Sashe 7
Facala Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read
*** *** ***
Fulani mazugal ce kishingiɗe akan kilisar da ta saba zama, wato tumtum na falonta zaka ɗauka cewar kujera ce amman kuma tumtum ne, me matuƙar laushi da kuma kyau, Lantana ce ta shigo gamida sallama ta zube gaban uwar gijiyarta sannan ta ce" dafatan na samu uwar ɗakin na wa lafiya, Allah yajada ranki uwar gida awajen sarki me babbar masarauta, uwa ga Khadija Hajara da kuma Lubna, kaka awajen Saifullahi yayan Amatullahi".
tunda ta fara yi mata kirarin bata saki fuskarta ba, har kuma ta gama bata yi ko da murmushin wushirya ba, baƙin cikine fal acikin zuciyarta tana son faɗar abinda ke ranta amman ta kasa faɗa ɗin, aduk sanda zata faɗa sai taga kamar Lantana na iya tona mata asiri wataran, amman duk da hakan tasan Lantana ta hannun damarta ce bayan jakadiyarta Asabe, babu wani amintaccenta agidan wanda ya wuce mutanen nan guda biyu.
Fulani mazugal ta buɗe ƙasaitaccen bakinta, wangalele dashi sannan ta ce" haryanzu baki kai inda nake son ki kai ba, duk wannan kirarin abanza ya ke tunda dai ai ba nida ɗa namiji, magajo awajen me martaba duk irin ɗawainiyar danayi da me martaba amman duk yanzu na tashi atotar babu ina da yara mata da yawa dana haifar masa,amman duk abinda ya tashi sai kaji ya kira sunan tsinanannan yaron nan, me ido atsarka wanda baya ganin kowa da gashi saboda yasha nonon waccan banzar bafulatanar, wacce ta nemi hargitsamin rayuwata tabbas aƙwai ranar da sai na wargaza musu duk farin cikinsu na rayuwa, sai na hanasu jin daɗin duniya baki ɗayansu har me martaba".
Lantana ta sunkuyar da kanta, don dama can bata haɗa ido da Fulani mazugal ɗin don bata taɓa bari ka kalli idonta, ranar da kuwa ka kuskure za kaga tozarci da wulaƙanci awajenta. cike da gwanewa amunafurci ta ce" kinyi min dai dai uwar gijiyata, ai dukansu kada ki barsu amman kuma abu ɗaya ne nake son ki cire acikin waɗannan kalaman naki, waɗanda sukayi matuƙar yimin daɗi da kuma sanyani annushuwa, me martaba uban yaran ki ne uwar gijiyata kuma ko babu komi mijinki ne, saboda haka idan ran uwar ɗakin nawa ya ɓaci ayafemin ajizanci ne na ɗan adam".
wani banzan kallo ta wurgawa Lantana sannan ta ce" to ke kina ganin shi yana yimin adalci? kinsan ina sane da gonakin me martaba da kuma gidajen gonakinsa daya sanya sunan waccan yaron akai wai ya bar masa? Ni Æ´aÆ´ana ko oho ko? Saboda an haifar masa É—a namiji ni kuma ban haifa ba? to wallahi ko yana so ko baya so sai naga bayan wannan tsinanannan yaron dagashi har uwarsa".
Lantana ta ce" ah lallai kina da gaskiya, don sun aikata miki laifi mafi muni arayuwa, amman kuma idan sunsan wata ai basu san wata ba zamu biyo musu ta bayan ƙasa ne, tunda su sun nuna ƴar taurin kai ne yo in banda ƴan taurin kai meye wannan? babu irin tuggun da bamu shirya musu ba amman kuma sai kiga cikin ikon Allah sun tsallake, sai dai awannan karon ina me jan hankalinki uwar ɗakina kada muyi musu da wasa, mu zo musu ta inda basu taɓa tunani ba mu kassarasu ta inda zasu durƙushe basu san sun kai ƙasa ba".
ta girgiza kai sannan ta ce" to ni kai na ya kulle baki ɗaya, uwar gijiyata duna, tace min dole sai an zubar da jini sannan za'ayi wannan aikin, sai dai ni fa bazan iya abinda tace ɗin inyi ba don duk aikin sa zata sanyani ban taɓa yi mata musu ba, amman kuma awannan gaɓar ba zan taɓa yi mata abinda take so ɗin ba".
