← Book details Facala Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 21

Sashe 1

Facala Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

[2/26, 6:53 PM] Ummu Maher Ce: _UMMU MAHER(MRS GREEN)_
https://arewabooks.com/book?id=6582a28d4ede3c5852b6cb60

*_SABAYA KAYAN MATA🥰_*
ko kunsan sabaya na gyara jiki🗣️ta ciko miki da ni',imarki a matsayinki na ƴa mace🗣️in har kika rasa ni'ima to tabbas kin zama saura🗣️🗣️na ce ba? kin haihu kinƙi ki koma dai dai? to wallahi ga sabaya zata gyaraki ciki da waje,ta matseki ta dawo miki da martabarki,ita sabaya bata cutarwa ko kaɗan sabida ƴaƴan itatuwa ce herberls.tana ciko da mama yayi kyau sosai.
08067329607.

*FACALA*

*TAKU NA BIYU*
PART TWO.
page 1

........sosai na waro manyan idanuwana, na fashe da wani irin marayan kuka, Ahmad ya cukumo likitan ya haÉ—ashi da garu yana ce wa" kai kuwa kasan abinda kake faÉ—a? matar tawa ce take da ciki? cikin ma har na wata huÉ—u? Allah ya tsine maka albarka kuma wallahi sai na yi reporting É—in ka".

ni dai kasa magana na yi, saboda yadda kai na yake masifar juyamin yaya Zubair ya yi saurin zuwa ya ɓanɓare hannun Ahmad daga wuyar likitan shi kuwa sai maida numfashi ya ke, tamkar dai wanda ya yi yaƙi a filin daga ya koma gefe yana gyara wuyan rigarsa, Ahmad kuwa sai huci ya ke kamar tsohon zakin daya gaji da cin nama.
Yaya zubair ya ce"wai ba kada hankaline Ahmad? ace matarka na da ciki amman madadin kayi murna sai kuma ka tadawa mutane hankali? ashe haryanzu baka daina wannan haukan ba?". ya faÉ—i hakan yana huci tamkar namijin zaki.

nima kukan nake banida kuma niyyar dainawa, tamkar wacce aka aiko mata da mala'ikan mutuwa, ya juyo wajena cike da haushina ya ce"ke ma taya mijin naki baƙin ciki kike? dama bakusan haihuwar shi ne kuma kuka samar da cikin? gaskiya na daɗe banga sakarkaru ba sai yau, amman ace mutane ku samu abin murna sai kuma ku hau kuka? Ashe ba banza ba Allah ya hanaku samun ɗan, tunda baku san yaron."

ya faɗi hakan cikin haushi ya fito waje, don ba zai iya ko kallon waɗannan sakarkarun ba, shi babu wanda ma yafi bashi haushi irin Rabiatu, to in banda shasha wa yake biyewa namiji idan baya son haihuwa, zai iya yiwuwa ma can ƙwayoyim haihuwar ya ke sha shiyasa bata samu cikin ba.

likitan kuwa tuni ya harzuƙa ya kalli Ahmad ya ce" idan kunsan baƙwa son cikin ai bai kamata ku samar dashi ba,Mtsss " ya yi tsaki sannan ya fita cikin som salon kare kansa.

yana fita ya ƙaraso gareni sannan ya ce" Rabiatu yaushe kika canja hali? ban sanki da biye biye ba, ya akayi yanzu na kamaki da hakan? Bayan kinsan rabona dake mun daɗe bama wata biyar ba, ballantana ayi tunanin lokacin ya shiga".

a matuƙar harzuƙe na ce" ban sani ba Ahmad, ban sani ba ko aruwa nasha ko kuma likitan ne ya faɗa don yaji daɗin bakinsa, oho amman nima bansan duk yadda akayi hakan ya faru ba, sannan kai da kake zargina da gantali kai ka manta abinda kayi ne? kada ka manta Ahmad kasha zuwa gadon barcina na sunnah, ka yimin hira da mace sannan kasha dawomin gidana da ƙamshin daba dashi ka fita ba, sannan bayan hakan har jambaki nasha gani abayan rigarka, alamar macece tayi maka kiss na taɓa faɗa maka ko waninka? ban taɓa faɗa maka ba ko kuma waninka, saboda dai duk in kare haƙƙin aure, amman rana tsaka yanzu ni sai in fara saboda kai kana yi?".

