← Book details Dan Minister Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 22

Sashe 10

Dan Minister Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Me hajiya Fatima da Amina zasuyi inba dariyaba hajiya Fatima tace nabil tafi daki ka kwanta kaji ka huta rabu da iya Wasa take muku kema shatuwa jeki kwanta ki huta Kan akawo Miki abinda kike din

Bayan su nabil sun fita

Baffah yace iya na dawo gareki Dan Allah Dan annabi karki Kuma kula nabil kome yai Miki jikankine shi Kuma sirikinkine ki Dena kula sani kome yai Miki kizo ki fa da min shatuwa Kuma namiki alkawari nabil Babu abinda ze Mata ga Fatima za tana kula da shatuwa da Nabil yanzu anjima Ni da ke zamu koma mazagai Kayan dakin shatuwa anyafe du za ai Mata anan ki kwantar da hankalinki Kuma in an kwana biyu akai akai zamuna zuwa Ni da ke muna ganin yaran muga Kuma ya suke Zama kije dakin shatuwa ki shirya anji zamu tafi Allah ya kiyaye gaba

Iya tace habawa ai in ban ciba Babu wani bayani bana Kuma Jin ko wace mgn Ni fa afah bani abinda nafi wayo naci bazan iya cin Kayan da mugayannan suke ciba akawo min Koko da kosai ko tuwo ko Yar tsala da kunun tsamiya

Baffah yace karki da mu du NASA ai Miki kije zaa kawo Miki

Tace to yanzu naji zance shimafa wannan kaja Masa kunne Dan Naga har yanzu wani gani gani yake min Kuma Ni da naso mu Dan Kara kwanaki Dan wlh bazan iya rabuwa da shatuwa ba Kuma wlh Babu inda zani Ina nan Kuma ai nazata nice Zan Mata zaman daki

Tatashi ta fice tana sababi

Baffah yace sani kaban kunya wlh kabani mamaki sani da iliminka da hankalinka kake kula tsohuwar Nan Kuna Raba abin kunya gaban yaranku Kai sani bakaji kunyaba ko mukamin da kake dash na MINISTER baka dubi girmanshiba saboda San danka yarufema Ido ka daka ta tsohuwar nan kuka dinga Raba abin kunya gaban su nabil ita ai yadace Kai Mata uziri akwai tsufa na damunta da rashin ilimin Kai kumafa wlh kaiwa kanka fada kayi kokari ka hada Kan yarannan su zauna lfy Kar na karajin makamancin haka yasake faruwa

Yace to baffah kayi hakuri Amma gaskiya inajin tausayin nabil wlh

Baffah yace au du abinda nake fada be shigi kunnan kana ko

Katashi ka tafi kaima da mgnar da zamuyi da fatima

New writer's

Hakan Take
*Husba'ahfama* 鉂ゐ煈� *'YAR KWALLIYA* 馃コ馃拑

馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹
馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼
馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹
馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼
馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹
馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼
馃憹馃憹馃憹馃憹
馃憼馃憼馃憼
馃憹馃憹
馃憼

馃拕馃拝 *DAN MINISTER* 馃拝馃拕
馃馃

Written by *Husba'ahfama*

*IG officiall_husba'ahfama*
Facebook *Real Husba'ahfama*

Follow me on Wattpad *@ Real Husba'ahfama*

9-10

MINISTER yace baffah kayi hakuri wlh tsohuwar ce bata da mutunci Dan Haka nake ajje komai agefe nake kulata yanzufa kaji me tace Wai MINISTER take Kira da Miss miss Wai mukamin Miss Miss aka bani Dan Allah Kar ta Kara kwanar Mana agida ta koma inda ta fito har jikar tata

Baffah yace Ni dai azamana na mahaifinka ka dena shiga harkar yarannan kayi kokarin hada kansu ba Wai kana hura wutaba Kana nuna bakaso tin daga jiya Allah yafara nuna maka ishara Akan auransu tashin farko anfasa maka goshi yau baya gaba in ka kuma shiga har karsu bakasan me ze faruba karabu da iya Kar ka daka ta halinta kaso shatuwa kamar yanda kake san nabil gaba bakasan wana alheri zata za me mukaba azuriarka gaba zakaji kunyar abinda ka aikata infa kaji nasihata in Kuma bakajiba to Allah yaba da sa,a tashi ka tafi

Bayan minister yafita

Baffah yace Fatima Allah yaimiki albarka Allah yabaki hakurin Kula da yarannan nasan daga ke har Amina Baku da matsala yanzu Dan Allah kiga me yarannan sukayi yau kowa acikinsu Yana Ji da danyan Kai ita rikwan Kaka uwa ba kwaba shikuma rikwan namiji uba bakwaba ga nabil da shegiyar zuciya da zafin Rai ga shatuwa da tsokana da taurin Kai shi ma Kuma nabil din akwai taurin Kai in Abu yafi karfinki atsakanunsu kina kirana ki sanar da Ni zan zo Dan sani ba ze musu fada na tsakani da Allah ba se yasa San zuciya aciki nashi ze so ita Kuma iya dole yau na jata mubar gidannan yakin badar din da akayima jiya da yau ya isa haka ai in har akabar iya agidannan bazamu iya gyara ko maiba yanzu kije kisa akai mata abinda takeso taci se mu tafi du abinda yashige Miki duhu Akan abinda na fada miki kiki rani kijin Allah yabamu sa,a Akan niyarmu ta alheri Kan yarannan

