← Book details Dan Minister Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 22

Sashe 16

Dan Minister Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

baffah yafara mgn yace to Kan mgnar mu na kiraku wannan shawarar da nayanke itace mafita insha allahu Kuma za a dace Amina tinda tafiyar Taki ke da mijin naki tazo zuwa kwas,din da zejeyi america kutafi tare da shatuwa tinda shi mijin naki yace tare zaku tafi Kuma sani na da gida acan america gidan nashi zaku sauka har mijin naki yagama kwas,din da zeyi na wata shida Dan Allah ki dada kokarin da kikeyi Akan Wanda kikeyi Akan shatuwa muma anan zamuyi iya namu kokarin Kan nabil har musamu abinda mukeso awajanshi Dan shiryuwarshi itace shiryuwar sani itama shatuwa hakane Dan Haka yanzu tinda kince yau da yamma zaku tashi zuwa America kije kisa shatuwa ta shirya ki hada,mata du abinda yadace ki tafi da ita gidanki lokaci nayi se dai ku tafi ko tanan karku biyo da ita Kuma karki Bari nabil yasan kece Kika tafi da shatuwa ko iya bazata San da tafiyar jikartaba Dan hakafa na yarda muka taho da iya dan Tai sallama da shatuwa Kinga karshe ga abinda yafaru itama bazata,san shatuwa tayi tafiyaba in bahakaba komai baci zeyi yanzu Fatima takira megadin gidan nabil ta tambayeshi ko nabil nanan yace bayanan yadade da fita Danhaka sekiyi sauri kije ki dauketa Kuma ko lokacin da wowarku yayi inhar dukansu Basu shiryu yanda mukesoba baza a dawo da shatuwa ba har se munga sun koma yanda mukeso

Amina tace to baffah Amma aganinka iya bazata damekaba Akan kafito Mata da jikarta kasan halintafa da rigima

Hajiya Fatima tace Nima tinanina kenan Kuma wannan matakin da kayanke Kan nabil da shatuwa baffah shine dedai Allah yabamu sa,a ni wlh daga iya har alhaji rigimar tasu dariya take bani garama nabil da shatuwa suna da dalilan abinda yafara hadasu fada tin farko Amma iya da alhaji Basu da wani dalili alhaji nabil yake tayawa fada iya Kuma shatuwa Kuma wlh Ina guje musu ranar da nabil da shatuwa zasu shirya zasuji kunya sosai mudai muna gefe kallone namu tasa dariya

Baffah yace rabu dasu gani sukayi zasu iya Ni abin takaicima sani ne mecewa indai Akan nabil ne ze ajje mukamin minister agefe in dokuwane shi da iya su doku Allah yaganar da su gaskiya; karku damu da iya danta umaru wato mahaifin shatuwa yasan komai Akan tafiyar Kuma yabamu goyan baya akai ita,kuma iya nasan yanda Zan shawo kanta har Allah yasa shatuwa ta dawo se Naga tafitarku Amina sannan zamu koma mazaigai Ni da iya Allah yakaiku lfy ku dawo lfy maza tashi kitafi Allah yai muku albarka

Amina gidan su nabil tasa direba ya kaita tana shiga taita sallama taji shuru ta dauka ko bacci sukeyi Kai tsaye dakin shatuwa tashiga ganin halin da shatuwa take ciki ko motsin kirki Bata iyawa tana kwance abin tausayi yadagawa Amina hankali tambayarta tafara me yasameta ko nabil ne ya daketa shatuwa Babu bakin mgn se kuka shima da kyar takeyi yaye bargwan jikin shatuwa da tarufu da shi tayi ganin yanda jini yabata inda take kwance yayi mugun tada Mata hankali Dakar ta rarrashi shatuwa tafada Mata abinda yafaru tsakaninta da nabil Amina taji Dadi sosai da haka tafaru tsakaninsu kafin shatuwa tabar kasar ita taiwa shatuwa wanka ta gaggasa Mata jikinta Taji tausayin shatuwa sosai ganin barnar da nabil yai Mata ita ta gyara ko Ina na dakin har zanin gadan se da ta wankeshi a injin wanki tayi du abinda yadace sannan takama shatuwa suka fito tasata amota da kayanta suka fice asibiti tatara Kai shatuwa aka dubata sannan suka shige gidan Amina yamma nayi wajan karfe shida jirginsu yatashi zuwa America baffah da Hajiya Fatima ne suka rakasu har sukaga tafiyarsu sannan suka dawo gida

