← Book details Dan Minister Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 22

Sashe 9

Dan Minister Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shatuwa Tai caraf ta anshe mgnar tace au Ashe Babu Dadi Ni da ka karyawa hannufa ai kome yafaru Kaine kaja ba waniba da baka Fara tsokana taba da du Haka Bata faruba gashi Ina ji Ina gani kabarni da jinya ai ko jiyan Ni ba shi nai niyar jefaba Kai nai niyar fasawa goshi yai maza yatarema Kuma wlh har yanzu ban hakuraba se narama Kuma ga tsiyar abincin kunnan Kuma Dole aje asamo Mana Wanda muka iya ci agarinmu

Nabil yace au har yanzu bakuyi sanyiba ko Dan ban gama nunamuku irin
Kalata bako

Plet da glasscup din Kan dining table din nabil yasa hannu yafara jifansu dshi suna tsalle suna kaucewa iya du tacika wajan da ihu da masifa shatuwa da taga abin bana Kare bane itama kome tasamu jifan nabil take dshi har abincin da yake gabansu ta dauka tana jifan nabil da shi lokaci Daya suka Bata ko Ina na wajan MINISTFR mutuwar zaune yayi yakasa motsi Yana kallan ikwan Allah Amina ita gefe ta koma tana kallansu anrasa me Basu hakuri hajiya Fatima tana boye abayan labulan wajan in taji anyi ihu se ta leko kanta daga taga ana niyar jifanta satai maza ta komar da kanta nabil kofin gaban MINISTER ya dauka da ruwan shayi ciki me zafi Yana tiriri garin ya watsawa shatuwa se awuyan iya wata mahaukaciyar Kara iya tasaki Dan azaba lokaci Daya du tabi ta gigice Dan zafi ai batasan lokacin da tashige karkashin dining table ta buyaba tana mai da numfashin wahala lokaci Daya wuyan iya yatashi abinka da tsufa ruwan shayin ya Kona Mata fata sosai ta gefan wuyanta

shatuwa ganin ruwan shayin da nabil ya watsawa iya da Kuma yanda iya take ta ihu yakuma konawa shatuwa Rai batasan lokacin da Tai tsanle ta finciko karfen labulan wajan gaba daya ta rikitosu sukayi kasa se ga hajiya Fatima abayan labule tana raba Ido tana ijiran ikwan Allah shatuwa Kan nabil tayi dagudu da karfen labulan ahannuta in takai Masa duka dshi se yai tsalle ya kauce Babu zato Babu tsammani garin shatuwa ta kwadawa nabil karfen se a gadan bayan MINISTER zafin karfenne yadawo da shi daga mutuwar zaunen da yayi tin dazu Dan azaba besan lokacin da shima yashige idan iya ta buyaba sun hadu susu biyu suna jinyar in da kowa aka illata shi Dan azaba bayansa rikewa yayi Dakar ma yakai kansa in da yabuya iya da MINISTFR Baki yamutu Babu me mgn

sunbar nabil da shatuwa na fafatawa fadan yakoma na manya nabil shima samu yayi yadauki karfen labulan daya yakan shatuwa da shi dagudu Yana kokarin kwada mata bakajin komai se karar karfe awajan Dan karfin Hali na shatuwa da hannu daya take wannan rigimar Kuma dudahaka shatuwa bakinta yaki mutuwa inbanda bakaken mgn Babu abin da yake fitowa daga bakinta tana gayawa nabil shikuma Yana dada tinzira ransa nadada baci gabadaya sunhada wani uban gumi Kai ace wani uban aikin wahala aka basu su keyi

Amina da taga suna niyar jiwa junansu ciwo kuma Babu Wanda yake da niyar hakura ya dena Dakar da dabara tasamu tafita wajan baffah ta gayomasa abinda ke faruwa da sanyin safiyar Nan da sauri baffah yabiyo bayan Amina tinkan yakaraso yakejin muryar shatuwa da Kuma karar karafuna natashi shikuma muskili Nabil baajin muryarsa akwai wata kofa tabaya Amina tacewa baffah sushiga tanan Dan asamu arike Daya daga ciki suna shiga Allah yabawa Amina sa,a tarike shatuwa tabaya shikuma baffah yasamu yarike nabil tabaya

