Sashe 8
Facala Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read
5. Yawan Lalacewar Ciki Ko Yawan Bari A samu kwan agwagwa a soya da man tafarnuwa a bai wa matar ta ci sau biyu (2) A rana har kwana (7).
[2/26, 6:53 PM] Ummu Maher Ce: âž¡ï¸6
……………tana jin wannan kalmar ta mlm sai ta shiga taitayinta, ta fice daga ɗakin ba tare da ta ƙara ce wa kowa komi ba ashe ƙaryar iskanci take, don tasan ko ayanzu idan mlm ya saketa ina ta kama? uwarta da ubanta duk sun mutu? to ina zataje yanzu sai ƴan uwanta duk maza da matansu marasa mutunci, do ko gidansu kaje kallon banza ne atsakaninku , shiyasa indai ba haihuwa ko mutuwa ko suna ba bata yarda ta raɓi inda suke, suma kuma basa neman inda take sai da ƙwararran abu, kamar mutuwa ko suna ko rashin lafiya ko kuma ja je.
Tana fita mlm ya zaune yaraf akujera, duk jikinsa da yake dashi bai ji zafi ko ciwo don zaman da ya yi haka ba, sosai ya daurewa zuciyarsa akan abinda ya ke ji, amman ya kasa hakan don yasan ko da ya daure ɗin ma duk wanda ya kalli fuskarsa yasan yana cikin wani hali, ƴar da ya keso ya ke ƙauna har cikin zuciyarsa amman yau itace acikin irin wannan mummunar rayuwar? Da duk mahaluƙin daya kalli wannan bidiyon zai tsine mata albarka?, tuni ya kasa tsayar da hayensa har sai da ya barsu suka dinga zuba tamkar famfo, mutumin da ya ke da dauriya da kuma tawakkali amman yau duk ya kasa ko da ɗaya, ya tashi cike da karsashi tamkar babu komi ya fice bai cewa kowa komi ba.
Umma ta bishi da kallon tausayi, don tasan kaf ƴaƴansa babu ya Adawiyya, tun tana tsummanta da ƙazantar haihuwa ajikinta ya ke tsananin sonta da kuma ƙaunarta, hatta haihuwar tama Mlm ɗinne ya amsa sai dai yarinyar tazo da ƙaddarori da yawan gaske, tun da aka haifeta ake haɗuwa da ƙalubale kala kala tamkar dai ita kaɗai ce ƴa agidan.
Ammi ta kalli Umma ta ce" wai ni me yake bin wannan yarinyar ne haka? wannan wacce irin ƙaddara ce Umma? ni wallahi na rasa me zanyi awannan gaɓar, ni ayanzu tunani na bai wuce Adawiyya ba? awani hali take ciki me ya same ta da har ta yarda wani namiji ya taɓa jikinta bayan tana da aure? Ko ba tada aure ai ba abune wanda ya ke da kyau ba".
Sai ta rushe da kuka tana ambaton sunan Allah.
Umma ta share hawayenta itama, ta kasa ce wa komi don tasan babu kalmar da zata rarrashi Umma da ita don duk abinda zata faɗa mata tasan dole wannan mummunan tabon ba zai taɓa fita daga zuciyarta ba, wannan wani mummunan tabo ne da ba zai taɓa gogewa a allon ƙaddara ba.
Malam yana zuwa ɗakinsa, ya zauna ya dinga jan carbi har sai daya yi sau babu adadi sannan ya canja kayansa zuwa farar shadda ƙal, babbar riga sannan ya kira Abba, mahaifin Ahmad bayan sun gaisa ne ya ce" Alhaji dama wata magana nake son muyi, akan Adawiyya ne matar ɗanka wasu abubuwane suke faruwa ahalin yanzu, waɗanda baza mu iya datse su ba don sun riga da sun tarwatse baki ɗaya sai dai a nemi hanyar mafita kuma yanzu".
