← Book details Dan Minister Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 22

Sashe 17

Dan Minister Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amina dariya take ta dannewa Dan tagama ganota yitayi Bata gane me take nufiba tace karasa tambayarki du Zan Baki amsa

Kuna waya da Yaya nabil

Amina tace eh to muna waya da kowa Amma nabil gaskiya ba sosaiba iyama bama waya da ita

Shatuwa tace to in kunyi waya dashi Yana tambayarki yanake ko Ina nake ko bayayi

Tace aa gaskiya bayayi Kuma ai besan na taho da keba bemasan kina nanba

Hawayene yafara zuba daga idanta
.Amina tace menai Miki kanwata ko na Bata Miki Rai ban saniba

Tace aa abinne yabani haushi Ni fa anty kullin shi nake ta tinani ko bacci nake tinaninshi nakeyi yanzufa San ganinshi nake Amma shi be tabama tambayarki ko Ina nanba Daman anty besan kin taho daniba Kuma in yashiga wani halifa Kuma fa mijinane ai bebarniba muka taho Kuma kece memin waazi Akan hakkin miji kumafa kinsan iya wlh damunshi zatayi akaina in tazo Bata ganniba

Hamdalah Amina tafara tana murna tace to akwai dalilin da yasa muka taho dake se nangaba Zaki gane me ake nufi harshi nabil din Kuma mgnar fadan da kukefa yanzu nasan muna komawa zakuci gaba da abinda kuke Kuna rabawa kanku abin kunya agaban mutane ai basan junanku kukeba Kinga kuwa ai yanzu hankalinki kema akwance yake anraboki da abokin fadanka ko

Tace aa wlh ai Ni nadena fada Kuma ko me yaimin bazan Kuma kulashiba ai kinmin fada ga Kuma waazi inaji Akan Mata tabi mijinta sau da kafa in tayi zata shiga aljanna ai shima nasan yanzu yadena gakuma iya inasan naganta anty mu koma gida Dan Allah

Amina tace to kanwata karki damu munkusa komawa insha allahu komai yazo karshe ammafa naji Dadi ashedai anasan Dankanin nawa kanwata na San mijinta tanasan ganinshi

Dariya shatuwa tasa tazuba dagudu tafice daga dakin tanajin kunya

Amina Kiran hajiya Fatima tayi awaya tabata labarin yanda sukayi da shatuwa itama hajiya Fatima tabata labirin halin da nabil yake ciki dukansu sunyi farin ciki sosai

Nabil tin Yana boye batan shatuwa yanzu yakasa boyewa gashi yazu tinani yamasa yawa har Rama yafara yarage walwalar da yakeyi da ko fita yanzu bayayi sosai se dai yaje dakin shatuwa yakwanta in Kuma yagaji da kwanciyar yatafi wajan hajiya Fatima yau wajan hajiya Fatima yaje yasamu kuwa babansa minister nanan suna hira

Da sallama yashiga zuwa yayi yafada jikin minister yafashe da kuka me karfi yace daddy Kai da mommy ku temakeni tinaninta ze kasheni wlh Santa nake na Dena du abinda bakwaso in dai za a dawomin da ita mundena fada naje na roki baffah yace bemasan da batan shatuwa ba Kuma Allah yanzu inaga dasa hannunshi yasan inda take Ni har mommy ban yarda da itaba

Minister rudewa yayi yace alhamdulillah Allah na godemaka da kabawa nabil matar da yakeso ba wannan mahau

Kafin yakarasa nabil yarufe Masa Baki

Yace karka karasa daddy wlh bazan iya jure Jin ana zagintaba wlh Ni matata ba mahaukaciya bace da hankalinta nifa daddy ba wata matar auren da nasamo matata nake nufi Wanda baffah ya auramin Dan Allah gobe muje mazagai tare mubawa baffah hakuri ya dawomin da matata har in Kuma yaki mommy ma Taki to wlh se na Nemo gidan iya masifa na fada Mata anbatar Mata da jikarta Kuma bawasu bane su baffah ne ai nasan in taji masifarta,ma kadai ta Isa su dawo da ita Dan itama tanasan jikarta sosai

Minister Baki yasaki Yana kallan nabil bemasan sanda ya sauko daga Kan kujera yazauna akasaba Baki narawa yace nabil kakuwa San mekake fada kuwa ko dai da gaske kaima kabi layin Yan shaye,shaye abokanka inkuma ba hakaba to tsohuwar Nan da jikarta sun maka wani mugun abin sun kaika an haukatama zuciya akansu shikenan baffah zamu rasa nabil ai Dole naje har gida na ci mutuncin tsohuwa iya

Nabil yace wlh daddy karma kafara inhar kana sona to karka yiwa iya komai Dan ran shatuwa ze baci intaji Kuma zata dada guduna Nima Kuma yanzu inasan iya kome zatai min bazan kulataba Nima kakatace nidai abinda nakeso da Kai ka tayani Nemo shatuwa mukuma je mubawa iya hakuri mubawa baffah hakuri mukuma bazama neman matata adu inda take aduniyarnan

MINISTER wani gumine yake ta keto Masa duda sanyin esin da ke wajan zare Ido kawai minister yake tayi Yana kallan nabil

