← Book details Facala Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 21

Sashe 5

Facala Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama uwar gida ta saki baki ganin Ammi sai kuka take, ga kuma Malam da kansa shima hankalinsa amatuƙar tashe, tuni zuciyarta tayi wasai tamkar an wanke ta da soso da omo sannan ta ƙaraso cikin salon yaudara da nuna damuwa afili ta ce" lafiya kuwa na ganku cikin wannan halin? Waye ye mutu?".

malam ne ya iya bata amsa da ce wa" zamuje unguwa ne amman yanzu zamu dawo".

baki galala ta buɗe na mamaki sannan ta ce" to amman ai kasan ƙwanane ko mlm? wannan wani irin zalunci ne wai? ace ranar ƙwananka adinga zaluntarka? ke dai Zulaiha kin cika kanwa uwar haɗi, da kina da dama da tuni kin rabani da mijina, saboda kissarki ta shuwa arab".

babu wanda ya kulata suka fice, zuciyoyinsu duk a tunkushe waje É—aya dukkansu sun kasa ko da tafiyar nutsuwa saboda tashin hankalin abinda ke faruwa.

suna shigowa gidan suka tarar gate ɗin a kulle, sai suka ɗan ƙwanƙwasa ƙofar gate ɗin Balaraba dake ƙwance afalonta tayi ɗai ɗai tana cikin nishaɗi taji ƙarar buga gate, ta ɗan buga tsaki ganin ba a dena bugawa ba saboda haka ta tashi da tsohon cikinta ta wuce don ganin wanda ke son cika mata dodon kunne.

ko da taje sai da ta ɗan leƙa kaɗan ta wani waje dake jikin gate ɗin, ta ɗan bushe da dariya ganin Malam da Ammi tsaye sunyi cirko cirko hankulansu duk atashe, ta ɗan tsaya kaɗan tana tunanin wani irin makirci zata shirya.
da sauri ta koma zuwa ɓangarenta taje ƙofar ɗakin Rabiatu ta janyo ahankali, sannan ta koma ta rufe ɓangarenta ta barsu awajen suna ta buga ƙofa, suka kira wayar Rabiatu itama akashe, suka kira wayar Ahmad shima akashe hankalinsu dai duk ya tashi, ƙarshe dai sai gida suka dawo Balaraba da taji shiru ta leƙa ɗakin Rabiatu sai ta ganta ta ɓingire tana barci, alamar maganin da ta sanya mata aruwa tashs kenan, sai ta dawo da sauri ta ɗauke wayarta sannan ta kira wata lamba awayarta sannan ta ce" yauwa plan A da B ya cika sauran plan C shima ina kan hanyar kammalasa".
sai ta bushe da dariya,lokacin da ta jiyo ƙarar Khadija ta fito daga ɗakin da ɗan sauri saurinta tsautsayi ya ɗebe ta sai taji........soon➡️

GYARAN FARJI BAYAN KIN HAIHU INA MATAN DA SUKAI HAIHUWA DA YAWA KO KUMA MATA MASU MATSALA BUDEWA

dole duk macen data haihu ta gyara kanta don ita mace yar gyara ce, mu hankalta mata a farka.

•aloevera.
•Karo.
•zaitun.
•kanunfari.
Ki samu aloevera ki samu Karo ki jefa kanunfari, ki tafasa ki dinga Kama ruwa dashi.
Sannan idan kika samu ganyen aloevera ki matse ruwan ya fito ki dinga wanke farjinki ki wanke wa da ruwan dumi, sai kuma ki dinga shafa zaitun in Zaki wurin maigida.