Alhaji dake riƙe da wayarsa ahannu ya ce"nima yanzu buɗe wayata kenan na kalli wannan fefan bidiyon me sanya mutum acikin ruɗani, wallahi mlm ni nasan yarinyar ba zata taɓa aikata hakan ba, ni dai zargin dana ke aƙwai wanda ya shirya koma menene, amma ba muda mafita ayanzu sai dai addu'ah da kuma bincike har Allah yasa agano duk waɗanda suka aikata hakan".
Mlm ya fusgar da wani numfashi me raɗaɗi, sannan ya ce" to yanzu ka fito ƙofar gida sai mu haɗu ko"?.
Alhaji ya amsa da " ganinan fitowa yanzu, don ba a sanyi da burin jiki".
Suka ajje waya su duka biyun, zuciyoyinsu na yi musu wani irin nauyi tamkar an É—aura gugun itace akawunansu.
Mama uwar gida ta ɗauko wayarta da sauri, murna fal zuciyarta yau Allah ya cika mata burinta na wulaƙanta waɗanda ta yi masifar tsana arayuwarta wato kishiyarta da ƴarta Adawiyya.
Hannunta har kakkarwa ya ke tana neman lambar da zata kaɗawa kira, kiran farko Mama Safiya ta ɗaga tana ce wa" ƴar halaj kinƙi ambato yanzun na ce, Safiya ta zo ta dubamin ke ƙwana biyu? Babu kira kuma babu zuwa"?.
sauke wata ajiyar zuciya tayi me cike da murna da kuma ƙawazucin son faɗawa Mata abinda ya ke faruwa ta ce" uhm ta ina zaki ganni? kin san idan Mlm yana nan to babu kai babu fita, shiyasa kika ji ni shiru amman ga wani albishir".
ta ce" goro".
"Fari ko ja?".
"Fari".
duk abinda ya faru ta ƙwashe ta faɗa mata jikinta sai kakkarwa ya ke, ta ce" ai yau sai nayi sadaka tsabar murnar dana ke ciki, ke dai kizo zuwa anjima ki ƙara shan labari, yadda mutuniyarki ta ƙule ɗaki taƙi fitowa tun ɗazu nake leƙawa ko zanji ko da tofinta, amman shiru kike ji tamkar malam yaci shirwa".
Mama Safiya ta sheƙe da dariya sannan ta ce" uhm ai daɗi na da gobe saurin zuwa, a'i dama na faɗa miki karo da aljani babu kyau shiyasa nake jiye mata ranar da zata faɗa koman mu, yanzu dai wa gari ya waya? ai ni nasan shi da kansa mlm ɗin yanzu zai tsaneta da ita da ƴarta, saboda haka ki koma gefe kisha kallo sannan agefe kiyi ta famfa Mlm ya hau sosai yadda zai yi mata korar kare, gamida takardar sakinta idan da hali ma ayi mata saki uku ƙwarara muma hankalinmu ya ƙwanta muyi ɗan kumari, haba kullum magana ɗaya Zulaiha ta fiku kirki ta fiku meye, shima Alhaji kullum maganarsa ɗaya kenan, wai Zulaiha ƴar aljanna ce wai tsabar cin fuska facala ta ce ƴar aljanna ni kuma ƴar wuta? yo duk mutuncina da facala ta idan naji mijina yaba yabonta ai ranar ba shida abinci agidan".
haka dai suka ɓata lokaci suna ta murnarsu na abinda ya samu Adawiyya da kuma iyayenta, abin ƙaunarta Malam da kuma Ammi ya yinda ita tana can baiwar Allah bata san abinda ya ke faruwa ba don lokacin ma barci take yi, duk tuggun da Balaraba ta shirya mata bata san halin da take ciki ita kanta ba har zuwa yanzu, don maganin da ta sanya mata aruwa yana kai tsahon awanni 8 ba tare da mutum yasan inda ya ke ba.
