← Book details Facala Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 21

Sashe 2

Facala Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

duk alokaci ɗaya ta yimin wannan tambayar? Na sunkuyar da kaina ƙasa na ce" ba komai Anty".
bayan na shiga motar ta ce" haba Adawiyya ya zakice min wai ba komi? bayan ko kina gidanku ba haka kike ba, balle yanzu da kikayi aure don ni rabona dake tun ranar bikinki, kuma tun lokacin ni bana ƙasar ma baki ɗaya ina Turkey ne an ɗaukemu wani aikin, domin naso ace lokacin ma kina free ba kida aure da mun tafi tare don nasan su Ammi ba zasu hana ba don sunyi matuƙar yarda dani".

kasa faÉ—a mata matsalar dana ke ciki saboda ko daman can ina da zurfin ciki sosai.
duk tambayar duniya naƙi faɗa mata, ko da zamu rabu 10k ta ɗakko ta bani tamkar daman ta ɗakko ɗinne saboda ni, na yi mata godiya sosai itama ta bani lambar da take amfani da ita tace zata kirani,na yi mata godiya sosai sannan muka rabu kowa yana tunanin ɗan uwansa don har ga Allah Anty Tahira mutum ce sosai, ba tada mugunta ko sanda muke aiki da ita ga ta da son mutane sosai.
Har zan tafi sai na jiyo muryarta tana ce wa"am Adawiyya ni kuwa na manta ban faɗa miki ba, ƙwanaki akazo nemanki wajena.................."
gaba na ne ya faÉ—i sosai, to waye É—in yazo nema na? daga take ko ya ke"?.

*** *** ***
tafiya ya ke cike da ƙwarjini, da ka ganshi kaha dakakkan namiji me cike da ƙasaita amman baya tafiya tamkar mace, cike da tafiyar nan wacce ake cewa ta zaki ya ƙaraso ɓangaren mahaifiyarsa, fuskarsa kamar an yi masa wahayi.
autar momma ya fara gani a falo, da handbag É—inta kamar makaranta ma zata je.
ta ce"ina wuni ya Galadima".
ya amsa mata cike da fara'a ya ce" ina Ƙhalbi ko tana ɓangaren me martaba"?.
ya faÉ—i hakan ba tare daya kalle ta ba.
azuciyarta kuwa ce wa take, anya kuwa yau bro ba albishir aka yi masa da gidan aljanna ba? don ita dai bata taɓa ganin dariya akan wannan miskilar fuskar ba, to ko dai don anyi masa aure ne?.
ganin bata amsa masa ba sai kallonsa take ya ce" ke tunanin me kike yi"?.
Da sauri ta ce" tana É—akinta ita da mama Lanta".
bai ƙara ce mata komi ba ya wuce zuwa ɗakin, dom zuciyarsa cike take da son ganin mahaifiyarsa abar tinƙahonsa, abar alfaharinsa abar ƙaunarsa.

Autar Momma ta dannawa Amira kira.
tana É—agawa ta ce

"albishirinki".

Amira ta ce"goro".

"fari ko ja"?.

"fari".

"yanzun naga angonki ya shigo, wallahi bakiga bakinsa ba kamar gonar audiga, ni dai ina jin tun da na sanshi har zuwa yanzu ban taɓa ganin yadda yake wannan smiling ɗin ba sai yau, duk da yana yi amman very sure bai taɓa yin na yau ba".
daga can ɓangaren Amira taji daɗi sosai, tana ɓangaren Gwaggwala ba damar yin magana, don tunda aka ɗaura aure Gwaggwala tace adawo da ita nan ta zauna don babu abinda ta iya sai charting, hatta girki bata iya ba ballantana yadda zata zauna da mijinta.

Amira tayi ɗan ƙasa da murya ta ce" kinsan fa yau ina wajen Gwaggwala, ɗazu ma karɓemin wayata tayi wai na fiya danna waya, shiyasa ban iya komi ba sai yanzun ta bani rabon dai zaki bani babban story me daɗi irin wannan".
Autar momma ta ce" oh wannan tsohuwa ko jarababbiya, to wallahi ki cire kunya ki zage da nemowa kanki matsayi don ni dai na faɗa miki waye bro ɗina, duk dama naga ya karɓi auren ba wani jayayya gashi har da smiling, saboda haka idan na dawo daga skull zanzo wajen Gwaggwalar sai dai ta kore ni, don wallahi sai na kusan sanyata kuka idan nazo, ba ta ɗakko ki bane saboda komi saboda ni ta ɗauke ki, to ai ba a raba jini da hanta".......maganar tata ce ta sarƙe ganin shigowar yaya Aamiru"........