Nabil tinda yaje wajan da yake hutawa tinanin shatuwa da abinda yashiga tsakaninsu yake ta dawo mishi ko Ido yarufe abinda yafaru yake gani ga fuskar shatuwa da take ta Masa yawo a idanshi kide kiden da ke tashi awajan da wakar du yau ji yayi basa Masa Dadi tinani yafara to da yafito yabarta awannan halin waye ze temaketa in tamutufa Kuma ko bakomai ai ta dalilinta yasamu lfy jiya Kuma yaji dadin da be taba jiba Daman mata na da wannan Ni,imar Haka me Dadi har da wannan ballagazar Mara mutuncin to yanzu waye ya temaketa ko tamutu fitowata daga gida jiyayi gabansa yafadi besan lokacin da yasaki wata karaba yafara mgn kamar zararre A,A,A Bata mutuba to Wai meyasa nake tinaninta Wai meyake faruwa da nine abokansa da sauran mutanen da ke wajan kallansa suke tayi suna mamakin me yasameshi yau haka Babu me bakin tambayarsa saboda kowa yasan halinshi wajan mota yanufa da sauri ze shiga dagudu yaransa suka rufamasa baya suka bude Masa motar Yana shiga sukaja suka fice dagudu zuwa gidansa

Motar ko Gama tsayawa batayiba yabude yafito da gudu,gudu sauri,sauri yashiga gidan jiyayi gabanshi yayanke yawani mugun faduwa dakin shatuwa yashiga dagudu yaga bataciki yaje da sauri yabude bandaki yaga bakowa aciki dakin yahau kalla yaga ko Ina tsaf angyara Babu alamun mutun yakwana acikinsa kangadan yakalla yaga agyare anma canja zanin gadan gabadaya fita yayi yahau duba ko Ina nagidan nanma be gantaba dagudu yatafi wajan masu gadi Yana tambayarsu da tsawa Ina matarsa

Jiki na Bari sukahu bashi amsa Suma Basu gantaba ko fitarta Basu ganiba

Yace Babu wata ko wani Wanda yashigo gidannan bayan fitata yatafi da ita

Sukace eh yallabai Babu kowa Kuma mu bamuje ko inaba muna wajannan da wasu sun shigo da mungani

Yace wlh inhar tabata kome yasameta kunsan Allah bazan barkuba Ni dakune to meye anfaninku agidan tinda baza kuyi abinda aka daukekuba korarku zanyi yau,yau dinnan bazaku dada kwanarmin agidaba dukanku se na kulleku kuje kuyi tinani ku fitomin da ita kannaje nadawo

Gida yatafi wajan su hajiya Fatima ko sallama beyiba yabanko dagudu Yana dube dube kamar me neman wani abin daga hajiya Fatima har baffah babu wanda yai Mai mgn yisukayi kamar Basu ganshiba dakunan gidan yahau dubawa be gantaba falo yadawo wajan su baffah yazauna yakwanta Kan goguwar kujera yarike kansa yarufe Ido kamar me bacci shi yasan meyake damunsa ga wani ciwankai da zazzabi me zafi na damunsa

Baffah ne yace nabil yau ko mgn Babu bare gaisuwa Ina matar taka

Nabil besan sanda yatashi zauneba Yana kallan baffah

Baffah yace ko dai baka da lfyne

Nabil yace lfyta kalau Daman batazo nanba

Hajiya Fatima tace wacece kake tambaya

Yace aa ba mgn nayiba

Komawa yayi yakwanta

Yace mommy a Ina tsohuwar Nan ta kwana

Kafin tabashi amsa sega iya tashigo

Iya naganin nabil tace me zamanman wando Ina shatuwa ko kakuma karyata ko baka,jina Kai min shuru

Ido nabil yabude suka hada Ido da iya batasan lokacin da taja bayaba

Tace nashiga uku Ni Aisha kuga idan mutun kamar gauta ko dai kakuma balballata Ina Nan bansaniba

