← Book details Dr Mahishi Meerah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 26

Sashe 18

Dr Mahishi Meerah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dr nawaz duk kishi ya kama shi jiyake ina mashine take bisa cinyarshi sai kallonta yake yana kishin dr

Wasu yan matane masu kama da juna zuqazuqa masu shegen kyau kamarsu guda ba wani babbanci hakama kayansu iri guda babu wani abunda ya babbanta su

Sai kamshi suke na hadaddan turare

Salam sukayi masu cikin muryasu mai shegen dadi hannuwansu dauke da abubuwan motsa baki sannnunku da zuwa ya hanya ya kuma maijiki

Dr mahishi ya dago kanshi dajin wanan muryoyi masu dadi sai da gaban shi ya fadi dukansu su suka zubama ido suna kallonsu dr nawaz sai yaba kyansu da kamarsu yake maganar gaskiya sun birge su

Yauwa dr ya fada tare da dauke kanshi da barin kallon su

Komai sun zuba masu yayinda daya ta zubama dr ido Dr ya hadu sosai zuciyarta sai buwatake kuma take taji wani canji cikin ranta

Fatanta Allah yasa marar lfy ba matar shi bace

Wata hamshakiyar macce ta shigo itada Alhji nurem taci ado da kwalliya sosai take maka da yaran da suka shigo

Suna ruge da hannun juna

Hajiya Narim kenan mata ga Alhji nurem masoya na Asali da sukayi rayuwa mai ban mamaki da ban tause

A cikin litafin

*GAMO DA KATAR YAR MAKAFI*

Wadanda suka karanta gamo da katar sunji yanda rayuwar su ta kasance

Cikin girmamawa su dr suka gaishe da ita ta amsa masu fuska asake

Suka zauna tace ya kamata kuci wani abuko oky thank u ruwa kawai suka sha ta kalli yaranta taimasu nuni da hannu suka tashi suka kwashe kayan da suka kawo masu suka maida masu dakin baki

Sannan suka dawo suka zauna hajiya narim wadda yaranta kece mata Inna ba wai dan kauyanci bane ko wani yasa suke cema Inna a a dan tunawa da Inna wadda tataka rawar gani ga rayuwar narim

A cikin gamo da katar

Sister ya kamata kiyi wannan aiki kinji kinga ban jima dayin wani aikin ba cikin shagwaba tace Kai Inna dan Allah kima su wallahi Inna wahala nake duk lokacin da nayi wannan aikin

To kina yarinyarki harkinsa wahala ni tun kafin na kai kamarki nake wannan aikin ke wahalar mi suka baki

Yar uwarta tace wallahi niko kinga Inna wanan aikin naku har birgeni yake naso ace ninayo wannan gado nake koba komai kana samun lada mai tarin yawa cinda kana ceton rai aman da ance sister tayi ai sai bakin rai hummm siso kenan dan bakisan irin wahalar da mutum kesha ba idan ya gama aiki sai nayi sati ina ciwon jiki kuskure kadan zakayi kuma kaji ajikinka dan maryam ba mutuncine da ita Inna tace ai tana jinki duk abinda kike fada ifa hakane nayi shuru

Human ni dai naso ace ninayi wannan gado Alhji Nurem yace qyalesu yar baba kara da bakiyi wannan gado na aljannuba

Kara da kika biyu ni duk fadin lagos babu macce kamarki a fannin zane ko wanne irine babu kamarki dan yanzu duk kinfini iyawa kin kwace komai kin tuna baindiyennan cewa yayi ke yake so ki zana mashi wani kamfani nashi
Eh hakane

Dady kowa da irin baiwar da Allah yabashi to kin gani barta ita tabi gadon uwa ke kuma kinbi na uba

Su dai su dr sun zama yan kallo yayinda kuma dr hirarsu tafara bashi haushi na sunki duba mashi sabry dinshi

Alhji nurem yayi gyaran murya ya gabatar masu da iyalin shi gare su inda ya sheda masu yaran shi gasunan yan ukku ne biyu mata na miji guda bashinan yana wajan aiki

