Sashe 19
Facala Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read
"ruhina, daman kina gidan duniya kika manta dani? me nayi miki dana cancanci wannan wahalalliyar ƙaunar? ina Ahmad? mayaudari maci amana? wanda ya kaini ya baro ni daga baya ya gudu dake ya barni da cutar zuciya"?.
Sosai jikina yake kakkarwa, sai gani aƙasa durƙushe ganin ina cikin wannan halin ne yasa ya sallami mutanen da suke tare, ya ƙaraso gare ni ya ce" Adawiyya, kema kina jin abinda nake ji ko? nine dai wanda nake ƙaunarki tun kafin ma kisan meye soyayya, wallahi tunda nake ban taɓa ƙauna da so na wata ƴa idan bake ba, don Allah ki faɗamin yadda akayi duk waɗannan abubuwan suka faru"?.
ya fara ƙoƙarin taɓa jikina.
Bansan lokacin da na aro wata jarumta nayi ba, na ture shi gefe sai dai ko gezau bai yi ba, na fashe da kuka ina tashi tsaye na ce" azzalumi mugu, maci amana in sha Allah rayuwarka ba zata taɓa albarka ba, kai ne mutum na farko daka sanya almakashi ya datsemin ƴar ƙaramar rayuwa ta, babu abinda zance da kai sai dai ince Allah yabimin haƙƙina, sannan mutumcina daka sanya ƙafa ka take Allah yayi maka abinda kayi min, tur da mutane masu kuɗi irinka marasa imani, waɗanda basu san komi ba sai cuta da kuma cin amana ya Allah ya tsinewa masu irin halin ka".
Sosai maganata ta ratsa ƙwanya da gangar jikinsa, ya rasa me ma zai ce min sai kawai naga shima ya tsugunna yana son yin hawaye ko da zai ji sanyi ajikinsa, sai dai ya kasa yin hakan saboda yadda zuciyarsa take, yana da zuciyar asalin maza saboda haka ba komi ya kewa kuka ba, duk kuwa da ƙolololuwar tashib hankalin daya ke ciki.
magana ya farayi da wata irin murya.
"Adawiyya ban zama azzalumi ba, sai dai ki tambayi Ahmad zaluncin daya aikata atsakaninmu, shiya aikata komi daya faru domin sai daga baya nasan komi, bana son tona masa asiri a idon duniya shi yasa na toshe kunnuwana, sannan na rufe wannan sirrin atsaninmu mu uku, sai dai Allah ya fimu wayo domin ayanzu haka Adawiyya aƙwai ɗanmu wanda yake da shekara uku agidan duniya, yana gidan marayu saboda gudun kunyar da ƴan uwana zasuji idan suka san komi, shiyasa na ɓoyesa acan ina zuwa in duba sa lokaci zuwa lokaci.... ............."
wani irin ihu na sanya, gamida toshe dukkanin kunnuwa na, na yi masa wani irin kallo da ya nuna tsantsar ɓacin ran dana ke ciki, na ce" dawa ka haihu? har kake faɗar muna da ɗa tsakaninmu da kai? to wallahi tun wuri ka nemo uwarsa, domin ni bazan haifi shege ba, sai dai kai ƙwarton daka saba yi wa ƴaƴan mutane fyaɗe, kana ajje ƴaƴan shegu kuma wataƙila gidanku ne aƙwai shegun, amman ka tambaya kaji mu gidanmu kaf babu shege ko shegiya".
wani murmushi yayi wanda yafi kuka ciwo, sannan ya juya bayansa yana me tsananin jin zafin maganganun dana faɗa masa, wanda ace da wanine ya faɗa masa abinda na faɗa masa ɗin da wallahi sai inda ƙarfinsa ya ƙare, domin yana da irin fushin nan nako ta ƙwana, idan ya shiga fushi bai damu da halin da zai shiga ba shi dai kawai ya isar da saƙonsa na fushi shikkenan.
"tabbas yau ne aka fara faɗamin waƙa me sanya zuciya ƙunci, nasan kinsan ke ce uwar Ayatullahi amman har kike iƙirarin ku baku da shegu agidanku kamar yadda ba kuda shi muma ba mudashi, ki tambaya adukkanin masarautarmu idan har kinji wani shege sai kiyi tutiya da kyau, sannan inason kisan wani abu wallahi indai har ina raye sai na rama abinda Ahmad yayi min, cin amanar daya aikata agareni bayan na yarda dashi, sannan ki sani bazan taɓa barinshi ba sannan kuma dole ne in mallakeki amatsayin mata, ba nida burin daya wuce in aure ki duk matar da zan aura gani nake tamkar ta rako mata duniya ne, aganina babu wata macen da ta dace da zuciya ta sai ke Adawiyya nasan kema bakiyi aure ba kamar yadda nima ban yi ba sai yanzu ne nayi, don Allah ki aure ni ko don mu gina rayuwar yaronmu".
wani irin kukan kura nayi na ƙwaɗa masa wani kyakkyawan mari, sannan na shaƙosa duk da ban kai ko rabin tsayinsa ba, amman bansan lokacin da nayi kukan kura na cafkosa ba tamkar zaki da giwa idanuwana sukayi jawur, daman ga baƙin cikin halin dana ke ciki ga kuma na wannan mugun bawan.
sosai yayi mamakin abinda nayi masa, bai kuma yi ko gezau ba ballatana in sanya ran yaji haushi sai ma wani irin kallon daya ke bina dashi tamkar wani namijin ingarma, sannan ga idanuwansa da suke da wani irin ƙwarjini irin na ƴaƴan sarauta, kai hatta kyaunsa da hasken fatarsa ababeb ƙwar jini ne, duk aman masifar da ke cini ban iya kallon idanuwansa ba na fara magana cike da gadara da tsiwa.