Da sauri Lantana ta ce" to ita kuwa me ta umarceki dashi haka? Da har kika kasa cika mata shi ba"?.
Mazugal ta karkatar da kai cike da takaici ta ce"uhm wai magana take akan jikokin da aka haifamin guda uku, aciki in bada jinin É—aya daga ciki..............
a matuƙar razane Lantaba ta kalli mazugal......
*** *** ***
Wasu mutane ne suka taho da sauri, kan motarsu Amrah wacce gaban gilashinta ya yi ƙwasa ƙwasa, aka fara kashe hayaƙin da motar ta farayi mutane da yawa suna kiran WUTA WUTA, motar ta fara kamawa da wuta, Allah ya kiyaye daga bayan motar ne daga nan aka ɓalle murfin motar aka firfito dasu, Allah ya taimaka dukkansu da aka tattaɓa jijiyar hannunsu aka samesu da ransu, nan da nan aka kira motar ƴan ƙwana ƙwana akazo aka ƙwashesu zuwa asibiti, tamkar kayan wanki wasu daga cikin waɗanda suka ƙwashesu ɗin suka bi motar asibitin da sauri don sun basu tausayi sosai.
ana kaisu asibitin aka ƙwashesu zuwa emergency saboda duk basa cikin hayyacinsu, sannan ajikinsu aƙwai inda za ayiwa tiyata, musamman ma yesmin rabin fuskarta duk ya yi dameji.
Wayoyinsu aka ɗauka don kiran wasu na kusa dasu don susan halin da ake ciki, wayar dadyn Amrah aka fara kira amman aka nuna lambar ba a amfani da ita, saboda baya ƙasar ma baki ɗaya yana ƙasar Turkey, sai aka kira lambar Hajiya Rabi.
gabanta ne ya ke ta faɗuwa, don tunda Amrah ta fita duk halin da take ciki ana bugo mata ana faɗa mata amman ahalin yanzu ɗan aiken nata bai bugo mata taji halin da ƴarta tilo take ciki ba, don tana masifar son Amrah so ba na wasa ba, don ita kaɗai ce ƴarta amman ahaka idonta bai rufe ta lalata tarbiyyar ƴarta ba, sai mahaifinta ne ke nuna mata rayuwar yahudawa da turawa, da basa ƙwaɓar yaransu duk abinda sukayi dai dai ne awajensu.
mama ta kalli ƴarta Hajiya Rabi ta ce" kiyi haƙuri ki dena wannan tunanin, in sha Allahu zata dawo gida cikin ƙoshin lafiya".
Hajiya Rabi ta cire tagumin da tayi sannan ta ce" uhm mama tunani ya zama dole inyisa, kina ganin tun ƙarfe shida ta bar gidan nan? gashi yanzu har ana ƙarfe goma bata dawo ba? haba mama zancan ƙwantar da hankali ai bai ta so ............"
dai dai lokacin maganarta ta gutsire, don kiran daya shigo mata cikin wayarta ƙaramar ƙara ce akan wayar, amman sai taji tamkar zata wuce ne da dodon kunnenta, saboda yadda take afirgice har wani zabura take tsabar damar tana cikin rikicin rayuwa.
abinda ta jine ya sanyata ɗan ɗauke wuta na wasu wucin gadi, ta saki wayar ta tarwatse aƙasa, Mama ta kalleta da sauri tana ce wa" Rabi lafiya kuwa? me ya samu Amrah ɗin? ki faɗamin mana"?.
kasa bata amsa tayi, saboda yadda cikinta ya rikice, ga wani irin amai yana taso mata da sauri ta shiga toilet ɗin dake ɗakinta ta dinga ƙwarara amai tamkar zata amayar da dukkanin abubuwan da ke cikinta.