Kama sheda masu Guda tayi gadon uwarta wajan bada magunguna guda kuma tabiyo shi

Suka jinjina kai da fatan Alkairi

Hajiya narim tace to shikenan bara ne mata aikin aman aikin bazai yoyuba cinda bacci take dolle sai sadda tatashi

Yanzu ta kai wanne lokaci bata tashi ba dr yace gasky sai ta kai Asuba oky to ba zaiyuyu yauwo ai mata aikinba sai dai zuwa gobe sai kabarta anan har zuwa safe kuje masauki ku huta kuci abinci to mun gode

Sister kai su masauki yes mam sister ta tashi dr nawaz na tsaye yana jiran dr yatashi aman yaki tashi Ahj nurem yace dr ya dai dr ya dago ya dube hjiy narima yace ba zaiyuyu muje masaukin da itaba idan na barta nan bazan taba samun natsuwa ba idan ban ganinta

Yan biyu suka saki baki suna kallon shi hajiya narima tayi murmushi tace hakuri zakayi kabarta anan da akwai abinda zan mata kafin tatashi cikin sanyi jiki ya tashi ya barta yana tafiya yana wayewayenta

Bayan ta
Kaisu masauki ta dawo ita dai dr mahish ya mata sosai

Dr MAHISHI wanka yayi ko takan Abinci bai biba Dr nawaz yayi yaci Abinci aman yace baici

Hankalinshi naga sabry baida kwanciyar cin abinci rabonshi da Abinci tun vanarasi

Wayarshi ya kunna bai jima da kunnata ba kiran meerah ya shigo wayarshi cikin rawarjiki ya daga tunkafin meera yayi magana dr kerero kuka

Meerah yana jinshi baice da shi komai ba saida dr yayi kuka mai isarshi sannan yayi shuru tare da gaida meera ya amsa mashi cikin kulawa wanda rabon da Dr yaji hakan tun kafin Abubuwa su lalace mashi
Su samu sabani da meera meera yace kuna inanne yanzu misa kuma kakashe wayarka misa baka shedaman halinda kuke ciki ba boye mani da kayi shine mafita Muhammad miyasa bazaka canza halinka ba ninasan lokacin da na haifi dana yaron kirki na haifa mai sona da kuma son duk abinda nake mai kuma gudun baccin raina wanda baya boye mani komai duk abinda yashafe shi yana sanar dani bashida abokin shawara da yawuce mahaifin shi

Aman tun lokacin da naraba dana da gida da kaishi wata duniyar dan cigabn rayuwarshi sai aka canza mashi mai makon yaci gaba sai yaci baya nayi da nasani matuqa da da turaka can danayi da nannabarka kusa dani da abubuwa sunzo mani da sauki

Aman komai Allah yashiryaka Allah yasa kagane Allah ya karkato da hankalinka wajanmu

Yanzu ina diyata wanne hali take ciki yanzu

Dr tun lokacin da meera yafara magana idanun shi ke tsiyayar da hawaye gaski meera ya fada mashi kuma bashida kamar meera shikanshi bai san Abinda ke da munshi ba ya daiga rayuwarshi ta canza lokaci guda

Cikin kuka da mutuwar jiki dr m yace Abba ka yafe man ni kaina nasan na tabka babban kuskure kuma nasan harda hakkinka ke da wainiya dani tun lokacin da na bujere maka ban sake masun kwanciyar hankaliba dai dai da sakan guda tundaga lokacin nasan hakkinka ne ke da wainiya dani Aman Abbana kasani duk abinda nayi naji kawai ina yinshine wani abunma sai nayi shi nasan nayi shi na koma da nasani aman dan girman Allah Abba ka yafe mani duk Abinda nemaka dana fili dana sarari ko na samu sassauci

Yasake fashewa da kuka meera ya share hawayan da suka zubo mashi dan sai yanzu yake nura da dr ba acikin kanshi yake komai BA da akwai shiga baga cikin lamarin