Tsawa baffah yadaka musu ya wankawa nabil Mari yace kunutsu kushiga hankalinku meyake damunku haka ko kunsamu tabin hankaline bamu saniba daga jiya zuwa yau Kai nabil meyasa kake biyewa mace Kuma matarka Dan Allah jibi yanda dukanku kuke maida numfashi kamar wayanda sukayi aikin wahala Dan Allah kukalli barnar da kukayi awajannan gaba daya kun lalata komai nawajan har falo Baku bariba abincinma gabadaya kun zubar dshi saboda Bala,inku Ina sani da iya da fatima suke suka barku Kuna wannan danyan aikin

Hajiya Fatima ce tasamu tafito daga wajan buyar da tacanja tace baffah du munanan abinne yafi karfinmu in muka tsaya ciwo zasuji Mana abanza abarmu da jinya ai yanda suka haukace dinnan ran kowa yake abace acikinsu Babu me iya raba fadannan Daman se Kai baffah Suma masu daure musu gindin sunyi takansu sun kasa rabawa baremu Yan kallo baffah Ni banma San Ina suka buyaba tinda naji ihun iya dazu ban Kara jiba inaga sunsamu sunfice suna waje abin yafi karfinsu

Muyar iya sukaji ta karkashin daining table tana fitowa da rarrafe tace kun ganmu Nan Ni da Mara mutuncinnan muna jinyar jikinmu konani da ruwan zafi mekirar zakunannan rabi mutun rabi aljani yayi daban gudu na buyaba da salibeni zeyi kamar kaza aruwan zafi gabadaya ko ya aikani lahira Babu shiri mutun amurmurde kamar samudawan farko fuska amurtuke sekace me gadin gidan wuta idanshi Dan mugunta har wani Jah da Kore suke komawa Dan masifa usuman kahada shatuwa da Bala,i rashin sani yasa na yarda ankawo jikata inda zaa kasheta nashiga uku Ni Aisha anfasa aurena billahillazi usuman kadau mataki Dan bazan yarda inaji Ina gani acutarmin da jikaba Dan Allah kaga yanda gabadaya Rabin wuyana yasale da ruwan zafin da wancan damisan yawatso min ko tsufana beganiba Dan rashin imani har da cewa ze karasa ciremin hakwaran bakina nagaba da suka rege Kuma wlh ze iya fin hakama Dan Babu tausayi da digwan imani azuciyarshi zantafi da jikata in komai yalafa sunyi hankali shi da ubansa na dawo da ita wlh inaji Ina gani bazan bar jikata akashemin itaba

MINISTER ne yafito shima Yana rike baya yace Ni bance inaji Ina gani jikarki zata kashemin yaroba Nima ta gurguntani se ke baffah kagani da idanka tin da aka kawo fitinanniyar yarinyarnan take hakona jiya kaga me tai min yauma gashi ta barni da ciwan baya Dan Allah Dan annabi baffah ka temaka kacire dokar da kasa Mana Ni da nabil ya sauwake Mata sukama gabansu su koma in da suka fito har in da muke Dan masifa muna karyawa tsohuwar Nan tazo ta samemu tahau Mana masifa Wai su tuwo da Koko da kosai suka sani Dan kauyanci tin ajiya nabil yakuma fadamin bayasan yarinyarnan ko ganinta bayaso yayi ya tsaneta karfa murasa nabil baffah kadau mataki Dan Allah