mugun bugu ya kaiwa bakina, sannan ya fara magana da kakkausar murya me cike da amo, yadda kowa ma zai iya juyoshi shi bai damu ba ya ce" daman ai can ke lala tacciyar ce? domin kuwa ke kika nunamin hanyar har nima na fara bnta, saboda haka kije ki nemo uban cikinki amman ni ba ni bane, sannan kada kiyi tunanin zan sakeki bazan taɓa sakinki ba, amman wallahi kina raye da numfashinki zanyi auren huce takaici don bazan iya zama dake kina musgunawa rayuwata ba, don kinga ina mararinki da son ki tunda ba ke kaɗai ce mace ba".

yana faɗar hakan ya fice tamkar ƙububuwa, na kalli bayan Ahmad ina wani irin tunani, da tunano wani lamari daya faru inason yin kuka amman na kasayi, saboda ahalin yanzu zuciyata ta bushe sosai ji nake tamkar in kashe kai na, amman da yake bakine na ƴar musulmi wacce ta taso acikin som Allah da manzonsa, sai na fara kiran sunan Allah, na kasa ko da faɗawa Ammi saboda wannan abin ba abune na daɗi da zan faɗa mata ba, na rasa dai inda zan sanya kai na saboda tashin hankalin halin dana shiga.

Balaraba na tsaye abakin ɗakin da aka ƙwantar dani, tayi tsaye da ƙaton cikinta hannunta ɗaya yana kan ƙugunta tana murmushin mgunta, ta kalli yaya Zubair ta ce" to ai wanman shashancin banza ne, ta yaya Allah zai baka wannan babbar kyautar kace wai kai baka so, gaskiyar magana dukkansu basu yiwa kansu adalci ba, cikin nan da suke ta nema kuma sai yanzu Allah ya yi,ai bai kamata su butulcewa Allah ba".

ta faÉ—i hakan cikin salon mugunta da kuma nuna tausayi duk alokaci É—aya.
Zubair ya ce"tashi mu tafi don ni wallahi bazan iya zama a asibitin nan ba".
Tuni ya tashi zai tafi sai ga Ahmad ma ya fito a mugun fusace.
Balaraba ta ƙunshe dariyarta, sannan ta matsa kusa da Ahmad ta ce"haba ƙanina me kumw nakeji haka? ya za'ayi ku da kuke neman abu kun samu rana tsaka kuzo kuna sa'insa har haka"?.
Ahmad ya ce" muje can gda idan mukaje zan yi muku bayanin duk abinda ke faruwa".
cikin makirci ta ce"to ita ƙanwar tawa an sallameta ne"?.
Wani kallo ya wurga mata har sai da ƴaƴan hanjinta suka kaɗa, sannan ya ce" ku taho mu tafi don minti ɗaya idan na ƙarayi awajen nan zai iya sanya zuciyata bugawa".

babu shiri taja bakinta tayi shiru, ta ce azuciyarta oh Balaraba garin munafunci zaki janyowa kanki masifa".
Yaya Zubair kuwa tuni yayi gaba, saboda ko da basu tafi da Rabiatun ba bai damu ba tunda da ya É—auketa me hankali ashe ba me hankalin bace.