BA komai Muhammad na yafe maka duniya da lahira Allah yayafemana baki daya kadage da Adua yanzu kuna ina yajin. Sabarina

Jikinta sauki zamuce yanzu haka muna lagos gidan Alhji nurem matarsa zataimata ai to Allah yasa adace aman abar aikin sai gobe idan munzo ayi gaban mu sanan kuma naga wanne irin aikine take naga idan ba shirka cikin kan garin neman lafiya a sabawa Allah

To insha Allah Abba daman sai gobe zaa fara aikin to Allah shikaimu insha Allahu koda goma keyi mun shigo to Abba Allah ya kawoku lafiya Abban na gode Allah yasaka da alkairi Allah yaqara maka lafiya da nisan kwana Ameen

Sukayi sallama dr yayi ajiyar zuciya yaji zuciyar shi sakat kamar ancire mashi kayan nauyi yasamu natsuwa. Sosai yaji farin ciki ya mamaye mashi bakin cikin da da muwarshi

Shima can meera ajiyar zuciya yayi ya shedama su adda halin da ake ciki da gwago harda moohan sun jinjina kai yace shu shirya gobe suyi asubanci

Kuma yace da moohan ya fadama Ahmat ya shirya ayi tafiyar tare da shi da moohan ya sheda ma ubanshi dariya ya bushe da ita yace Allah shikaimu mujen miyo kallo

Tunda asuba bayan sunyi salla suka nufu katsina airport hayar jirgi suka dauka jirginsu yadaga zuwa lagos

*topa fans kubiyoni danjin wannan tonan sililin*

More comments more typing
Ammyn khairat
💉💉💉Dr MAHISHI MEERAH

Nྂaྂ

Aྂmྂmྂyྂnྂ kྂhྂaྂiྂrྂtྂ
Gྂoྂlྂdྂeྂnྂ gྂiྂrྂlྂ

Dྂeྂdྂiྂcྂaྂtྂeྂdྂ tྂoྂ mྂyྂ cྂhྂeྂrྂiྂeྂ fྂeྂeྂnྂaྂrྂ
PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09

Social gift GA yan Group dr MAHISHI

*PAGE 41*

___________8:am taimasu airport na lagos

Moohan ya kira dr mahishe ya sheda mashi sun. Iso yanzu haka suna filin jirgi. Na lagas

Cikin. Dauki dr suka shirya shida dr nawaz Alhj Nurem ya basu mota biyu da. Drive

Mintina 30 suka isa airport yau dr. Cikin farin ciki ya isa ga mahaishin ya rungume shi. Harda hawayan shi shima. Meera cikin kulawa ya rungume dan shi yana tambayar lafiyarshi

Adda sai murna take. Da shiryawar da da uba

Ahmat. Sai harare. Harare yake wajan shi dr ya nufa yana gaishe shi tare da yi mashi barka da Zuma moohan shima ya gaishe shi rabonda suga juna harsun manta

Gwagota inji dr itao gwago. Sai kauda kai take saboda alkunya ta dan farin

Aman cikin ranta murna take da ganin danta musamman yau yanda ta ganshi yana farin ciki uwa kenan

Sun shiga mota zuwa gidan alhj nurem ba jimawa suka isa hon sukayi aka bude masu murginenan get din

Falon baki akai masu masauki mintina kadan yan biyu sukacika su da breakfast da kayan motsa baki

Sai da suka dai daici sun karya sannan su Alhji nurem da iyalishi suka shigo suka gaisa a mutunce yan biyu suna
Kwashe kayan abincin Duk da bawani mai yawa sukaci ba dan meera ruwa kawai ya iyasha

Burun shi yaga yarshi shima dr abinda ke cikin ranshi kenan rabon shi da ita tunjiya

Hajiya narim tace da yaranta kuje ku tafoda ita ina ai tabar fizge fizgen ko kin sha qamata wannan maganin eh Inna
Chapter 18 · 0% Book details