← Book details Facala Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 21

Sashe 18

Facala Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

ko amotar ma bai ce min komi ba, ni kuwa mamaki ne ya cikani domin naga ba haka mukazo wajen ba fuskarsa cike da walwala da farin ciki, amman kuma sai gashi cikin ƙanƙanin lokaci ya koma tamkar namijin zaki fuskarnan ya haɗe gabas da yamma.

Ammi ce ta kirani awaya, nayi saurin É—agawa jikina duk asanyaye na gaisheta ina tambayarta Malam da mutanen gidan?.

ta ce" yanzu haka ma muna tare dashi ya ce in gaisheki, amman gobe zamuzo gidan naku don gobe Ahmad yace min zaki tare aɓangarenki".

na amsa mata duk jikina babu daɗi, jin muryata haka sai ta ɗauka ko don duk abinda ya faru ne, sai kuwa ta ce" sai haƙuri Adawiyya ai in sha Allahu babu abinda zai ƙara faruwa duk mlm ya bani labarin komi, har wajenki daya ƙone kada ki damu komi ba duniya ƙunusun fana'un ne ƙararre fararre".

ta dinga yimin nasiha, jikina yayi sanyi don jin abinda take ce min sai ga hawaye suna bin kuncina mukayi sallama, ina ce wa" ya Ahmad Ammi tana gaishe ka". ya amsa ba tare daya kalle ni va, tsoro ya kamani kada fa mu dawo yadda muke da don wancan É—in ma daga haka ya fara har abin yayi nisa ya gagari kundila.

tambayarsa na fara yi abinda ya faru? na matsa masa da tambaya nan da nan ya firgice idanuwansa suka kaɗa sukayi jawur ya juyo don ya bani amsa kawai sai motarmu tayi karo da wata...............soon➡️
[2/26, 6:54 PM] Ummu Maher Ce: ➡️16
.............tun daga lokacin babu wanda ya ƙara sanin inda kansa ya ke, sai a asibiti muka samu kanmu da ƙer na iya buɗe idanuwa na ina duban ɗakin dana ke, zuciyata sai harbamin take da sauri da sauri na fara magana ahankali" ruwa....ruwa...ruwa... zan sha".
da sauri likitar ta É—akkomin ruwa ta fara bani cikin nutsuwa, na juyo ahankali na ce" me ya kawoni asibiti kuma"?.
ta É—an sunkuyar da kanta sannan ta ce" sorry Æ´ar uwa kun samu accidents ne, so amman ke iya buguwa ce kika samu".
da sauri na miƙe domin tunowa da mijina dana yi da kuma Nana khadija, da mugun sauri na tashi ina salati, ko ɗan ƙwalina ban nema ba na fara shirin miƙewa don zuwa wajensu.

likitar ta riƙeni tana bani baki, akan ce wa inyi haƙuri su basu farfaɗo ba amman ban saurare taba na wuce fuu abina, ina fitowa na dinga duba ɗakuna har sai dana gano inda ya Ahmad yake to amman banga khadija ba, tsoro ya kamani na buɗe ɗakin na shiga, ashe likitan yana ciki na faɗa kan ya Ahmad ina kuka da salati, saboda yadda duk yaji ciwo ajikinsa duk jikinsa bandeji ne.

na tashi da sauri ina ce wa" likita aƙwai.....aƙwai wata yarinyar da mukayi hatsarin tare, ita tana ina"?.

sai daya gama rubutunsa sannan ya É—ago, sai daya É—an ja fasali sannan ya ce" baiwar Allah wannan yarinyar tana can É—akin, muje in nuna miki ita".

na bisa da sauri zuwa ɗakin, har ina haɗawa da tuntuɓe sai waiwayan ya Ahmad nake ina kuka na rasa inda zan tsoma rayuwata, kuka biyu kenan ga Nana khadija ga na Yaya Ahmad.

da baya na fara tafiya, saboda ganin Nana lulluɓe da farin kyalle, sosai na firgita har na sanya ihu likitan ya dinga bani haƙuri amman ni ba ta tasa nake ba, ta abinda idanuwa na suka ganemin nake.