Tashi yayi Yana hada hanya yai dakin da iya ta kwana nanma bega shatuwa ba dakin minister yatafi ya kwanta daga yarufe Ido se yaga shatuwa gashi San ganinta yake yarasa me yasa ga zazzabi yatakura Masa se rawar sanyi yake

Hajiya Fatima ce tashigo taga halin da yake ciki tace nabil baka da lfy bayannan Kuma da abinda ke damunka ka fadamin

Yace bakomai mommy kawai dai bani da lfyne

Tace to Alllah yabaka lfy Bari na kawoma magani tafice

Mgn nabil yahauyi shikadai kamar Mara hankali to Wai Ina taje ko an sacetane to ai babu Wanda yashigo gidana Kuma anty Amina tayi tafiya baza Kuma su tafi tareba tinda kwas mijinta zeje yi Kuma ai baffah da matsifanfiyar tsohuwar Nan baza su Bari atafi da itaba to yaushema Yar Kauye irin wannan zataje America ai ko jirgi Bata iya hawaba to waima meye nawa in tabata ba na hutaba da jarabar ta da ta wannan tsohuwar to Wai meyasa nake ta ganinta in narufe Ido ko Dan ta dalilinta naji saukin ciwan marata jiya Kai nabil manta kawai macacefa Kuma nafa tsaneta Wai meyasa naje nahada jikina da ita kazama Yar Kauye irinta tsaki yajah me karfi

Hajiya Fatima ce tadawo
Bashi magani tace Kai dawa naji kana ta mgn ko dai kun dada halinne Wai Ina shatuwa ana ta tambayarka kayiwa mutane shuru

Yace tana gida na barota

Mgni tabashi yasha bacine ya kwasheshi acikin baccin Yana ta mafarkin shatuwa da Kuma garar da yasha awajanta jiya kusan rabin baccin du mafarkinta yake

Iya da baffah sun koma mazagai Dakar aka lanlabata takoma da cewa tayi se taje tayiwa shatuwa sallama Kuma akwai nasihar da ta manta batai mataba

Shatuwa bakin America Tasha jinyar barnar da nabil yai Mata se da tawarke sosai Amina tasata amakaranta saboda shatuwa na da kokari Kuma Babu lefi tana ganewa turancine ake fama da ita in anyimata Bata gane wani abin in angaya,Mata da turanci se ta dawo gida take tambayar Amina me ake nufi da kalma kaza da turanci in Amina tabata amsa to tarike kenan karatu kuwa tana ganewa tamurje tadada fari sosai in ba ka santaba bazaka gane taba Amina tayi kokari sosai wajan dada wayar da ita yanzu shatuwa tazama Yar birni Kuma Yargayu acikin wata ukun da sukayi tsokanar da akasan shatuwa da ita yanzu du babu tazama saliha kamar ba itaba yanzu Abu dayane yake damun shatuwa da Amina ta kula dashi tana yawan tinani kome take lokaci daya zatai shuru ko mgn ake Mata bazata baka amsaba Amina tayi Mata tambayar duniyarnan meke damunta se tace Babu komai

Yau Amina nazaune adaki tana shayar da yarta shatuwa tashigo ta sameta tazauna kusa da ita Amina tace yadai kanwata Naga kamar da mgn abakinki

Shatuwa tace Daman tambayarki nazo nayi Dan Allah in mutun koyaushe na yawan se Tai shuru ta sunkuyar da kai

Amina tace cigaba Mana kanwata Ina jinki meye abin Jin kunya nifa Yar uwarkice

Shatuwa tace to anty in mutun nayawan tinanin mutun mekenan kamar Wanda kasani Kuma abokin fadanka Kai tayawan tinaninsa ko in kana bacci Kai ta mafarkinsa

Amina tace kafara damuwa dashi Kenan Kuma yanzu kana sanshi kekuwa kanwata meyasa kikemin wannan tambayar ko tinanin gida da su iya kikeyi

Ido tarufe tana dariya tace to anty bayan su mommy Kuna waya da su iya dah takuma,sa dariya
Chapter 16 · 0% Book details