← Book details Facala Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 21

Sashe 15

Facala Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

Riƙo hannunta yayi, ya zaunar da ita kan kujera tree seater sannan ya tsugunna akan capet ɗin dake falon, idanuwansa sukayi jawur alamar abinda tayi ɗin ya ɓata masa rai, ya ce" Balaraba, meye wannan ɗin kike yi? Kina son hana abinda Allah ya halasta atsakaninsu ne? akullum ina faɗa miki kiji tsoron Allah ki daina aikata wannan mugayen abubuwan da kike yi, zato zunubi ne koda ya kasance gaskiya, amman wallahi ni gani nake kina da sa hannu cikin abubuwanda suka faru da wannan yarinyar, sai dai ban gasgata hakan ba amman ni azatona zaki iya aikata abinda ma yafi haka, sanin hali ai yafi sanin asali biyo bayan yadda kika tsani yarinyar mutane, babu gaira babu dalili? ita ba kishiyarki ba ita ba maƙiyiyarki ba? amman duk kinbi kin tsane ta kema kin tsani kanki"?.

da wani irin fushi ta tashi tsaye, ko nauyin cikin dake jikinta ma bata ji ba ta fara magana cike da harzuƙa ta ce" Zubairu ka fita aharkata don Allah, yanzu tsabar kafi sonta shi ne har kake yimin irin waɗannan mugayen kalaman? to wai ni ko sonta kake yi ne?". ta faɗi hakan cike da izgili da tinƙaho da kumfar baki.

da sauri shima ya miƙe, ya tsinka mata wasu lafiyayyun maruka har guda biyu sannan ya ce" wai me yasa ba kida hankali ne? idan banda ba kida hankali matar ƙanin nawa zan so? abisa wani dalili zan aikata hakan? kin ɗauka kowa ma mahaukaci ne irinki? to maza maza kima cire wannan tunanin don Ahmad ko mutuwa yayi ba zan auri iyalinsa ba, saboda haka ki shiga hankalinki ki san irin maganganun da zaki dinga faɗamin domin wutsiyar raƙumi tayi nesa da ƙasa, sannan ruwa ba sa'an ƙwando bane".

ya karkaɗa hannunsa suka bada wani ƙara daya ɗauki action, sannan yayi gaba abinsa yana huci da kuma jin tsanarta azuciyarsa, wallahi don ba shida yadda zai yi ne da ko ƙwana baza tayi agidansa ba, saboda yada ya tsaneta da kuma halinta sam ba tada hali me kyau ko kaɗan ba tada wani alkhairi acikin al'umma.

ya fice zuwa wajensu mlm dake ta hirarsu atsakar gidansu.

Balaraba ta rasa me zatayi saboda tsabar baƙin ciki, kawai sai ta samu wani abu me nauyi ta buga kan center table ɗin dake falon nata na glass ai kuwa nan da nan ya tarwatse ya bada wani irin ƙarar da kowa na gidan sai daya san da zaman ta'asar da ta aikata.

ita kuwa ko ajikinta ta durƙushe awajen tsabad baƙin ciki ta fashe da wani irin wahalallan kuka tana cire ɗan ƙwali tamkar mahauciya ta hau hauka.

Mu kuwa da muka lula duniyar ma'aurata bamu ma san duk wainar da ake toyawa ba, sai da komi ya lafa ya Ahmad ya koma gefe sai naga ya fara juyi yana riƙe marar sa, da mugun tsoron na ƙaraso kusa dashi ina kiran sunansa, tsabar firgita ma sunansa nake kira ina ce wa" Ahmad! Ahmad!! Ahmad!!!.

*** *** ***
washe gari
tun da wuri gwaggwala ta tashi, ta tisa jakadiyarta gaba da kayan breakfast farfesun ɗawisu da ruwa ruwansa wanda yasha kayan ƙamshi irin na tsohon hannu, sannan ta bata wata dafaffiyar madara me bala'in ƙamshi da kuma kauri ta ce akaiwa jikarta Amira.

