← Book details Facala Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 21

Sashe 16

Facala Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

yana shan coffie ne awani ɗan ƙaramin cup fari ƙal na glass, coffie ɗinda bai fi cikin cokali goma ba computer ɗinsa ɗauke akan cinyarsa yana jujjuyawa, yana farin ciki yana wasa da ɗansa tamkar gashi ga yaron.

Haushin wannan bugun ya sanyashi kashe computer ɗin baki ɗaya, ya ƙaraso bakin babbar ƙofar tasu ta alfarma tamkar ƙofar gate amman irin ta katako je dakakkiya ƙirar Turkey, wacce taji kayan ado na alfarma tamkar ba ƙofa ba.

yana buɗewa ya iske Gwaggwala tsaye tana yi masa wani irin kallo na baka isa, shima yana tsaye tamkar dogari gashi ya kasa matsawa sai kallon mamaki yake mata, sannan ya buɗe ƙasaitaccen bakinsa ya ce" sannu da zuwa Gwaggwala me babban ɗaki, ina tunanin ko dai kinyi ɓace ne kika faɗo mana nan tamkar aradu daga sama, babu zato babu tsammani kinsan dai gidan angwaye ne ba'a yi musu dirar mikiya ko?".

sosai taji kunyar maganarsa, amman sai ta maze tayi masa na yaran zamani sannan tayi masa wayo da dabara irin na waÉ—anda suka ga jiya suka ga yau, ta ce" to ai gwara inzo don ko banzo bama ai za'a kirani don tun sassafe ma naso zuwa, sai kuma na aiko da Jakadiya don ta ganemun ku? sai tace ai duk kuna lafiya ma, to shi ne nace nima bari inzo in duba ku É—in, amman tace É—azu bata ga gimbiya Amira ba ai tana faÉ—ar hakan na ce ai gwara inzo da kaina inga ko lafiya bata ganta ba".

ta faÉ—i hakan da dabarar son sanin abinda ke faruwa, tunda dai shi ba zai faÉ—i komi ba ta sanshi da masifar miskilanci da kuma zurfin ciki irin na mahaifinsa, shiyasa take son ta zo masa da salo da kuma dabara.

Jin ta ce hakan, sai ya ce" oh kinzo dai sa'ido kawai Gwaggwala, amman banda haka sai ki taso ki taho da sassafe haka, masu gidan ma basu san da zuwanki ba"?.
Gwaggwala tayi zuru tana kallonsa cike da haushi, daman tasanshi da masifar wayo kamar dila da dabara tasan zai yi wuya bai gano inda ta dosa ɗin ba, saboda haka sai ta harzuƙa ta kuma fusata ta miƙe tana lalleƙa ɗakunan dake falon, tare da shiga ɗayan ɓangaren na gidan tana ƙara buɗe hanci da baki wajen ganin yadda aka tsara komi amuhallinsa tamkar daman don su akayi komi, ta kasa gane yadda ɓangaren yake gidane me part kusan huɗu kowanne kuma yana da girma ga kuma saman benen daya zagaye ɗakin yayi circle sosai ga ta ita kanta matattakalar da faɗi da kuma tsayi tamkar ba a falo ba, haushi ya kamata ta dawo da baya ta kalleshi ta ce" to sai ka tashi ka nuna min ɓangaren jikata?".

ya ɗan murmusa irin murmushin daya sabayi idan yaci nasara kan wani abu, sai kuwa ya ce" to ai da kinci gaba da dubawa wataƙila kiyi katari da naki ɓangaren, kinga sai inyi ciko da ke ko"?.

ta galla masa harara sannan ta ce" haba yaro ai komi wayon amarya sai ansha manta, indai muna raye zanzo in zaɓa me kake ci na baka na zuba"??. tayi maganar tana yin gaba alamar so take adole ya nuna mata sashen.

