← Book details Dan Minister Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 22

Sashe 11

Dan Minister Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Biya Mata tafara ai ko nisa batayi da shirmen karatun taba Amina ta tsaidata tace ya Isa Haka shatuwa kinaso kema ki zama Yar birni Kuma Yar gayu kamar Yan matan garinnan ko da yake ban kaiki yawo Kinga yanmatan garinnan ba da sun birgeki sosai to kalarsu nake so ki Zama Zan sa akawo Miki me akoya Miki karatu daga na boko har na isilamiya Nima Kuma in nazo Zan na koya Miki Amma yanzu ki ajje karatun iya da ta koya Miki agefe har ki iya Wanda zaa na koya Miki kinji kanwata

Tace to ke ya zan na kiranki dashi

Tace anty Amina su nana yanzu abinda nakeso da ke wanka nake so muje na hada Miki ruwan da kaina kiyi muga kitsan kanki

Shatuwa na bude gashin kanta

Mamaki Amina ta fara yarinya me gashi Amma saboda rikwan iya ce ita kitsan kanta ya dankare ko tsagar kitsan baagani gawata uwar kasa akanta

Amina tinani tafara azuciyarta tafara mgn tace gaskiya da matsala yanzu Kai nasa ta budemin nagani to Kuma sauran wajanfa ga yarinya kyakkyawa Amma rashin kula yasa kyanta yabuya da zata yarda in na tsefe Mata Kai wlh dada kaina Zan Mata wanka yau dai Daya nayi Mata du abinda yadace na Kuma nuna Mata yanda zatana yi gaba yanzu yanda Zan Mata ta yardar ne matsalar

Zama Amina tasa shatuwa tayi ta tsefe Mata Kai tashiga bandaki tahada Mata ruwan wanka shima se da takirata tahada komai agabanta takuma nuna Mata du abinda yadace saboda gaba in zatayi tace yau komai Ni Zan Miki da kaina gashin kanki Zan Fara wanke Miki daga baya maje gidan gyaran gashi agyara Miki shi nifa yau ni zan miki wanka da kaina kinji

Shatuwa kitayi tadai yarda ta wanke Mata gashin Kanta lfy se da akazo wanka da gyaran jiki da du inda yadace aga Babu gashi da kazanta jikin mace shatuwa Taki yarda Dakar da rarrashi ta yarda Amina Tai Mata du abinda yadace ta Kuma nuna Mata kalar du wani Kayan da mace in tatashi wanka zata na anfani da shi da Kuma to du inda yadace aikuwa Amina bakaramin wankar shatuwa tayiba ta wanketa tas sannan ta barta Shatuwa se runrufe kirji ake abinma dariya yabawa Amina ganin ita kirjin tafi damuwa dshi

Suna fitowa shatuwa tasa hannu tarufe Ido tasa dariya tace wlh kunyarki nake ji anty Amina Kuma fa naji Dadi ako Ina na jikina sakayau nake jina ga wata iska me Dadi nashiga jikina nifa amazagai bana wani wanka sosai Kuma iya bata min fada Kuma fa Ni banasan kitso wlh

Amina tace ai Dole kice bakyasan kitso Daman ku Masu gashi bakwaso ataba muku Kai du wannan me saukine akwai inda Zan na kaiki ana wanke Miki gashi agyara Miki akai akai Kinga Babu mgnar yin kitso se haka in kina so wataran se ana miki Kuma mu anan wanka kullin akeyinsa safe da yamma da yammanma anfiso in Zaki kwanta kiyi inma sansamune Ni kullin sau uku nake so kinayi kinji kanwata zakifi Kyau da kanshi har maganar wanke Baki shima du yanda nakoya Miki da yanda nagaya Miki zakinayi kullin haka nake so kinayi Kinga yanzu kin Fara Zama Yar gayu Kuma Yar birni yanzu Kinga du yanda na koya Miki yanda Zaki shafa wayannan Haka zakiyi Banda kwalliya me yawa kinji kishirya inkin Gama kizo bangaran su mommy muyi Hira Kan natafi gida Kuma ko natafi akwai mommy zata nuna Miki du abinda Baki saniba Nima Kuma zanna zuwa wajanki akai akai muna gaisawa natafi Ina jiranki