Jakadiya na zuwa ta hau buga sashen na su, duk da taji haushin rashin buɗe mata da wuri da bata yi ba amman gefe na zuciyarta cike yake da son ganin wani sirri, wanda uwar ɗakinta gwaggwala ta aikota ta gani cike da zaƙuwa ta ƙara taƙarƙarewa tana buga ƙofar sashen Galadima sarki me jiran gado, tuni ta manta wanene Galadima son taga gulma ya rufe mata idanuwa ruf ta dinga bugawa tamkar zata ɓalla ingarmar ƙatuwar ƙofar dako zata ɗakko fatanya tayi ta bugu ko alamar lotsawa ba zatayi ba saboda ƙwarin ƙofar.

kamar daga sama ya fara jiyo wannan bugun, alokacin daya ɗan farka bisa lallausar sallayarsa wacce yayi sallar asubahi, ransa yayi mugun ɓaci don kaf faɗin babbar masarauta babu wanda baisan halinsa na rashin son magana da ƙara ba, ya taso cike da sauri don ganin me shirin jijjige masa ƙofar sashensa daman gate ɗin gidan abuɗe ya ke daya dawo sallar asubahi bai rufe ba, sannan dogarawan da sojin dake bakin sashen nasa duk ya sallamesu su huta zuwa ƙwana biyu, don yana matuƙar tausaya musu ace zafi rana, ruwa sanyi duk suna zaune suna gadi su kuma suna cikin gida ana gadinsu, gaskiya wannan da rashin tausayi ciki shiyasa ya basu hutu don kowa ya huta har sati biyu ba tare da kuma janye musu albashin ko sisin ƙwabo ba.
Shida ya saba ƙwana ajejin Allah, babu kowa babu me gadi ko ɗaya kuma Allah ya kare.

yana buɗewa jakadiya tayi saranda, gamida gwako idanuwa waje kuma ta kasa koda kalmar A, saboda tsabar ƙwarjinin da yaron yake mata don za tayi jika dashi amman wallahi tsoronsa take ji idan ya juye musu, ahakama wai rabin rainonsa yana yaro su sukayi ina ga kuma baka saba dashi ba? ita dai har tausayin yarinyar nan take Amira, don tasan halin mutumin na ta da bala'in miskilanci tamkar mahaifinsa Sarki.................soon➡️
[2/26, 6:54 PM] Ummu Maher Ce: Sirrinmu➡️➡️➡️➡️➡️➡️

*MAGANIN SANYI KO WANI IRI*

Ki samu darbejiya ki dafata, ki juye ta abaho me kyau sannan sai ki ƙara ruwa yayi ɗan ɗumi yadda zaki iya zama, sai ki shiga ciki ki zauna tsawon minti ashirin, kiyi haka na ƙwana 7 in sha Allah zaki rabu da sanyi na mara da sanyi me sanyi ƙaiƙayi ko fitar ruwa......

➡️13
............jikin jakadiya ya hau tsuma, ya juye asalin Galadimansa kuma Canal A, ta hau inda inda tana son yin magana da ƙer ta ce" uhm....uhm...uhm.. dama...dama... Gwaggwala ce ta aikoni ta ce inxo in kawo muku abin karyawa da kuma in duba Banteeeeeeee".

wani duban tsanaki yayi mata, yana sane don ya ƙure ta ya ce" uhum ina jinki? meye kuma Banteeee"??.

ta kasa magana sai muxurai, tana wulkila ido ta ce" eh dama ana dubawa ne ko matar ta kai budurcinta É—akin mijinta kasan mu Æ´an sarauta haka ake mana".

ya yi ɗan murmushi gefen baki, yana tuno da wasu al'amaran da suka shuɗe wanda ƙwaƙwalwa ba zata taɓa gogesu ba tamkar haddacesu yayi, kuma akullum yi masa gizo suke yi.

ya amshi abincin sannan ya ce" to zaki iya komawa don matar gidan bata tsshi ba". jikinta yayi sanyi ƙalau don batasan abinda za ta cewa gwaggwala ba, don tasan halin masifarta idan ta koma ba tare da ta kawo mata komi ba, zata sanya yarinyar acikin matsala ne don cewa za'ayi bata kawo banten ta ba.
Da ire iren waɗannan tunane tunanen ta koma ɓangaren uwar gijiyarta, don bata san masifar da zata sha ba.

