← Book details Dr Mahishi Meerah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 26

Sashe 19

Dr Mahishi Meerah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

To kufuto da ita ba jimawa sai gasu ruke da ita kan kushin suka zaunar da ita dukansu ita suka zubama ido duk tarame taqara fari sai dan siririn hancinta da manya idanunta da suka qara fitowa

Moohan jiyayi kamar yaje ya rungumeta dr kasa hakuri yayi sai da yaje wajan ta dafata yayi yana fadin sabry sannu

Hajiya narim ta dube shi tace kyaleta dan bata cikin hayacinta yanzu bata masan inda kanta yake ba

Saboda maganinda aka shaqamata

Da ba ai mata shakeba da ba Mai iya ruketa wajannan

To Alhmdull yanzu zamuyi abinda ya kawoku

Tayi duba ga yarta sister daukoman darduma da turare yes mah

Da sauri tanufi aiken Innarta

Shinfida mata sallaya tayi sannan ta bata turaren ta fesa tare da bude alqur'ani mai girma salati ga Annabi tayi sannan ta cigaba da sauran dukkan aduoin ta sai tabudo suratul jinnu ta karanta

Tana cikin karatun tafara hamma kowa yayi tsi ita kawai suke kallo

Zuwa can tayi gyatsa mai karfi tare dayin sallama agaresu wata murya ce sukaji wadda ba tata ba

Muryar na miji cikin sanyin shi yayi masu sallama suka amsa

Baki muna maku barka da zuwa Muhammad meerah da kaida iyalanka da fatan kunzo lafiya Ahmat meera naji dadin zuwanka dan zuwan da kai ya dace

Meera ya amsa da sunzo lafiya yana mai jinjina kai lallai jinnu gaskiya ne

Da farko dai ni sunana Alhaji malam aikinmu shine taimakon aluma daga cikin irin baiwar da Allah yabamu

Kuma cikin ikon Allah da nufin shi da yardarshi Ana dacewa

Dafarko dai sabarina sihiri ne ke damunta tare kuma da turan miyagun Aljannu da aka turo mata haka shima dr yana tattare dana shi sihirin su duka biyun an masune dan hanasu zama lafiya aman insha Allahu komai yazo karshe za'a basu magani da Ayoyin Allah kuma jinnun zasu barta yauyau dinnan

Sannan ka'idar aikinmu shine mai'dama kura aniyarta ma'ana dukkan wanda yai masu aikin to zai komamshi wanan shine ka'idarmu

Ahamt cikin shi sai murdawa yake duk sanyin A'Cn dake wajan aman sai zufa yake jiyake kamar ya tashi ya gudu

Sannan yanzu maryam zata qarayi maku karin bayani duk wanda yayi aikin zakujishi abakinta na barku lafiya

Ajiyar zuciya suka sauke sai mamaki da Al'ajabi suke basu gama mamakin suba sukaji wata murya ta macce ta rangada masu sallama

Ansa sallamar sukuyi to masha Allahu bakinmu sassannuku da zuwa Adda tace yauwa

To sunana yar mero masha sugar

Ke sister kawo man tiyar sugar yau ranar tonan sililice

Yes mero

Yar mero tatabe baki tace uwar kilbibi

Sugar ta kawo mata mai yawan gaske sai shan abinta take harda rufe ido da tandar yatsa

Sannan tace kuyi hakuyi idan na biyema zakinnan bani abinda ya kawo mu

To sabarina insha Allahu sauki yazo ita da kanta zata fara nuna maku aya kafin ni nace wani abu wajan sabry ta nufa da garin magani ta shaqa mata zuwa can sabry tayi atishawa ta bude ido

To zali tayi da Ahmat aiko tayo cikin shi tana shaqe shi tana fadin aljani aljani sai dukan shi take ta KO ina baji ba gani duk kokarinsu na kama ta suka kasa meera yace haba maryam ya haka naga tana dukan dan uwana miye mata

Yar meero ta cika baki da sugar sai da ta shanye sannan ta bushe dadariya tace meera kenan ai dan uwanka ba mutumen kirki bane shiko yayi Abin duka kara taci ubanshi