likitan ya ce" wannan yarinyar tun sanda hatsarin ya afku aka duba numfashinta, ta rasu kuma daman ba isasshiyar lafiya ce da ita ba saboda haka ku kira Æ´an uwa sai azo a É—auke ta".

sosai naji maganar tasa ta daki ƙwaƙwalwata, wannan fa shi ne rana zafi inuwa ƙuna, ni aganina matsalolina duk sun gama warwarewa ashe ba haka bane, domin kuwa ni nafi kowa sanin halin Balaraba, baki ɗaya ni zata ɗorawa alhakin mutuwar ƴarta ba zata lura da ƙaddara ba, ni zata ɗorawa laifin mutuwar ƴarta daman gashi ayanzu ma tana jin kamar ta kashe ni ina kuma da ƴarta ta mutu ta sanadiyyar hatsari, kuma ina tare da ita lokacin da hakan ya faru?.

kuka nake sosai, har ban san adadin kukan danayi ba na ɗauki wayata da ƙer na kira lambar yaya zubair, don wayata babu abinda ya same ta tamkar babu wani hatsarin da mukayi.
Bugun farko ya É—aga yana ce wa" lafiya kuwa haryanzu baku dawo ba?".

jin hakan ya sanyani fashewa da matsanancin kuka na kasa magana baki É—aya sai jan zuciya nake, jin hakan hankalinsa ya tashi sosai ya ce" me ya faru ne Adawiyya? kukan me kike yi? Allah yasa dai ba wani abune ya faru daku ba?".

jin hakan ya sanya Balaraba murmushi, sai dai shifa ramin mugunta idan zaka ginasa ka ginashi dai dai da kai, domin kuwa ta manta da Æ´arta ma aciki sai da taji mijinta yana ambato khadija sannan ta farga, kuma taji yana salati.
Kamar mahaukaciya sabon kamu, ta janyo wayar dake hannunsa ta sanya akunnenta tana ce wa" uwarki mi ya samu khadijan, banza baƙa me baƙar aniya wallahi muddin wani abu ya samu ƴata wallahi bazan taɓa barinki ba, yadda kika sanyani baƙin ciki kema sai na sanyak......."

bata ƙarasa ba ya warce wayarsa, yana sanyata a aljihunsa ya kalleta ido acikin ido cike da ƙunar rai ya fara magana, duk haukanki ba zaki dawo da hannun agogo baya ba ahalin yanzu khadija ta rasu sanadin hatsarin da sukayi".

wata irin muguwar ashar ta saki, sannan ta fara kuka tana ihu tamkar mahaukaciyar da ake shirin É—aurata aturu.

Shi kuwa yayi wucewarsa ba tare daya ce mata komi ba, sosai mutuwar nana ta girgiza kowa saboda yarinya ce me saurin shiga rai.
kiran hajiya tayi cike da tsananin tashin hankali, tana faÉ—a mata tana kuka tana cin alwashi da kuma mugayen maganganu akaina, har tana cewa itama sai ta kasheni indai har tana raye.

nan da nan aka cika asibiti, har dasu Ammi dasu Malam ban ma san wa ya faÉ—a musu ba, ni dai nasan na shaidawa ya zubar shi kaÉ—ai, amman babu wanda na faÉ—awa.

ina ganin Ammi naje na rungumeta na fashe da matsanancin kukan tausayin kaina, domin ada na ɗauka dukkanin ƙaddarorina sun yaye ashe da saura.

wata mahaukaciyar fisga naji anyomin, na juya da bala'in sauri sai naga ashe Balaraba ce, cike da haushina ta fara kaimin duka tamkar Allah ya aiko ta, ga kuma tsohon ciki ajikinta ko tunanin abinda yake cikinta bata yi, sosai ake janta tana ƙara fisgoni tana shan mugayen alkaba'i akaina, anan dai halinta ya fito don da duk lulluɓin biri takewa mutane babu wanda yasan halinta.

Sosai ran Alhaji badamasi ya ɓaci, daman mahaukaciya Zubairu ya aura haka? ya dinga tunano mugayen halayyarta lokacin tana gidansu, tana yawo daga wannan hotel ɗin sai wannan ashe ba iya karuwanci ta iya ba, har da hauka ta iya.