Tana shiga kuwa ta ganta zaune kusa da tumtum, tana shan madara me zafi wacce aka kawo mata yanzu daga cikin gida, ta kalli jakadiya da wani duba sannan ta juya bata ce mata uffan ba amman tana gane jakadiya musamman ma idan tana cikin matsala.
ta ƙaraso ahankali duk da kuwa macece me matuƙar kuxari da karainiya, ta zauna kusa da ita ta ce" uwar gijiyata wallahi an sami matsala wannan jikan naki me masifar ƙwarjini shi yazo da kansa ya buɗe ƙofar, wallahi ba kiga yadda ya tsatstsareni da wannan idanuwan nasa masu kama dana mage ya hanani sakat wallahi".

Gwaggwala ta kaÉ—a kai alamar kinyi dai dai, sannan ta ce" to ke da kika dawo zaman mi kike yi anan? Ai kamata yayi kawai ki wuce ba sai kin ce min komi ba, tunda kema kin zama abinda kika zama da har ban isa ince ga yadda za'ayi ba, sai an samu Æ´an hana ruwa gudu sun shiga gaba, yanzu so kike ace jikata bata kawo Banten ta ba? Ko kuwa so kike ace jikina ba namiji bane?".

da sauri Jakadiya ta ce" ni kuma wane ni? Ai kinfi ƙarfin haka awaje na, sannan abinda nakeso dake Uwar ɗaki na kiyi haƙuri mu bishi asannu, kinsan fa maza basa son tonon asiri sannan ƴanda da ƴan yanzu aƙwai babbanci me girma tsakaninmu dasu, saboda haka kada ma wani yaji wannan batun".
Da sauri ta kalle ta sannan ta ce" oh abar ma maganar ko? saboda bata shafeki ba? to anƙi abar maganar ni da kaina zanje har turakar tasu in ganewa idona".

Saura ƙiris Jakadiya ta tuntsire da dariya, ta ɗan buɗe ido na mamaki ta ce" haba uwar ɗaki na, me kuma zaisa kije da kanki gamu? idan kika je yayi miki abinda yayi min fa? Ai kinga munji kunya ko"?.
ta wani yi mata kallon tsaf sannan ta ce" oh wato nufinki nima idan naje zai min abinda yayi miki ko? wallahi yayi min kan uwarsa Fulani zan wuce, ba zanji kunya ba zan faÉ—a mata tunda ita ta kawo nata ta tambayi É—anta dalilin daya sa bai je ga matarsa ba".

jakadiya ta gyaɗa kai, babu damar tace ƙala cibi ya zama ƙari ƙari ya zama ƙababa. saboda haka ta ce" to Allah yasa adace amman ni dai gaskiya kunya nake ji haka kurum yaro ya rainaka kuma girmanka ya faɗi".

Gwaggwala ta gama yana lifayarta da yake asalinta yaren kanuri ce, bata ko kula taba ta fito da kanta da yake da nata ɓangaren dana Galadima ba wani nisa ne dashi ba, bayinta dake ƙofar falonta mata suka biyo ta tayi saurin ɗaga musu hannu da ce wa" ku barshi kawai bana son rakiyar". ta wuce afusace Jakadiya na ɓoye dariyarta, sai da ta wuce ne ta fito da ita fili tayi tayi tana riƙe ciki ta tashi ta shiga kicin don ɗora abincin dare.

tana zuwa ta fara bugu tamkar zata ɓalla ƙofar, haushi ya kama Galadima wanda ke zaune gaban laptop yana vedio call da ɗansa, don tun ranar da sukaje da Aamiru bai kuma komawa ba saboda wasu dalilai da dama, amman son ɗansa yana nan binne azuciyarsa, yana yi masa wani irin masifar so me wuyar fassaruwa, ya kasance baya samun nutsuwa indai bai kalli fuskar yaron ba, fuskar mahaifiyar Siraɗillahi ya ke gani afuskarsa da yake sunan daya raɗawa ɗansa kenan wato SIRAƊILLAH.
Chapter 15 · 0% Book details