" ni kake mafarkin aura? to kuwa indai har kana wannan mafarkin ka farka, domin kuwa ko mutuwa nayi aka kawoni gidanka ban yafewa waɗanda suka kawo ni ɗin bw, saboda kai azzalumi ne mara imani wanda bai san annabi ya faku ba, sannan inason ka sani Ahmad ɗin da ka tsana kake ganinsa maƙiyinka, ahalin yanzu shi ne mijina kuma uban ƴaƴana in sha Allah, domin dashi na saba kuma dashi zan rayu".
ina faÉ—ar hakan na turesa gefe na tafi da sauri sauri har ina haÉ—awa da gudu na fita daga cikin asibitin baki É—aya.
gaba ɗaya ya durƙushe awajen, kansa ya fara wani irin juya masa tuni yaji yana shirin fita dags hayyacinsa, aure kuma tayi? auren ma da maƙiyinsa Ahmad? me yasa yayi masa haka ne? duk cutar dashi ɗin da yayi bai ishe saba? har sai daya haɗa da aurenta? yana masifar son ta, ko zai rasa ransa dole Ahmad ya sake ta ya aure ta, amasifar kishinsa gani yake tamkar ba zai iya barin Adawiyya ta zauna da wani namijin ba shi ba, to tun farko ma me yasa ta auri Ahmad? indai kuwa haka ne to tabbas sai ya lalata rayuwar Ahmad tamkar yadda ya yi masa..................
[2/26, 6:54 PM] Ummu Maher Ce: âž¡ï¸18
...........wata zabura yayi, ya miƙe tamkar wanda aka bugawa gangi masu gadinsa suka taho da sauri domin sunga uban gidansu ya fita kuma duk abinda ya faru akan idansu ne, hankalinsu ya tashi sosai sai dai babu yadda za suyi dashi domin tun a farko ya nuna musu baya buƙatarsu awajen.
Mamakinsu ɗaya to shi me ya haɗashi da mace balle ma har akai ga maganar mari? wannan marin ya sosa musu rai matuƙa har suna ganin muddin basu ramawa uban gidansu ba zuciyoyinsu ba zasu samu salama ba, domin Galadima mutum ne me matuƙar son mutane da taimakonsu, sannan taimakonsu ɗin da yakeyi ko ƴan uwansu na jini ba zasu yi musu hakan ba.
motar ma da kansa ya buɗe, sai dai su suka gama buɗe ƙofar saboda har da gudu suka haɗa wajen isowa wajen da yake hannayensa har haɗewa suke saboda tsananin ɓacin rai, shi kaɗai yasan yadda yake ji acikin jinin jikinsa ga wani irin zazzaɓin daya lulluɓesa acikin lokacin da bai wuce minti biyar ba.
gudu suke yi akan titi tamkar zasu bar ƙasar baki ɗaya, da yake titi ne irin na masu kuɗi duk G. R .A kafin kace me sai gasu a babbar masarauta.
Ko kafin su fito tuni ya fito ya wuce da wani irin mugun ɓacin daya kasa banbance awata duniyar ma yake baki ɗaya, hankalinsa da nutsuwarsa duk basa jikinsa.
lokacin daya ƙaraso Autar mamma ta dawo daga makaranta, sai taga yayi asalin ɓangarensa bana matarsa ba da sauri ta shiga motarta ta ƙarasa ɓangaren aminiyarta kuma matar yayanta wato Hafsy.
a falo ta same ta da bayinta, suna tayi mata tausa ahankali tamkar wata ƙwai ko jaririya sai lumshe ido take cike da matsuwa akan wani muradin da ta san ba lallai ta same saba, sannan ta gama sanyawa ranta yaya Galadima ba zai taɓa sonta ba saboda baya nuna mata ko da kulawa balle daga hakan azarcewa so.
bata ma bi takan bayin ba ta É—akawa hafsy duka akan cinyarta, tayi firgigit gamida buÉ—e idanuwanta kan baiwarta Hadiyatu ta fara zazzaga mata masifa har zata wanke ta da maruka, wai ita ce ta É—aka mata duka.
sai da ta ƙara jin wani dukan, sai taga ba hannun Hadiyatu ɗin ne ba.
sai ta kalli inda take tunanin daga nan dukan ya iso, ta ce" haba auta wannan wani irin wulaƙanci ne? agaban bayina ki hau duka na"?.
Auta ta galla mata harara tana me harɗe hannayenta a ƙirjinta sannan ta ce" to sai me? su tashi su fita mana".
sum sum suka fice kowacce tana haÉ—a kai da Æ´ar uwarta , suna gulmar autar momma wai gwara da ta dake ta daman suna jin haushinta saboda Hafsa macece me masifa sannan ta tsani talakawa ganinsu take tamkar su ba komi bane su.
" yanzu ke kina nan kina zaune, mijinki yana cikin damuwa amman ko ajikinki? ke kina nan kina hutarwaki ma? haba Hafsa ita fa mace me son ta zama done gaban mijinta itace me kula da dukkanin wani motsinsa da kuma kula da dukiyarsa, amman ke kullum sai dai ki ƙwanta ki baje bayi suna miki tausa"?.
hafsa ta buga tsaki me ɗan ƙarfi sannan ta ce"oh so kike in zame masa me gadi? haba besty wai me yasa kike da son kai ne tsakanina da yayanki? duk abinda zan masa awajenki ban iya ba? don Allah kiyi min uzuri mana, yayanki fa baya sona baya kuma son ganina kusa dashi, to me zanyi masa ni kuwa in burgesa"?.
sai ta fashe da kuka alamun abin yana dukan zuciyarta.