Mama ta kasa barin wajen har sai da ta bata ruwa ta wanke bakinta, ta ɗan ɗago ta sai ta faɗa kan kafaɗar maman ta fashe da wani irin kuka me masifar tsayawa arai, ta fara magana cike da son yin maganar", mama shikkenan na rasa ƴata yanzu aka kirani aka faɗamin wai Amrah tayo hatsari ita da wata ƙawarta".
Sosai Mama ta fiddo idanuwa waje, tausayin ƴarta ya cika ta sosai itama ta fara ƙwararar da hawayen tausayin kansu ita da ƴarta da kuma jikarta...........................
*** *** ***
Sosai Ammi da Malam suka firgita, musamman da ganin ƴarsu ƙwance ahannun wani namiji yana yadda ya keso da ita, Ammi da zuciya akusa nan da nan ta maka wayar aƙasa ta rushe sa kuka ta durƙushe awajen.
Umma bata ji haushin wayarta da aka buga ba, ta tsugunna ta rungume Ammi a ƙirjinta tana ɗan buga bayanta, itama hawaye sai ɓulɓulowa suke tamkar an kunna ruwan famfo, na tausayin abinda ya samesu don wannan abun ba iya Ammi da Rabiatu ya shafa ba,hatta su ya shafesu ko ba komi Rabiatu ƴar gidance kuma jinin malam ce".
Mlm kuwa zama ya yi daɓar akan kujerar dake falon Ammi,ya rasa yadda zai fasalta abinda ke nuƙurƙusar zuciyarsa kawai sai ya sanya ɗan shawul ɗin da yake goge gumi, ya fara tsiyayar da hawayen daya manta rabon da ya yi sa, tun mutuwar mahaifiyarsa sai kuma wani abu daya yi shawagi rayuwarsu acan wani ƙarnin daya wuce shuɗaɗɗe.
Mama uwar gida kuwa ce wa tayi"oho dai ko ayanzu anyi walƙiya kowa an ganshi, saboda munafurci mu nan cewa ƴaƴanmu ake marasa tarbiyya, ashe kina da babbar mara tarbiyya aɗakin nan, in sha Allah duk masifar da ƴarki ta ɗakko akanki zata ƙare, kuma........................"
wata irin muguwar tsawa Malam ya buga mata yana nuna da manuniyarsa, ya ce" idan kika Æ™ara tofa koda kalma É—aya abakin aurenki................soonâž¡ï¸
LITTAFINA NA KUÆŠI NE, KI BIYA KI KARANTA......
Amfanin Tafarnuwa Ga Jikin Dan’adam
1.Ciwon Mara Lokacin Al’ada Idan mace tana ciwon mara ko ciwon ciki a lokacin al’ada ko jinin yarika yi mata wasa, ta samu zuma ludayi biyu
(2) ta hada da man tafarnuwa ludayi daya
(1) in an hada sai ta rika sha cokali biyu
(2) da safe biyu (2) da yamma. In Allah ya yadda zai bari.
2. Matar Da Jini Ya Ki Dauke Mata Ta rika shan man tafarnuwa babban cokali sau hudu (4) a rana. In sha’Allahu zai dauke.
3. Riga-Kafin Ciwon Nono Ga Wadda Tahaihu Ana cin dabino guda bakwi (7) a sha man tafarnuwa babban cokali sau uku (3) a rana zuwa kwana uku (3). Ana dacewa da izinin Allah in an gwada.
4. Daurewar Ciki Ko Mara Bayan Haihuwa A samu ruwa mai zafi kofi daya (1) a zuba man tafarnuwa babban cokaki daya (1) a sha so uku (3) a rana har kwana uku (3).