Sai tama shege jinajina sannan narabasu

Ah moohan kayi hakuri kaji ubanka dan iskane qara a koya mashi hankali kafin kuji miya aikata

Koma miyayi dan uwanane maryam ina neman Alfarma da ta kyaleshi karta illata shi to shikenan sister zaunar da ita yes mero sister ta zaunar da ita sunyi mamakin yanda ta kwace daga hannun Ahmat

To kubar mamaki dan sister ba karfin ta bane tana tare da manya

Ahmat yaji jiki ba kafan ba sai muzurrai yake

Ahmat yanzu ka kyauta na kuntatama dan uwanka da cin Amanshi shi yana zaune da kai da zuciya daya da gaskiya da Aman aman kai burunka ganin bayan shi

Samun Dan uwa irin meera a wannan lokacin sai antona

Kayi makirci kayi sihirin dan gani duk ka to zarta dan uwanka aman Allah bai baka iko ba saboda shi meera ya ruke Allah shiyasa Allah ya isar mashi

Kaga bacci gareshi shine a koma sihirinka ga dan shi mai tsananin son mahaifin shi dagani kyautata mashi kayi sihiri kasa ya bujera ubanshi lokacin da yake bukatarshk kayi nasara sa da ya kunyata ubanshi a bainar jama'a lallai kayi nasara

Baka tsayanan ba ka shiga ka fita karaba tsakanin masoya biyu masu matukar kaunar junansu dasa tsana da kiyayya atsakanin su kaso ace basu auri juna ba

Sai kuma Allah yanufa

Duk da haka baka gyalesu ba katura masu jinnu dan hanasu rayuwar aure cikin jindadi ka cutar dasu Aman kasani da kai da bokanka duk sai kun karbi hukunci

Dr matar da ka Aura bada sanin iyayenka shima ba laifinka bane duk baka cikin hayacinka kake komai sannan itama tama matar taka sihiri dan tarabaku

Ita aniyarta zata koma mata

Dr nawaz kanshi ya kulle shifa bai fahimci komai ba shin wacece matar dr din ba dai babyn shi shin daman matar dr ce shine bai fada mashi ba

Yayinda Ahmat fitsari kemashi tsiyaya na kunyar duniya

More comments more typing
Ammyn khairat
[9/5, 13:19] Ammyn Khairat: PROFICIENT
WRITERS ASSOCIATION

💉💉💉💉💉*Dr *MAHISHI MEERA*

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.come m/pro__writers?s=09

*UHMM!!! Wai miya sa sis feenat kuke mani hakane?sis aysha alto maza ki jawo mani sarauni da shalele, aunty hanne maza rike mani su ni zan fara*,

*Tirkashi*

*Rigi-rigi babban dahuwa, mai karya itacen yaro. In kaji tambari sai sarki, in kaji jiniya sai gwamna. Biki na farar kaza, balbela ba gaiya ba.*

Ina kuke? Masoyan *PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION.*
Kungiyar da Ta tara kwararrun marubuta, masu aiki da basira da hazaƙa.marubuta ne wadan da suka san kan alkalami, yayinda suka karanci matsalalon da duniyarmu ta yanzu ke ciki, basu tsaya a nanba, saida suka zaƙulo maganin matsalalon. kai baki bazai iya baku labari ba, sai dai ku kasance tare da mu, bayan kun antaya shafin mu na Facebook .👇🏾

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

*Proficient writers association*

*Uhmm lallai!!!, ummu najma ki dena rawan kai,ke nuseey, ina ki ke,wallahi kija da baya, ammiyn khairat, sis khadeeja haydar ku kamo mani su, tirkashi!!! Ashe yaya indabo da yayah sadiq suna neman riga na, bari ku gani*,

🤭Ap. Na manta ban fada muku ba masoya. Wannan kungiyar mai haɗin kai, da zaman lafiya, Uwa Uba soyayyar gaskiya da amana, sun shirya tsaf domin kawo muku Audio ɗin littaffan kunyigiyar gaba ɗaya. Bisa Youtube channe namu.👇🏾

https://m.youtube.com/channel/UCa6VZD_0ZlXycCLTT1i-ygQ

*Proficient writers association*

*RUkayya ikra ya naga kina ta ɗaga hannu ne!?bari kawai!! sia shamsiyya da sa'a datu naga suna gyan gyaɗi, shine zan taɓasu karda abarsu abaya,*