Baffah yace du kanku kunemi waje ku zauna zamuyi mgn da ku kowa Zama yayi baffah yakalli nabil Kai nabil dakai Zan Fara Dan Kaine yanzu komai yake hannunka na shatuwa zaman nan dan kai da shatuwa akeyinshi yanzu Dan Allah azamanka na mijinta abinda ka kulata kukeyi yadace kaifa yanzu girma ya kamaka ko kana so ko baka so Dole kana hakuri Akan wani abin in matarka tamaka karfa kamanta ko Babu aure sama kake da ita ka girmeta bare Kuma yanzu da take akarkashin ikwanka Dan Allah ba girmanka bane karka Kara kulata ku Kara raba abin fada haka gaban mutane da safiyar Allah yanzu girmannan da kake da shi agaban yaranka da yan aikin gidannan yanzu du kazubar dshi a idansu dakai da ubanka dalilin wanna abin kunyar da kukayi jiya da yau kaga kuwa yanda maaikatan gidannan suka taru awaje suna sauraran abin kunyar da kukeyi Kuma saboda suna tsoro ko rabawa Babu Wanda yashigo yayi kabi zabin da nai maka nabil insha Allahu zakaga alheri komai daran dadewa kaji jikana nimafa ina sanka Ina kaunarka kamar yanda sani yake sanka San da nake makane yasa na zabama matar aure da kaina Dan Allah kana hakuri da ita karka Kuma kulata Kaine babba itama Zan Mata fada se mgnar iya kakar shatuwa cefa matarka itace Kuma ta raini matarka tin tana cikin tsumma har zuwa yanzu kaga kuwa dolene ka girmamata karka Kara kulata kome tai maka kaima kakace awajanka yanzu kaga ka kona Mata wuya saboda zafin Rai irin naka Dan Allah karage zafin Rai bashi da anfani arayuwa kaji nabil Allah yai maka albarka

Kekuma shatuwa nabil mijine awajanki dolene ki bashi girma Kuma kibishi sau da kafa aure yafi karfin Wasa Babu raini tsakanin miji da Mata daga yau se yau karna karajin wani abin yafaru na fada tsakaninku Dan Allah kuji tsoran Allah ku zauna lfy kiwa mijinki biyaiya aljannarki tana karkashin kafarsa se yadaga Zaki shiga karki Kara dagawa mijinki ko da muryane bare har takai ga niyar zaku illata juna da makami yanzu kema kin girma bakamar da bane da Baki da aure tinda kike kin taba ganin babarki suwaiba da umaru suna irin abinda kukeyi daga jiya zuwa yau ko Kai nabil tin da kake kataba ganin Fatima da sani suna fada to karna karaji kun yi ku zauna lfy ku Zama abin alfahari adangi da duniya gaba daya kodan yaran da zaku Haifa gaba inma mafarki like ki farka aure dai anriga an daura Babu rabuwa mutu karaba ke da shi inma zaku koyi San junanku to ku ku koya Dole muma wasu daga cikinmu dahaka muka so namu matan shatuwa dolene ki girmama iyayan nabil wannanfa da kike gani Kika fasawa Kai jiya yau Kuma Kika kwadamai karfe abaya uban mijinkinefa karki kuma gida dayafa zakuyi rayuwa kuke haka karna karajin bakin wani daga cikinku ku tashi ku tafi nagama daku Allah yaimuku albarka Allah yabaku zaman lfy yakade fitina Amina maida shatuwa dakinta

Kafin su tafi iya ta kalli nabil tace me mugun Hali kadaiji me Wanda ya haifi ubanka yace saura kaki ji Dan Allah jibi yanda yake ta huci kamar wani mayunwacin Zaki Tai maza ta toshe bakinta au yacefa in na Kara kiranshi da wani suna ze ciremin hakwaran gaba da suka rege na bakina Wai jiya wanama suna naji kakira ubanka dshi ko miss miss kome Kai Kuma naji kace Wai kana Dan miss miss ko me usuman Daman gwaunati mukamin da tabawa danka kenan mukamin Kiran maguna miss miss Kuma naji yakira fetir Daman du uban kudinnan da yatara da mukamin kiran miss miss ya tarasu Ashe magunama na da daraja akasar Nan ban saniba dakai na kirkine sani ai da inna komawa mazagai da nasa na tarama maguna dayawa in zan dawo ganin shatuwa na tahoma da su to baka da mutunci daga Kai har danka me shigar Mata
Chapter 9 · 0% Book details