MATSALAR KEKASHEWAR ALAURA RASHIN NI'IMA

KARIN NI'IMA AMARYA

Karin ni ima da Sha'awa ga amarya da ango amarya ga kayan hadin kamar haka 1 zuma 2 idon zakara Adaka idon zakara yayi lukwai sannan a kwaba da 1 kananfari 2 zuma 3 garin ridi nonon shanuwa marar tsami ki dafa kananfari da ruwan zafi idan ya dauko nuna dahuwa sai ki sauke ki sami garin ridi da nonon shanu marar tsami ki hade guri guda ki gauraye ki saka a firij ko kisaka kankara idan yayi sanyi sai ki Sha. wanan hadin idan kinyi sai kuma bayan mako daya sati daya za a kumayi amarya sakin goda kinban labari
[2/26, 6:53 PM] Ummu Maher Ce: *_SABAYA KAYAN MATA🥰_*
ko kunsan sabaya na gyara jiki🗣️ta ciko miki da ni',imarki a matsayinki na ƴa mace🗣️in har kika rasa ni'ima to tabbas kin zama saura🗣️🗣️na ce ba? kin haihu kinƙi ki koma dai dai? to wallahi ga sabaya zata gyaraki ciki da waje,ta matseki ta dawo miki da martabarki,ita sabaya bata cutarwa ko kaɗan sabida ƴaƴan itatuwa ce herberls.
yana gyara breast sosai,masu son su ciko suyi gwanin sha'awa sai su garzaya su nemu na su.
tana maganin ramewar mace, ki ciko kiyi gwanin sha'awa, ina mata masu son gyara gaba ya ciko ya y zam zam yadda oga zai gamsu, sannan ina mata masu son ganin mamansu ya yi zam zam to ga sabaya nan zata gyara ki zam zam.
idan kin shirya gyara ki kirawo MAMAN KHAIRYS SABAYAS🗣️🗣️🗣️🗣️.
08067329607.
💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼

➡️4
...........ajje wayar tayi tana kallo na tana dariyar mugunta, don tasan daga yau ba ma Ahmad kaɗai ba iyayena ba zasu ƙara ganina da daraja ba.
ni kuwa baiwar Allah barcina nake yi ta yi, sai dai barcin nawa cike ya ke da mafarkai marasa daÉ—i, waÉ—anda na dinga ganin abubuwa da dama acikinsu.

Ammi tana zaune tunanin duniya ya isheta, tana son kiran Æ´arta amman ta kira wayar shiru, Malam ya shigo ya zauna kusa da ita ya ce" wannan kukan da kike yi ba shi ne zai cire Æ´armu a cikin matsala ba, kamata ya yi ace yanzu kina gaban ubangiji kina nema mata kariyar ubangiji, amman kuka ba zaiyi komi acikin wannan yanayin da muke ba, abinda ya kamata yanzu shi ne ki tashi muyi alwala muzo mu gabatar da sallolin nafila wa ubangiji har Allah ya fitar da ita daga cikin wannan tsaka mai wuyar".
haka kuwa ta tashi duk jikinta babu wani ƙwari tamkar ba tada lafiya.

suna cikin yin sallar Umma ta shigo amatuƙar hargitse tana ce wa" inna lillahi wa inna ilaihi raji'un, shikkenan mun shiga ukunmu masifa ta shigo cikin familinmu, ya Allah kasa mafarki nake ba da gaske bane".

duk da gabansu ya faɗi amman basu tsaya da bautawa Allah ba har suka kai raka'a ta biyu, suka sallame zuciyoyinsu na sarƙe da juna tamkar dai zasu faso ƙirjinsu su fito saboda tsabar tashin hankalin da suke ciki.
ana cikin haka Umma ta shigo tana zage zage tana ce wa" haba wannan wani irin akuyanci ne da dabbanci, ya za'ayi da aurenki ki dinga zina da wani namijin wannan ma ai ba ɗabi'ar ɗan adam bace ɗabi'ar dabbobi ce, haba ni daman nasan za'a rina shiyasa mijin yaƙi yarda da ita,ashe yasan ƙasurgumar maras mutumci ce, tunkiya uwar tunɓele".
Sosai Ammi taji abin ya yi matuƙar dukan zuciyarta, duk da haryanzu bata gano abinda duk ake surutun akansa ba.
Mlm ya kallesu su dukansu sannan ya ce" kai wannan wani irin rashin mutunci ne? menene kuma zaku shigo mata É—aki kuna wannan surutan"?.
Mama uwar gida itace kanwa uwar haÉ—i ta kada bakinta ta ce" eh saboda tsabar zubarwa da gida mutunci ka duba kaga abinda wannan yarinyar ta aikata? anya kuwa ba Æ´ar shegu bace wannan yarinyar".?
Mlm ya daka mata tsawa sannan ya ce" wai ke menene? ki fito fili ki faɗa mana abinda ya ke faruwa, ni musulmi da aka haifa cikin musulunci tun fil azal, saboda haka ni bazan zargi kowa da faruwar komi ba sai abinda Allah ya ƙaddarowa rayuwa ta".