Duk wanda ya riƙeta sai ta fisge ta hau hauka tana dukan duk wanda ya tiƙeta ɗin, gashi ni kuma banida ƙarfin da zan kare kaina, domin ni indai har na shiga tashin hankali bana jin ƙarfi ko na sisi ajikina, saboda haka sai ta samu lagona ta dinga dukana, har ta fasamin hanci na hau Zubar da jini.

Ammina tayi kukan kura ta hankaÉ—ata gefe, sai gata akan wata kujera sannan ta nuna ta ta fara magana cikin fushi.

"ashe dama ke mahaukaciya ce jahila? wacce batasan ƙaddara ba? idan banda rashin sanin Allah ita ce ta kashe miki ƴa? idan da Allah yaso ita ɗin da kanta zai ɗauka bama ƴarki ba, idan kuma yaso sai ya ƙwashesu duka."

Hajiyarsu Ahmad tayi wuf ta ce" to mayya, aniyarki ta biki ɗana yafi ƙarfinki sannan jikarmu da kuka kashe wallahi sai munyi shari'a daku".

sosai abin ya yiwa Ammi zafi, waje fa ya É—au harami aka hau tone tone abin fa babu daÉ—i waje ya kacame.

wata irin tsawa Malam ya daka musu, nan da nan kowa ya kama bakinsa yayi shiru Malam ya fara faɗa yana ce wa" haba don Allah, nan fa asibiti ne bai kamata hakan ta faru anan ɗin ba, duk abinda zakuyi ku bari mana kuje gida kuma duk abinda ya faru rashin yarda da ƙaddara ne, da kunyi haƙuri da komai da Allah ya kawo mafita cikin sauƙi".

Harare harare aka hau yi, tsakaninsu, Ammi tayi ƙwafa ta rungumeni aƙirjinta tamkar zata mayar dani cikinta.
[2/26, 6:54 PM] Ummu Maher Ce: ➡️17
..........muna ji muna gani aka fito da gawar Nana khadija, kowa ya fashe da matsanancin kuka me wuyar fassaruwa, domin yarinyar aƙwaita da shiga rai kuma har a wannan lokacin ya Ahmad bai farfaɗo ba, abinda ya ƙara tada hankalin kowa kenan, saboda har wannan lokacin bai ko motsa ɗan yatsansa ba, ni dai tashin hankali ya haɗemin biyu, gana rashin khadija ga kuma na rashin farfaɗowar miji, wanda nayi yaƙinin indai har ya mutu nima daga ranar ƙwanan duniya ya ƙaremin, saboda ina masifar son kasancewa da mijina.

da sauri nayi kan gawar Nana, Balaraba tayi saurin riƙemin hannu tana wani yimin banzan kallo me cike da fassarori da ma'ana ta mummunar tsanar da ta yimin.
idanuwanta sukayi jawur tamkar an zuba garwashi, cike da tsana ta ce" idan hannunki ya ƙara taɓa khadija wallahi sai nayi ajalinki"!!!.

ta faɗi hakan da wani irin karsashi me amon wuta, sosai maganarta ta daki kunnen kowa ni juwa kawai sai na sunkuyar da kaina, hawaye suka zubomin na juya na fara tafiya ba tare dana san inda nake jefa ƙafata ba, kawai tafiya nake kuma bana waiwayan bayana.
dai dai wani waje naji naci karo da mutum da sauri na juyo don ganin waye?.

wani irin salati na sanya gamida ƙamewa awajen tamkar gawa, yana kallona ina kallonsa shima mamaki ya kusa durƙusar dashi awajen, yayi saurin fara magana sai dai bakinsa yana kakkarwa, masu tsaronsa sukayo kaina ganin ogansu ya fita daga hayyacinsa cikin ƙanƙanin lokaci suka fara magana" oga ko dai aƙwai matsala ne"?.
ÆŠaga musu hannu kawai yayi yana kallona, gamida cigaba da maganar daya fara furtawa sai dai a harharÉ—e take na mamakin ganina a inda bai yi zato ba.
Chapter 18 · 0% Book details