*Muna maraba da ku masoyan duk ku antayo, domin, muna alfahari daku😍 ta kuce ta muce,*

~Mu kafta~🤾🏻‍♀️

SOCIAL GIFT TO👇🏻

*RUKAYYA MY BLOOD*

And
*SARAUNIYA BEELAT*

A'A INDABO
*SADEEK*
Umman NAJMA
*sis AISHA ALOTO*
Sis FEENAE
*sis Shalele*
Nuseer
And
*young novelis*
Pagen na kune

Ammyn khairat nayiku
*over*

Masoyana fans. Dina yan olly commented group
*ina Alfahari daku sosai*

Group dr mahishi
*ina yanku irin sosai dinnan*

*PAGE 43*

________________direct Hospital din kudi suka nufa da shi ba bata time. Emajancy aka. Kar6e shi cikin gaggawa. Ayi. Mashi duk abinda ya. Dace. Sosai yasamu. Raunuka ajiki kwankwason shi ya kare da hannu guda da kafa. Gashi. Kanshi yayi muguwar buguwa dolle. Ka tausaya mashi idan ka ganshi dan yana cikin wani hali kwatakwata bai son inda kanshi yake ba

Hankalin meera yayi mugun tashi sosai ya tausayaw halin da dan uwanshi yake ciki rayuwa kenan idan zaka gidan raman mugunta ginashi sannu sannu

Yanzu wa gari ya waya

Bayan tson wani time Doctors suka fito suka rubuta magunguna da sauran abubuwan bukata an samashi drip da Allurar bacci

Moohan duk ya fita hayacin shi,

Sune basu samu kansu ba sai wajan Azahar sannan duk anyi clearly din komai sukayi sallah

Alhj nurem ya koma gida ya kawo masu lunch

Meera sai godiya yake ga nurem dan kuwa yaga kirkin nurem ba kadan ba

Bayan sallah isha'i meera ya umarce su da su koma gida su huta subar shi da dan uwanshi

Haka ko akayi daman Dr hankalinshi naga rabin ranshi daurewa kade yake ama duk wani motsi da zashiyi da tunaninta manne a zuciyarshi

KO da suka isa gida masaukin su suka nufa Dr ya shiga wanka bayan ya fito dr nawaz yashiga karshe moohan shima yashiga

An cikasu da kayan abinci wanda mai'aikin gidan ta kawo masu sun zuba sunaci dr kuma rabi hankalishi naga sanyin idaniyarshi

Karshe ture pilat din abincin yayi ya tashi dan ba zai iya hakurin rashin ta ba

Cikin gidan ya nufa parlour gidan inda suka zauna dazun

Sallama yayi bai jira isoba ya shiga suna zaune su ukku suyin wanka ko waccen su naji da kanta wajan kyau hira suke wadda bakajin me suke cewa sai dai murmushin su sallamarshi ce tasasu dago kansu zuwa duban shi

Masha Allahu Alhmdull sabry dita ta samu lafiya baya ganin kowa sai ita domin ita tafi cika mashi ido yayinda kowa da abinda ke ranshi cikin yan matan wajansu ya nufo sabry na ganin shi tatashi tsaye bai damu da kowa ba dan baima ganin kowan idan ba ita ba rungumeta yayi tare da sauke ajiyar zuciya wanda duk wanda ke wajan yaji hakan itama ta sauke tata ajiyar zuciyar najin masoyinta jikinta

Ya jima rungume da ita wanda ita kunya mutanan dake wajan ya hanata mai da mashi martani sai fikifiki da ido take kunya duk ta cikamata zuciya

Dan sakinta yayi yayi tsaye ya zuba mata ido tsawon wani lokaci sannan ya sake fizgota jikinshi da karfi yaimata wata irin runguma ya dannata jikinshi harsaida kakkasan jikinta sukayi kara tace washhhhhh da karfi sannan ya sassauta rungumar da yayi mata
Chapter 19 · 0% Book details