hakan ta fice fuu tamkar ƙububuwa.

tana ganin ta fita, ta juyawarta gami da ɗaukar hand bag ɗinta, ta zura wani pink ɗin glass me shegen kyau da kuma sheƙi, sannan ta feshe jikinta da turaruka masu masifar ƙamshi da kuma jan hankali. tun daga nesa zaka jiyo sautin takunta da ya ke takalmi ne ta sanya me mugun tsini, tana kuma sanye da wani skin tired ɗin wando, wanda ya kamata sosai ga kuma crazy ɗin da akayi masa duk an yanyanka cinyar, fararen cinoyinta tar tar suka fito, rigarta kuma irin rigar nan ce me mugun matsewa, wanda ba don Allah yayo halittarta kamar silindium ba da babu abinda zai hana surar jikinta fitowa, amman da yake irin muguwar siririyar nan ce sai baka ganin komi sai ƙashi, tamkar ba ƴar gidan Alhaji Mawashi ba, me kuɗin da za a iya sanyashi ajerim masu kuɗi a africa baki ɗaya.

kallonta ya ke sosai, yana raya abubuwa da dama akanta, ba mummuna bace ita tana da kyau sosai don gaskiya ba ƙarya ta haɗu amman cikas ɗinta ɗaya, ba tada mutunci ko kaɗan sannan kuma sam bata ɗagawa kowa ƙafa, ciki harda mahaifiyarta domin kafin yazo sai da ya tambayi asalin tarihinta, yarinyar da ta sanya aka saki uwarta axamanin ƙuruciyarta? Ai kuwa ta isa maras mutunci, amman tunda ta shigo gonarsu sai ya dawo da ita tayi mugun laushi tamkar lagwani.bata ko kalli inda ya ke ba tayi niyyar wucewarta, ko faɗan da Hj Rabi tayi mata ma bata san anyi mata ba, ita dai rawar jikinta ta isa ga sahibin zuciyarta wato Galadima, don yau ne akace mata za a gudanar da bikinsa, ko da taji hakan ta shiga mummunan yanayi sosai, don har sai da ta ɗan watsa ƙwayoyin da ta saba sha sannan ta dawo nomal ɗinta.

da sauri Faisal ya tashi ko kunyar Hajiya bai ji ba, yasha gabanta ya yi kalar tausayi sannan ya ce" haba Amra sahibar rai na, don Allah ki tsaya mana ko gaisawa muyi".
idan tace masa tatafar to ci kanka, don ko kallon inda ya ke ma bata yi ba, ta sanya hankalinta gabanta don da bai matsa ba za ta iya bugesa ta wuce, don masifar jin haushinsa take daman ga baƙin cikin da ya ke ranta na Galadima.
da sauri ya matsa don yasan ba kirki ne da ita ba, xa ta iya wucesa har ta wuce ɗin saboda haka ya matsa amman can cikin zuciyarsa ji yake inama yana da dama da ya wulaƙantata agaban mutane.
Sosai ran mahaifiyarta ya ɓaci, har Asabe ta kula da hakan ta ɗan matso kusa da Hj sannan ta ce" Hajiya don Allah kiyi haƙuri, ni bana son kina sanyawa kanki damuwa akan Amrah, addu'arki take buƙata ba kukan nan ba". ta faɗi hakan cike da tausayin halin da take ciki, don tana matuƙar tausayinta don sam ba halinta ɗaya da ƴarta ba, ita mutunce me mugun tausayi da jin ƙan marayu da marasa ƙarfi, albasa ce dai batayi halin ruwa ba amman da ana gado hali da Amrah ta gado halin mahaifiyarta.

jikinsa amatuƙar saɓule ya ce" Hajiya ni zan tafi, amman don Allah aƙara rarrasan mun ita zuwa wani satin zan dawo kafin na wuce mexico".

GyaÉ—a kanta kawai tayi ba tare da tace masa komi ba, don ita kaÉ—ai tasan yadda take jin zuciyarta.
daga baya ma tashi tayi ta wuce ba tare da ta ƙara magana da Asabe ba, don ayanzu kuka take buƙata sannan kuma ta samu gabatar da sallolin da ta sabayi don kaiwa me duka kukanta akan lamarin ɗiyarta, wacce kullum iskancinta da cin zarafin al'umma ke ƙara haɓaka azuciyarta, ba komi yafi ɓata mata rai da halin Amrah ba shi ne ita batasan babba yayi mata magana taji ba, ciki kuwa har da ita kanta mahaifiyarta, sannan abinda ya ke ƙara ɓata mata rai da kuma bata tsoro bai wuce yadda Amrah ke ƙwana awaje ba, don ta kai ta kawo tun tana dawowa shabiyun dare to yanzu sai washe gari take dawowa, abin yana bata mamaki sosai kuma an tabbatar mata daba yawon banza take ba, to ina take zuwa? shi ne abinda ya damarta mata zuciya da ruhinta, sannan ya kasa fita daga zuciyarta.