Shatuwa Zama tayi tashafa du abinda Amina ta nuna Mata kamar abin arziki bayan tagama tadau jambaki da Hoda da jagira tazuba wata kwalliyar hauka itanan tafara Zama Yargayu kayan da Amina ta kawo Mata tace tasa su tasa wasu riga da siket ne na atamfa sunyi Mata Kyau sosai sun karbi jikinta abinda yabata kwalliyar fuskarta tsayawa tayi gaban mudubi tajuya takuma juyawa wani Dadi yakamata

tace Yasin du Wanda yaganni yau seya hargitse saboda mugun kyan da nayi

Amina tana shiga falan tasamu Hajiya Fatima azaune

Hajiya Fatima tace Amina ansamu ta hakuran ko har yanzu kukan take Allah yasa kinfara naki aikin

Amina tace eh ta hakura Kuma nafara aikina mommy ammafa akwai matsala sosai wlh yarinya kyakkawa Amma iya ta cuceta tabarta ba ilimi tana zaune cikin jahilci in kinji yanda mukayi da ita wlh se takaici yakamaki in yarinyarnan tagyaru wlh yarinya kyakkawa zaayi Kuma nabil seya rude Akan Santa se yasota sosai wlh Allah dai yabamu saa

Suna cikin hirarsu nabil yashigo ko sallama Babu bare gaisuwa yanemi waje ya zauna Yana kallan kofar shigowa yawani hade Rai kamar bega mutane awajanba

Hajiya Fatima tace Allah yakyauta Allah yashiryeka nabil Dan Allah yaushene zakayi hankali yaushene zaka Fara jin fadan da nake maka Akan sallama da gaisuwa yanzu kashigo Mana ko sallama Babu bare Musa ran gaisuwa Kuma me yakawoka wajena ko kamanta kana da Mata kamanta yamukayi da Kai jiyako tin wuri katashi katafi wajan matarka tinkan nakira baffah na gayamasa me kake niyar yi

Nabil yace haba mommy meyasa baka Sona yaushene Zaki Fara Sona kamar yanda sauran iyaye Mata suke San yaransu Dan Allah yaushene Zan samu kauna da kulawa awajanki yaushene mommy yanzu Dan Allah kin goyi bayana auran kandarar da akayimin na mara hankalin yarinyarnan da ita da kakarta Mara mutunci na tsaneta na tsaneta bazan kwana gu Daya da itaba

Hajiya Fatima tace nabil nikuwa nake sanka Kuma nake kaunarka Ni nake so kagama da duniya lfy nabil Babu uwar da zata haifi da a cikinta tace bata sanshi nabil kowace uwa burinta taga Dan da ta Haifa Yana hanya madaidaiciya hanyar da zata kaishi aljana Amma nabil kaki ganewa nabil kullin inamaka addu'ar shiriya Allah yashryeka Allah yaganar min dakai gaskiya kasan irin San da nake maka Kuma insha Allahu nasan Allah natare Dani Kuma ze cikamin burina ya amshi addu'a ta akanka har yanzu inasa ran zaka Zama yanda nake so na ganka insha Allahu nasan Kuma lokacin zakasan gaskiya nake fadamaka

Fitowa tayi zuwa bangaran Hajiya Fatima tana wata irin tafiya abin dariya ita adole tazama Yargayu du Dan aikin da yaganta na gidan tazo shigewa ta gabansa seyayi dariya aboye

wani daga cikin Yan aikin yace Allah kenan abinda kake wulakantawa arayuwa nabil Daman wataran se kunyi rayuwa tare Kai da kake wulakanta mutane musamman Mata gashi yanzu abin dariya kuga wanta ya aura azaman matarsa ai wannan tsohon arzikin yaburge Ni wlh

Dariya sauran sukayi Daya daga cikinsu yace ku dai yi ahankali Dan wlh kunsan Yana ciki bedade da shigowa ba Kuma kowa yaga yanda yake tafiya yasan ransa abace yake Babu ruwana