Me hajiya Fatima zatayi inba dariyaba har da rike ciki tasaki Buda tace Allah ngdma ranar muke jira yau gashi tazo Allah karabamu da abin kunya ko wana irine Naga yanda zaayi wajan zuwa gurin iya ba da hakuri da wajan baffah da alhaji yanzu Dan Allah bakaji kunyaba tin ba a je ko inaba ai ga abinda muke ta fadamaka Ni da baffah gashi kashiga fadansu yanzu zaka dawo kaji kunya gashi dai yaro yadawo yace yanasan matarsa saura iya ita Kuma zamuga yazatayi garama ita tsohuwace akwai shiruftun tsufa Kai kuwafa ai Babu wani tsufa da kayi Allah kadawo da shatuwa lfy muyi kallo muna daga gefe yanzufa tinda kana san danka seka Rakashi neman shatuwa da bawa iya da baffah hakuri du kuma se kamanta abin kunyar da kayi nasan yanda San nabil yarufema Ido ko cewa yayi kabawa shatuwa hakuri Bata zakayi ko to karma ku sakoni Dan bansan komaiba Akan batan shatuwa shine mijinta shi zefi kowa sanin inda matarsa take to mawai yaushe ta Bata ai kullin in yazo se na tambayeshi ya matarsa se yace lfy take har sako nake bashi yakai Mata du wayake kaiwa

Nabil zuwa gaban hajiya Fatima yayi yace mommy Haka mukayi da ke kinface kema kina Sona Dan Allah in kinsan inda matata take ki fadamin ko wani abinda na keyine bataso du ki fadamin wlh Zan Dena

shi dai minister har yanzo kallan nabil yake ko hajiya Fatima yakasa bawa amsa

Hajiya Fatima tace gaskiya abubuwa da dama bataso kakeyinsu Kuma ta fadamin Allah sarki har kuka take abin tausayi ko akansu ta guduma Allah masani Kuma ai badan Allah zaka denaba kaga Kenan in kaganta ta dawo zaka koma ruwa kaci gaba da halinka da bataso Kuma dada guduwa zatayi

Jiki na Bari yace wlh mommy nayiwa Allah alkawari Zan Dena danshi badan itaba tinda du kema kin fadamin Babu Kyau abinda nakeyi kecefa abokiyar shawararta kibani shawarar yazanyi na gyara ammafa wlh ko Ina iya take Sena Nemo gidanta na fada Mata halin da ake ciki dan itama ta Hura muku wuta kufito Mana da ita aini yau masifar iya ikwan Allah zata yimin Rana Kuma yanzu ita zanna gani inajin Dadi azaman shatuwa kafin aganta

MINISTER hannu binbiyu yasa yai tagumi Yana Jin ikwan Allah

Hajiya Fatima in takalli minister taga yanda yake ta raba Ido ga gumi na ta keto Masa dariyace take dada kamata Babu halin yi saboda nabil Kar yaga tana ta dariya yadau du maganganunta azaman Wasa ko yaudara zega Kuma tasan inda shatuwa take Dan Haka ta hade Rai ta nuna batasan komaiba

Tace Ni yanzu nabil azamana na mahaifinyar,ka Kuma me baka shawara Zan baka wasu shawarwari da zasu anfaneka Amma seni da Kai

Nabil yace mommy Ni yanzu nakeso muyu mgnar muje ko dakin,kine

Tace to tashi muje

Nabil yace daddy muna zuwa kaima da mgnar da zamuyi da Kai Kuma gobe kashirya mazagai zamu tare wajan iya da baffah

Hajiya Fatima da nabil daki suka shiga bayan sun zauna

Tace nabil shawarar da zan baka itace ka koma isilamiya cikin biyu ayi Daya ko anemo maka malami Yana koyamaka karatu agida ko kashiga ta malam liman da ke unguwarnan daga magariba ne da Isha akwai Kuma na bayan sallar Isha zuwa karfe goma nadare kazabi Daya kana zuwa karkayi girman Kai ko wata kunya Babu kunya wajan neman ilimi daga Ni har shatuwa bamasan halayanka da kakeyi nafarko maganar Yan aikin gidannan kacire musu dokar in sun ganka suna durkusawa har se kabar wajan kacire wannan dokar in sun ganka Kuna gaisawa cikin mutunci da girmamawa Amma Banda wannan durkusan har kasa Babu Kai Babu Kuma korar wani Dan aiki dake gidannan ko karkashinka Kuma wayanda ka Kora ada ko kabatawa Rai a Yan aiki du kabisu kabasu hakuri Wanda kaga yadace kayiwa alheri kayi Masa se maganar gudu da mota atiti babushi yanzu kudena Kai da yaranka kudena daukan hakkin talakawa Kai da su yanzu se girmamawa da Basu sadaka Kuma wannan kudin da kake rabawa abokanka suna aikata sabon Allah da kudin kadena ka koma rabawa talakawa maganar Jin kide kide du kadena ko karage ka koma Jin karatun Qur'an zuciyarka zatai sanyi zaka rage zafin zuciyar da kake dashi du in kashiga isilamiya zakaji waazi akai Kai abubuwa da dama insha Allahu du Zan na fadama ahankali kadaure kadena kazama me adalli da hakuri ga kowa kaji nabil kakoma mutunta Mata da darajasu kadena cewa ka tsanesu

Yace to mommy du naji Kuma zanyi isilamiyar ta malam liman zan shiga nafi karuwa da wasu abubuwan sosai

Tace yauwa nabil Allah yaimaka albarka

Nabil yaji mgnar hajiya Fatima yafara zuwa isilamiya hajiya Fatima da kanta taje har gidan malam liman Tai Mai bayani Akan nabil zefara zuwa isilamiyarsa ta maza magidanta da matasa Tai Mai bayani halin da nabil yake ciki Kuma Yana yawan temakawa da yawan yin waazi Akan zamantakewar Dan Adam ko malam liman yaji Dadi da Jin bayanin hajiya Fatima Akan nabil
ranar da taje ranar nabil yafara zuwa da magariba
Chapter 17 · 0% Book details