tana shiga ɗakinta ta ɗauki wayarta ta danna wata lamba, daga can aka amsa mata gaisuwarta sannan ta ce" Amrah ta fita daga gida, inason abita aganomin inda take zuwa". ta ajje wayar tana kuka me ƙarfi don bazata iya riƙe kukan ba, tabbas Alhaji ya cuce ta sosai daya nuna mata komi yayi dai dai ne, sannan ko me za tayi bata isa ta hanata ba wai amatsayin mahaifiyarta kenan, ina ga kuma ba kai ne ka haifeta ba ai sai abinda taga damar yi maka.

tana cikin wannan halin ne taji taku abayanta, tana juyowa taga mahaifiyarta daman duk abinda ake ita tana can tana barcinta wanda takeyinsa duk safe saboda ciwonta na hawan jini.

ahankali ta dafa kafaÉ—ar Æ´artata sannan ta ce"Rabi ki daina sanyawa kanki damuwa, domin damuwar za ta iya jefa ki acikin wata matsala ta daban, kuma kinsan kina da hawan jini saboda haka indai ni na haifeki na baki umarni akan ki cire wannan tunanin, ni aganina babu abinda kika nema kika rasa arayuwarki, kina da uwa kina da Æ´an uwa kina da miji kina da Æ´a, to miye ya dameki haka da har zaki saka shi azuciya"?.
ta faÉ—i hakan tana binta da ido, alamar tana son jin menene É—in?

fashewa ta kumayi da kuka sannan ta ce" na shiga uku na Mama, wannan yarinyar tana son kashe ni ne da raina so take sai ta ƙuntatamin bata jin magana ta, ta raina ni Mama bata jin maganataaaaaaaa".
ta faɗi hakan cike da matsanancin ɓacin rai, da kuma tashin hankali alamar abin yana cin ranta.
rarrashinta ta hau yi sannan ta ce" yi haƙuri Rabi, ita haihuwa jarabta ce, rashinta ma jarabta ce yanzu wani yana can yana kuka ba a basa haihuwar ba an hanashi, ke kuma kina kuka ne akan halin ƴarki, to kinga dukkan biyun nan idan bakayi haƙuri ba sai ka rasa imaninka, saboda haka kiyi haƙuri ki barwa Allah komi sannan ki ƙara tashi tsaye da daddare kina faɗawa Allah dukkanin buƙatunki, musamman ma acikin sujjada, kinsan sallar dare ba tada shamaki tsakaninka da Allah, shiyasa matuƙar kana son a amsa maka addu'o'inka ka kasance kana yawaita sallar dare, nima kuma amatsayina na mahaifiyarki zan tayaki da addu'ah, Rabi ni ɗinnan da kike gani na rasa wani abu mafi soyuwa arayuwata, amman haryanzu Allah baisa abin ya goge a allon ƙaddarata ba, saboda haka kiyi haƙuri komi zai wuce in sha Allah".

*** *** ***
Ammi ta ce" wai meye ya ke faruwa ne? na kasa gane me kake ce wa Ahmad, matar taka ta sunnah ce kake zargi da cikin shege komi? wallahi ƙarya kake ƴata ba zata taɓa yin cikin shege ba, kawai dai kayi haka ne don ka tozartamu kuma kanka ka tozarta, kuma wallahi wannan auren yazo ƙarshe kenan, don wallahi ba zaka kashemin ƴata ba mugu kawai azzalumi".
kashe wayar tayi tana haki, Malam ya kasa hanata abinda tayi niyya ɗin shima hankalinsa duk atashe ya ke, don zai iya rantsewa bai taɓa jin abinda ya girgizasa ba sai yanzu, wannan wacce irin masifa ce? daga wannan sai wannan? ganin Ammi na ta kuka ne yasa ya matsa kusa da ita gamida ce mata, kinga kiyi haƙuri ki dena wannan kukan tashi zakiyi muje can gidan muji duk abinda ke faruwa, don wallahi sam hankalina bai ƙwanta da wannan maganar ba, gwara muje kada wani abin kuma ya ƙara faruwa".
hularsa ya ɗauka ya sanya, Ammi kuma ta sanya zumbulelen hijabinta tana sharar ƙwalla har suka fito waje.
Chapter 4 · 0% Book details