*NA YI MUKU ALƘAWARIN KOYAR DA WASU ABUBUWA KAMAR MAGUNGUNAN MU NA MATA, DA KOYAR DA GIRKI ADUKKANIN PAGE ƊINA*

*MIJINKI A TAFIN HANNUNKI*

Wannna matsin dauke yake da magunguna guda shida Wanda kuma sune mafi shahara wajen Mallaka ta hanyar ganyen magani ba tareda sihiriba
Idan kun lura akwai

(1)Dan kadafi
(2)hana kishiya
(3)kafi malam
(4)bita zaizai
(5)manta uwa
(6)Mallaka

Wadannan kusan kowacce mace me hada magani tasansu saidai wajen sarrafasu shine babban aikin domin sahihin mallaka ne ba ruwanki da boka cikin sauki Zaki shawo kan miskilin mijinki matukar yana saduwa dake ko kuma yanacin abincinki domin maganin kala ukune na farko akwai Wanda Zaki shafa agabanki lokacinda Zaki sadu da mijinki zaiji babu mace irinki saboda dadinki zaiyi jarabarki sosai
Sai kuma Wanda Zaki hada kinasha zai kara miki ni ima ta daban Wanda idan mijinki ya sadu dake shi kadai yasan yanda zaiji
[2/26, 6:53 PM] Ummu Maher Ce: _*❤️F𝘼C𝘼L𝘼 ❤️*_
{{}}Ta fi kishiya🔥{{}}

TAKU NA 2 (Book 2)

_BY_
_*©UMMU M𝘼HER(MRS GREEN)*_💚

*_AREWA WRITER'S ASSOCIATION✍️_*

*AREWABOOK$✍️*
FACALA:: https://arewabooks.com/book?id=6582a28d4ede3c5852b6cb60

*UMMU MAHER COLLECTION👛👠*
https://chat.whatsapp.com/EBmNeSHdAl9EgqmlWo3Z3C

*_SABAYA KAYAN MATA🥰_*
ko kunsan sabaya na gyara jiki🗣️ta ciko miki da ni',imarki a matsayinki na ƴa mace🗣️in har kika rasa ni'ima to tabbas kin zama saura🗣️🗣️na ce ba? kin haihu kinƙi ki koma dai dai? to wallahi ga sabaya zata gyaraki ciki da waje,ta matseki ta dawo miki da martabarki,ita sabaya bata cutarwa ko kaɗan sabida ƴaƴan itatuwa ce herberls.tana ciko da mama yayi kyau sosai.
08067329607.

➡️2
da sauri ta juyo ta ce" ya Aamiru ka shigo mana".
ɗan kallonta ya yi, sannan ya ce" am daman wajen Galadima naje, sai kuma naga baya ɓangarensa shi ne na ce bari in biyosa nan ko yana nan".
ya faɗi hakan kamar an matso maganar tashi daga cikin ƙahon ƙirjinsa.

ganin kamar aɗarare ya ke sai ta ce"ok ai yanzu shigowar ka kenan ya shiga wajen Fulani, amman ka jirasa anan ni skull zan tafi ne". ya amsa mata da kansa kawai ba tare daya ce mata komi ba, amman can ƙasan zuciyarsa shiyasan abinda ya ke damunsa, gameda halin da Yariman ya ke ciki da kuma yardar da yayi dashi yaci amanarsa, alhalin shi ya rufa masa asirin da ba kowa ne zai iya hakan ba ko da kuwa iyayenka ne, waɗanda sukayi sanadin zuwanka duniyarmu.