wata likitace ta shigo ɗakin da nake ɗauke da takardu a hannunta ta ce"baiwar Allah ba an sallame ki bane".? ta faɗi hakan da ɗan ƙarfi don na jiyo sosai don na tsunduma cikin tunani, da sauri na kalleta ba tare dana ce komi ba, sannan na tashi na sanya hijabina na kama hanya zan tafi sai kuwa ta ce" baiwar Allah kada ki tafi kina cikin wannan damuwar, don na lura ko inda kike sanya ƙafarki baki sani ba, kawai dai tafiya kike yi ba tare da kinsan inda kike jefa ƙafar ba".
ban san ya akayi ba sai naji wani irin jiri nake ji, kaina ya fara juyamin ina ganinta tana magana amman na kasa maida mata saboda nauyin kaina dana keji gamida jiri da kuma hajijiya".

da sauri ta ƙaraso inda nake, ta ɗagoni da sauri ta ƙwantar dani, ta ɗan ɗebo ruwa tana watsamin afuskata ahankali cike da kulawa ta ce"sannu baiwar Allah, amman don Allah me yake faruwa ne? tunda naga ke kaɗai na tarar anan".?

bayan na dawo hayyacina na faÉ—a mata duk abinda ya faru, tun daga farkon abinda ya kawoni asibiti har zuwa yanzu.
ta ɗan kalleni cikin tausayi ta ce"baiwar Allah abu ɗaya da zan faɗa miki amatsayin shawara shi ne kiyi haƙuri, sannan ki koyi haƙuri wajen ɓoyewa iyayenki duk damuwar da kike ciki,tunda kin daga gani kina son mijinki ni ɗinnan haƙurin dana kasayi kenan agidan mijina, har mukazo yanzu yana biyoni gidana da yake ni ba ƴar nan garin bace ni ƴar garin bauchi ce, to amman ba nida ko ɗa ɗaya dashi ahalin yanzu, biyo bayan ɓarin dana yi abaya sai ya zamanto daga baya ko samun ma bana yi, saboda likitoci sun tabbatarmin ba zan ƙara haihuwa ba, wannan maganar ita ta ƙara tunzura zuciyata saboda mijina mutum ne me takura sosai, ko da farko likitoci sun bamu shawara amman yayi fatali da ita, sannan mahaifiyarsa macece me mugun kishi da ɗanta, duk abinda ya siyamin ko ni na siya sai kiji tana ce wa na gama mata da ɗanta, wannan damuwar ta haɗu ta yimin yawa saboda haka na takura masa akan sai ya sake ni, shima zuciya ta ɗebe shi ya yankamin har saki uku".

cike da tausayinta na ce" amman yanzu kin koma wajen iyayenki"?.
tambayar tawa sai naga kamar ta ƙona mata rai ne, sai ta ce"uhm ke dai ayi sha'ani wai ɗan birni ya cuci na ƙauye, amman ba zancan komawa wajen iyaye na saboda tunda na kira Babana na faɗa masa ce wa yayi kada in sake in komo masa gida don bai da wajen ajje bazawara, duk abinda Aminu yayi min arayuwa amman na tubure sai ya sakeni, saboda haka inje duk inda zan shiga in shiga shi babu ruwansa da ni".

sosai naji tausayinta, don ayadda take faÉ—amin maganar kana kallon fuskarta kasan tana tsananin kewar wasu abubuwa waÉ—anda ta kasa samu.

ta bani lambar wayarta ko zan kirata nima na bata tawa sannan na taso na fito, ko kuÉ—in motar da zan shiga ma ba nidashi haka na dinga tafiya kusan awa biyu akan hanya, ina cikin tafiyar naji hon abayana na juya da sauri don ganin ko waye?.
da sauri na waro ido ganin Anty Tahira, oganmu ta wajen aikin decoration da kuma ƙwalliya.
da murna ta na gaidata, sai kallona take yadda nayi wurjanjan dani ƙafafuna sunyi butu butu tamkar wacce aka ciro cikin ƙasa, ɗan ƙwalina ahannu mayafina sai saɓulewa yake,ga bakina abushe ga wani irin baƙi danayi daga jiya zuwa yau kawai.

tuni na hango tausayina fal zuciyarta ta ce"Adawiyya ina zakije ne haka? ga rana gashi kuma naga duk kin canja kamar ba ke ba"?.
Chapter 1 · 0% Book details