Hajiya Fatima na Kan yiwa nabil nasiha Sega shatuwa itama tashigo tana wata tafiya tana karkada idanu itama tashigo Babu sallama tanemi waje ta zauna irin zaman da nabil taga yayi yadora Daya Kan Daya itama shi tayi tana ta hura hanci ita ala Dole tahade Babu Wasa daga Hajiya Fatima har Amina kallan shatuwa suka koma yi

Hajiya Fatima tace ohh Ni Fatima du gautan jahne daga mijin har matar lanlai akwai aiki

Nabil Kare Mata kallo yayi besan lokacin da dariya ta kwasheshi yace tofa abin nayine Dan Kauye yashigo birni ba lfy se ya warke Dan Allah kiga wata kalar kwalliyar mahaukata Wai kenan gayu kikayi anan kenan gani kike Wai ke macace ko ahakan Allah yakyauta gaskiya baffah ka cuceni ka gama da Ni Wai arasa Wanda Zan aura azaman matar aure se wannan akuyanlen kuga wani kwalliya kamar anyiwi akuya kwalliya wlh bazan taba Sankiba kome Kika Zama aduniya na tsaneki bana san ganinki adalilinki da wannan tsohuwar na dada tsanar Mata aduniya

Tashi tsaye shatuwa tayi tadaka tsalle taje gaban nabil ta tsaya ta rike kugu tace Nima kamar yanda kake fada ka tsaneni Nima Haka na tsaneka ko ganinka bana san yi da idona kafara yiwa kanka dariya kafin kafara yiwa wani kaifa me shigar Kayan Mata dandaudu matamaza rabi mace rabi namiji adalilinka na rabu da iya me kaunata karabani da ita Ina ji Ina gani ta Ina Zan soka har naso Zama da Kai yasin baka isaba Kar Kuma ka kaini bango Dan wlh akwai abinda na dauko tin daga mazagai saboda Kai Dan na koyamaka hankali karka Bari nafara ma anfani dshi Dan yanda kabarni da jiyar hannunna kaima se na wahalar da Kai kaji jiki kamar yanda Nima naji wannan alkawari nane Ni bana yafiya Kuma bana manta ranar daukan fansa ga du Wanda ya tabani Dan Haka kabi ahankali kashiga hankalinka

Nabil tashi yayi yadauke shatuwa da wani gigitancan Mari me zafi yakuma dauketa da wani lokaci Daya tafara ganin duhu hannu yasa ze Kama hannunta me karaya dasauri hajiya Fatima Tai maza tarike Mai hannu se wani huci yake Dan bacin Rai

Yace mommy Dan Allah kibarni na karasa ragargaza hannun Naga me zatayi ita da kakarta kinafa ji mommy irin kalaman da take fadamin baa Mai damin da mgn baa Kuma yimin rashin kunya baa nunani da yatsa ban karyawa mutun hannuba Dan Haka kiki,yaye ko Dan gaba ki fita harkata har murabu Danni bazan iya Zama dakeba rikwan tsohuwa kazama kawai yau zanga yanda Zaki zo kice za mu kwana daki Daya wlh da yau sekinyi Dana sani arayuwarki

Shatuwa neman abin ramawa tafara yi da sauri Amina tazo takama hannuta tajata dakar suka bar falan Dan taurin Kai irin na shatuwa ko alamar hawaye Babu a idanta burinta kawai itama ta rama abinda yai mata jitayi takara tsanar nabil azuciyarta takuma dau alkawarin se ta dau fansa itama se tabashi wahala

Amina bangaran nabil tamai da shatuwa ta zaunar da ita itama Zama tayi kusa da ita tace haba shatuwa yakike,yin Haka bakiji fadan da baffah yai mikiba ko in har bakya,bin abinda baffah da mommy zasu fada miki Zan Dena kulaki Nima tinda nasan Nima bazakiji nawaba yanzu Dan Allah wace irin kwalliyace wannan afuskarki karki Kuma mu anan ba a irin wannan kwalliyar in kayi mahaukaciya za a dauki mace Zan koya Miki irin kwalliyar da Zaki nayi afuskarki Kar na karaji kin kula nabil Kuma kome zemiki Kar ki kulashi mijin,kine
Chapter 11 · 0% Book details