ya murmusa sannan ya ce" to ai da kin dawo baya nayi gaba wataƙila na taimaka miki don ki hau benen". da sauri ta gwalo ido daman ga Gwaggwala da manyan idanu ta ce" subhana yanzu ni da wata ƙafar zan iya hawa wannan benen me kusan hawa ɗari"?.
ya murmusa sannan ya ce" ah da ƙafarki mana gwaggwala, ba jikarki zaki gani ba? shi ne zan rakaki wajenta ai".

tayi rau rau da ido, ta ce" haba ɗan nan? Yanzu kai saboda ka ƙware da mugunta ka rasa inda zaka ajjeta sai asaman bene tamkar shaho? haba ba'a banza ba ka iya mugunta haka ashe uwarka usulin Fulani ce, shiyasa lokacin da mahaifinka zai aure ta naso na hana, sai akayi katari kuma ƴar uwarsa ce banda haka da bazan taɓa yarda ya auromin ɗiyar mugunta ba".

ya ƙyalƙyale da dariya sannan ya fara hawa saman yana sanye da hannunsa cikin aljihun farar doguwar riga irin ta barci tayi masa kyau sosai, gashi fari dogo namijin ingarma.

yana tafiyar yana ce wa" gashi kuma ita Fulanin ta fitar da tsiro har an yi girbi sun zama gudan jini, kinga kuwa ko kiso ko kar kiso jikokinki Fulani ne".

*** *** ***

Alhaji mawashi yayi saurin juyowa, gamida ƙarewa mutumin kallo duk da tsawon wasu shekaru basu haɗu ba amman ya gane sa sosai, yayi saurin bin mutumin yana nemansa amman ko kafin kace me ya neme sa ya rasa, da yake da mutane da yawa wajen biyan kuɗine na asibiti.

Sosai ya ruɗe, ya kasa gaba balle baya tunaninsa kawai inda zai ga mutumin don bayyanar wannan bawan Allahn shi zai sanya rayuwarsa rugujewa tamkar yadda akw ruguje gini daga gini zuwa fili, ya kusa fashewa da kuka saboda ruɗani amman haka ya daure ya wuce sashen da aka ƙwantar da ƴarsa, wacce rayuwarta ke cikin gagarumar matsala wacce tafi tashi don ganin wannan mutumin ba iya shi kaɗai zai wa barazana ba, hatta shi barazana ce arayuwarsa balle kuma uwa uba wacce yake so yake ƙauna ita ce abar tsoro fatansa dai Allah ma ya ɗauki ransa bayan ya fita a asibitin.

yana shiga ya ƙarasa da sauri, ganin Amrah aƙwance tamkar gawa hatta farcenta ma bata iya ɗagawa, fuskarta duk bandeji alamar fuskarta abin yafi shafa.

Hajiya Rabi da mahaifiyarta suna gefe, suna kallonsa don ko ɓangaren da suke ma bai kalla ba ta ƴarsa kawai ya ke, Hj Rabi ta ce" sannu da isowa Alhaji"?.

Ko kallonta bai yi ba kuma sarai yaji komi amman yayi shiru tamkar mlm yaci shirwa, shi ayanzu ma gani yake duk halin da ƴarsa ke ciki ita ta sanyata ciki. Gefe ɗaya kuma na zuciyarsa yana tuna wannan mutumin daya gani yanzu wanda yake shirin barazanar tarwatsa rayuwarsa...............soon➡️
[2/26, 6:54 PM] Ummu Maher Ce: ➡️14

………… Hajiya Rabi ta ce" haba Alhaji ya ina maka sannu da zuwa kaƙi amsawa? Allah dai yasa lafiya domin ban gane yin shirunka ba"?.
wani kallon zaki san koni waye yayi mata sannan ya ce" har zaki tambayeni lafiya? yarinyata tana gadon asibiti babu lafiya kuma ki dinga tambayata lafiya? to bari kiji idan ma da haɗin bakinki komi ya faru ni nafi ƙarfinki, daga har masu Zugaki ɗin Allah ya fiku, kuma ki sani ni bana yafiya duk abinda akayi min sai na rama haka nake".