****
har ya shiga ɓangaren ɗakunan da yake tunanin mahaifiyarsa na ciki,bai daina fara'a da kuma zumuɗin kasancewa da mahaifiyarsa ba, abar tunƙahonsa arayuwa ita ya ke gani ko da yana cikin wani hali yaji zuciyarsa tayi fari.
muryar Lanta ya juyo tana ce wa" to ke yanzu wani biki kika shirya mana don taya É—anmu murna"?.
sai yaji ta ce" to ai ni ke zaki tsara komi, tunda gaki komai ai yazo da sauƙi ni sai in koma gefe in zama ƴar kallo"......dai dai lokacin ya shigo cikin ƙasaitaccen ɗakin na ta, wanda ya gama jin komi na more rayuwa don hatta lallausan capet ɗin da aka shimfiɗa a ɗakin abun ka tsaya ka kalla ne.

wani sanyi taji yana ratsa dukkanin jini da hantarta, farin ciki maras misaltuwa ya ziyarci ƴar kyakkyawar fuskarta ta asalin fulani tamkar dai ba ita ɗin ce ta haifi yariman babban masarauta ba, ɗaya acikin dubu shakundum ja yaƙi soja mazan fama, soja marmari daga nesa idan ya matso sai ka nemi ƙafarka.......

bayan sun gama gaisawa ne Lanta ta murmusa, ganin Fulani ta sunkuyar da kanta alamar jin kunyar ɗan nata amatsayinsa na ɗan fari, don duk da shaƙuwar dake tsakaninsu aƙwai kunya me girman gaske ca take a tsakaninsu, idan suna hira baya kallon idonta itama bata kallon idonsa ahaka suke hirarsu cikin ƙwanciyar hankali.

Lanta ta ce"ango kasha ƙamshi".

sai ya gimtse fuskarsa, fara'ar daya shigo da ita ta gushe akan kyakkyawar fuskarsa, bai ce dai komi ba har sai da Fulani ta ce" inason ka bani labarin abinda ya faru abaya, wanda ni da kaina nasan wasu abubuwan amman bansan dukka ba, ina son ka warwaremin komi sannan inason in baka umarni duk inda yaron nan ya ke kaje ka É—akkosa ka dawo dashi gidan nan, duk ma abinda zai faru ya faru amman baza a salwantar da rayuwar yaro abanza ba".

ganin yaƙi ɗago kansa ya yi magana yasa Lanta ce wa" haba Galadima ka amsa mana ko zamuji daɗi, ka fitar damu acikin duhun da ka sanyamu don dukkaninmu hankalinmu atashe suke, wanda zai ce maka hankakinsa bai tashi ba to wallahi ƙarya ya ke maƙiyinmu ne".
É—agowa ya yi cikin yanayin zafin nama, da kuma zamar son abinda duk ya faru, amman ya rasa me yasa idan ya buÉ—e bakinsa zai yi magana sai yaji tamkar ab rufe bakinne, amman yasan yin shirunsa ba xai haifar masa daÉ—a me ido ba, cike da son basar da maganar ya ce" Fulani don Allah ku bar zancan yaron nan, sannan bana son É—akkosa yazo ya janyo muku abin surutu sannan lokacin da zan bayyana komi yana nan zuwa".
Fulani kamar tayi kuka, don daman tasan ba kallai ne ya faɗi abinda ya faru ba, tasansa da mugun miskilanci saboda haka taja bakinta tayi shiru amman ta ɗau alƙawarin sai ta binciko komi ko da ta hanyar Aamiru ne, don kaf duniya bai da aminin daya kaisa.

Ganin ta bagarar da maganar sai ya ɗan saki fuskarsa, suka cigaba da tattauna yadda bikin zai kaya amman fa shi bai ƙara ce wa uffan ba, yana dai zaune yana kallon wani hoto awayarsa wanda ba zai taɓa gujewa ganinsa ba, tabbas lokaci ya yi da zai nemo wannan fitinanniyar yarinyar, wacce ta firgita rayuwarsa baki ɗaya, wacce ta hanashi ganin kowacce mace amatsayin mace duk wacce zai gani sai ya ganta tamkar namiji ce. yana wannan tunanin Lanta ta fuskance sa, ta taɓa Fulani alamar me ya ke kalla ne?. ta ɗaga mata kafaɗa akan bata san me ya ke kalla ba? cike da dauriya Fulani ta tashi don ganin me ya ke kalla ɗin..........
Chapter 2 · 0% Book details