mama uwar gida ta ƙara harzuƙa, ya yinda ta fizge wayar dake hannun Umma ta ce" ai nasan itama abinda ya kawota ɗakin kenan, don tazo taga ko kunsan abinda ke faruwa? Sai kuma aka sameku kuna ibada, ashe ana can ana aikata masha'a, mu dai Allah ya isanmu don wallahi an cuci ƴaƴanmu an ɓata musu suna".
Tana faɗar hakan tana laluba inda facebook ya ke don nuna musu komi, ita kuwa Ammi tuni ta kama salati don tun kafin ma afaɗa mata zuciyarta tamkar zata fito haka takeji, ga kuma wani irin faɗuwar gaba tana roƙon Allah yasa kada abinda take zargi ne ya faru, idan kuwa hakanne ita da kanta tasan zuciyarta bugawa za tayi baki ɗaya tayi bom.
*** *** ***
daga can nesa Amrah ta hango ango Yarima Aliyu, fuskar nan tasa tayi kyau sosai cikin yanayin kayansa na gidan sarauta, amman kalar ruwan fari ƙal kamar madara, itama amayarsa Amira tasha wani rantsattsan leshinta fari ƙal, da ratsin brown colour kalar ruwan sirfanin dake jikin Yarima, doguwar ƙasimbar nan tasa tayi luf luf tamkar wace aka yi wa yayyafin mai ajiki yadda take kyalli da kuma shining.
ya sanya irin hular sarakan nan , wacce ake ɗan lanƙwasa kanta sosai ya yi mata kyau kyaunsa da haskem fatarsa ya ƙara fitowa sosai, kishinta ya ƙara fitowa fili har sai da Yesmin ta ce" haba Amrah ki yi tunani fa, don naga tamkar kina son zubarda hawaye ne? ba fa agida muke ba, don Allah ki maida komi ba komi ba awajen nan, don kinsan ƴan gidan sarautan nan ba kirki ne dasu ba, yanzu sai su kawo mana raini sannan kuma ki kula mubar wajen nan lafiya, idan yaso daga baya koma meye zai faru sai ya faru ɗin, amman kada ki sake ki nuna ki shanye baƙin cikinki azuciyarki, har sai lokacin da Yarima zai zama mallakinki ki motsa kambunki yadda kike so".

da sauri ta kalle ta sannan ta ce" kina tunanin zan iya shanye wannan gagarumin baƙin cikin? kinsan tun tsawon lokacin dana ɗauka wajen adana soyayyarsa a cikin ruhina da gangar jikina, shi ne kuma yanzu ina ganinsa da wata kice hankalina zai ƙwanta? Wallahi babu macen daya isa ya aureta har su rayu cikin aminci da ƙaunar juna, wallahi sai na yi sanadin rushewar wannan farin cikin da waccan jakar take ciki,sai na yi sanadiyyyar mutuwar tama baki ɗaya".

Sosai Yesmin ta zaro ido, sannan ta rufe mata baki ta jata zuwa wani waje acikin ƙaton hall ɗin, tuni Amrah ta rushe da kuka tamkar wata ƴar ƙaramar yarinya ta kama ihu sosai har tayi me isarta, daga bisani ta janyo hannun yesmin zuwa ƙirjinta ta ce" kina jin yadda zuciyata take bugawa? to wallahi muddun ban auri yarima ba komi zai iya faruwa dani, tabbas sai na auresa sannan babu yarinyar da zan zauna da ita amatsayin matarsa wallahi duk wacce ya aura sai na yi sanadin rayuwarta".

da mugun sauri ta kalle ta sannan ta ce"haba Amrah? wannan wani irin furuci ne? kinsan kuwa me kike faɗa? kina son yin kisa ne ko menene? kiyi haƙuri mubi komi ahankali mana"?.
Ganin taƙi gane abinda take son sanar da ita ne yasa ta janyo hannunta ta kaita cikin motar da suka zo da ita sannan yesmin ɗin taja motar da ƙarfi suka bar wajen".
Chapter 5 · 0% Book details