*** *** ***
Ahmad ne zaune, tunanin duniya ya ishesa tun lokacin daya kalli wannan fefen bidiyon zuciyarsa sai harbawa take da saurin gaske har sai daya sanya hannunsa ya riƙe saitin inda ya ke buga masa, idanuwansa sukayi jawur tamkar garwashin wuta da ƙer ya ke iya haɗiyar yawu saboda wutar masifar da ke azalzalar zuciyarsa, wacce take cike da ruɗani da kuma wasi wasi akan abinda ya kalla, duk da kishi ya rufe masa idanu amman yana ɗarsawa ransa anya kuwa Rabiatun dai daya sani ce matarsa ahannun wani namijin? anya kuwa zata iya aikata wannan babban zunubin? tuni idanuwansa suka rufe, ya fara ganin wani irin yaji yaji ya tashi da wani irin saurin gaske ya baro wajen aikinsa ya dawo gida, don ayau za'a yi ta taƙare kome ma zai faru sai dai ya faru don waɗannan abubuwan sun ishesa, daga wannan masifar sai wannan masifa? saboda haka ayau ba a gobe ba zai datse wannan alaƙar da ta sanyashi ya ɗauru da matsaloli kala kala.
yana isowa ƙofar gidan ya tarar da Alhaji Badamasi mahaifinsa sannan Malam mahaifin Rabiatu.
Sosai suka kafa masa idanuwa, suka kasa ɗaukesu daga kansa saboda yadda suke hango tsananin ɓacin rai a idanuwansa, wutar masifa da wutar kishi ce take ta faman aci bal bal azuciyarsa da ƙwaƙwalwarsa.
Babu yadda zaiyi dolensa ya ƙarasa ya tsugunna har ƙasa yana gaida su Malam, Alhaji ne ya iya magana don Malam shiru ya yi daga wannan amsa gaisuwar bai sake tofa ko da uffan ba, don shi ahalin yanzu baya buƙatar yin magana zuciyarsa baki ɗaya ta gama tsinkewa duk da carbinsa na hannunsa yana ja, bakinsa ɗauke da addu'o'i kala kala na neman samun yafiya daga wajen ubangiji da kuma samun rahama.
"Ahmad dukanmu munji kuma munga abinda ya faru, amman abu ɗaya dana ke so kasani shi ne ƙaddara bawa baya taɓa tsallakewa ƙaddararsa, duk inda yake kuma aduk inda ya ɓuya, Allah yana ganinsa kuma dole sai an jarabcesa, kada ka taɓa cire rai da rahamar ubangiji, azatona kuma atunanina ko da Rabiatu tayi wannan abun da ake gani amatsayin abin kamata alaifi, kai bai kamata ka ƙyamace ta ba biyo bayan irin abubuwan da suka faru abaya, sannan bayan haka ma kai kafi kowa sanin tarbiyyar Rabiatu kai da kanka ka shaida tarbiyyar da ta samu daga wajen iyayenta, uwa da uba kai da kanka kasha faɗamin kyawawan halayen matarka, shi zato zunubi ne ko da ya kasance gaskiya ne, saboda haka inason ka yi haƙuri ka fauwalawa Allah komi shi xai dube mu ya fitar damu daga cikin wannan tsaka me wuyar da muka tsinci kanmu, sannan ahalin yanzu muyi mata adalci muji ta bakinta sannan kuma a tsaurara bincike tunda ba ita kaɗai ce agidan ba".
wannan maganar da mahaifinsa ya faɗa ta ƙarshe ita ce ta sanyashi jin ɗan sanyi ajikinsa, to idan Rabiatu za tayi yawonta ai bazata kawo namiji gida ba, gudun kada asirinta ya to nu sannan kuma za taji tsoron Balaraba tunda ai waje ɗaya suke, kusan za'a iya ce wa ma ga ɗakinta ga ɗakin Balaraban, saboda haka shi gani ya ke anya ma ba da wata aƙasa ba kuwa........................
Alhaji ya katse masa numfashi da ce wa" mu shiga gidan yanzu, idan ka shiga sai mu biyo ka mi zauna afalo ka kira mana mutanen gidan É—aya bayan É—aya".