ya faɗi hakan yana girgiza mata babban ɗan yatsansa, ta zaro ido tana kallonsa Mama ta dinga mamaki da jimamin halin Alhaji Mawashi, wannan wani irin mugun hali ne dashi har haka? ƴarta na bashi labarinsa amman bata taɓa tunani ko hasaso haka halin nasa yake ba.
da mamakinta ta ce" haba Alhaji? ya uwa zata so jefa ƴarta cikin matsala? idan hankali ya gushe ai tunaninmu bai kamata ya gushe ba, sanman arayuwa ana son mutum me yadda da ƙaddara me kyau ko mara kyau, ka kasance cikin masu yarda da ita sai kaga cikin ƙanƙanin lokaci Allah ya kawo maka mafita daga dukkanin halin da kake ciki".
ya kai maƙura da wannan matar, tana son nuna masa bai san menene ƙaddara ba ko miye? itama fa yana lura da ita ba son Amrah ɗin take ba, saboda haka zai san yadda zai yi da ita don duk wanda ya tsani ƴarsa Shima ya tsanesa.

ana cikin wannan halin me likita ya shigo, suka gaisa da Alhaji likitan ya ce" barkanka da zuwa Alhaji ashe har ka iso"??.

kamar abin arxiƙi ya ce" eh na iso, daman ina jiranka ne kazo don muji ta yadda zamu ɓullowa matsalar ƴarka Amrah".

da sauri ya juyo don jin matsalar ƴar tasa ya ce" likita me kake son faɗamin? banda wannan matsalar ta fuskarta har aƙwai wata matsalar ne"?.
Likita kuwa ya ɗaga kai shida bai san dawar garin ba, ya ce" eh Alhaji aƙwai kuwa matsala babba ma don ƴarka tana cikin babban riski wanda in har ba'a yi mata maganin damuwarta ba komi zai iya faruwa da ita, domin hawan jinine yayi mata babban kamun da komi zai iya faruwa da rayuwart..............."

tun kafin ya ƙarasa Alhaji ya shaƙosa da sauri, ya ce" kai likita wannan wani irin mugun sharri ne? ta ya za'ace yarinyar da bata fi 24 ba ace wai tana fama da hawan jini har haka? ko ka ce ba haka bane ko kuma inyi maganinka yanzu ɗan sharri me mugun baki".
Da sauri Hajiya Rabi ta miƙe ta isa gare su tana kuka tana ce wa" haba Alhaji wai mi yasa kake haka ne? likita zai maka ƙarya ne akan ciwonta...................

bata ƙarasa ba ya sharara mata wani lafiyayyan mari, sannan ya ƙara ɗaga hannu zai ƙara mata Mama ta tashi da sauri har da wata sufarta ta riƙe hannunsa, ta kallesa kallon cikin ido tayi masa wani mummunan riƙon da bai isa ya kauce ba, ta fara magana cikin kakkausar murya ta ce" ashe daman ba kada hankali? ashe dabbancinka da ake faɗa ya wuce haka? wallahi ayau ba sai gobe ba zaka sakarmin ƴa, saboda ƴarka ba ƴar gwal bace sannan baku isa ku kashemin ƴata indai har ba lokacinta ne yayi ba, na gane bakwa buƙatarta arayuwarku daka kai har ƴarka, saboda haka ka sake ta kuma saki uku yadda babu wata alaƙar da zata shiga tsakaninku ko da nan gaba ne kuwa".

ta ƙarasa faɗar hakan tana sakar masa hannu, ya koma gefe ya zauna kan wani ɗan ƙaramin benchi, ya zauna yana mayar da numfashi ya saki wani irin kuka me wuyar fassaruwa.
sai da yayi kukan me isarsa, sannan ya fice baki ɗaya daga asibitin ba tare daya ƙara ce wa komi ba, takaici fal zuciyarsa yau idan ba don wani ɓoyayyan sirri ƙwara ɗaya tak ba, da babu abinda zai sanya shi zama da Rabi sai dai ita kanta Rabin ba ƙashin yadawarsa bace don ta taka babbar rawa acikin rayuwarsa, saboda haka ba yadda zai yi dolensa ya ɗauki wani matakin na daban.
Chapter 16 · 0% Book details