Tace ameeen baffah Ni yanzu damuwata yanda nabil da shatuwa zasu na kwana waje Daya wlh abinda kamar wuya Dan bakaga rigimar da mukayi dshi Akan su iya sun kwanar Masa adaki cewa yayi yabar bangaransa gaba Daya Kuma baya San komai na wajan shi sabo ze canja se da nacimai mutunci sannan yahakura Kuma kasan alhaji bayansa ze goya

Shawara baffah yai tabawa hajiya Fatima sannan yadada samun minister yadada jamasa kunne sosai Amina itama yafada Mata gudunmawar da yakeso tayi atsakanin nabil da shatuwa

Iya ankai ruwa Rana da ita sosai Kan ta yarda ta koma mazagai ta rabu da shatuwa bakara min kuka iya tashaba na rabuwa da jikarta har tausayi tabawa su baffah ana haka nabil yashigo falan yasamu iya tana kuka Baki yatabe yaja tsaki kawai se gani sukayi iya tatashi tsaye tabi ta bayan nabil babu zato babu sammani Dan Babu Wanda yakawo me zatayi tatakarkara ta dimawa nabil dundu a gadan baya se da yagantsare Dan abin yashige shi beyi zatoba se saukar hannunta yaji

Iya tace Dan kwal uba ai ga Wanda du yaja komai Nan yarabani da jikata muna zaman zaman mu Kuma Zan tafi saura ka Kuma karyamin ita Kuma har yanzu ban huceba se nayi zaman Yan bori akanka ko yaushene me zubin karfafa me shigar Mata dandudu kawai yau Kuma irin shigar da akayi kenan kuma ubanka nagani yaki ya hanaka Dan miss miss din uwa kawai takalli hajiya Fatima yarnan bakiya Saar Daba da mijiba du Basu da mutunci ke Kuma gaki saliha me kirki Amma auran Dole aikai Miki da uban Dan daudun Nan ko Dan Baku dace da junaba

wani irin juyowa nabil yayi cikin zafin nama da bacin Rai yadaga hannu ze damkota iya baffah yai maza yashiga tsakani

Yace haba nabil Kai ta hakuri kaji yau fa zata tafi shikenan Kuma in tatafi se Allah yasake hadaku Kar ka kulata yanzunma tsautsayine Bata saniba Tai maka

Baffah mgn yaiwa minister da Ido kar ya kula iya Dan yaga ranshi yabaci da abinda iya taiwa nabil

Nabil fita yayi daga gidan ko tafiyar baffah da iya be tsaya yagani ba cikin bacin Rai Yana ta huci zuciyarshi na Masa zafi ga baffah yahana shi yai maganin iya

Hamdalah hajiya Fatima tayi azuciyarta da nabil yafice gaba Daya daga gidan ahankali tace alhamdulillah gwara da ka tafi Dan Naga itama shatuwa kadan take jira Kai mgn ta kulaka ga alhaji shima ransa abace yake iya ta taba Dan gwal dinsa

Shatuwa Bata tashi yin kukaba se da taga da gaske zasu rabu da iya hankalinta yatashi Tai ta kuka rikicewa tayi se sun koma tare Dakar akasamu aka rabasu iyama kukan tafara Haka motar taja tafice daga gidan iya se waige take baffah yasha mitar iya Kan su je mazagai shidai ba da hakurine nashi har Allah yasauke su lfy

Nabil da yafita wajan da yake shakatawa yatafi yasamu abokansa acan suna ganinshi sukayo kanshi suna murnar ganinshi da murnar zasu hule tinda ga me kashe musu kudi yazo abokan nasa nasan suyi Masa maganar amaryarshi Amma kowa najin tsoro Kuma sunga yanayinsa Yana cikin bacinrai haka kowa ya hakura yaja bakinsa yai shuru

Da hannu yakira wani daga cikin abokan nasa yazo yabashi damin kudi yace gashinan kowa kabashi yai abinda yakeso in Basu isaba azo akarbi wasu

Yace to mutumina Dan Haka nake sanka kake burgeni baka halin karanta guri in bakai sunansa lami Ni da dashawarar da nakeso nabaka in zaka Dan bani lokaci yau Naga kamar kana cikin bacin Rai kaima kahau layi karabu da bacin Rai kadan Sha abinda muke Sha ko kadanne yau ka gwada lokaci Daya in kasha zakaji kafin yakarasa

Nabil ya daga Masa hannu cikin bacin Rai yace bani da raayin Shane tintini da inaso kaima kasan ko ana siyarwa nera nawa Ina da kudin siya Ni kwata kwata shaye shaye baya burgeni Kuma baya cikin tsarin rayuwata

Yace to ko finah ce yau Daya gatacan na kirama ita kuje ku huta da ita tinda kaga yarinyar na mutuwar sanka

Nabil yace tinkan nai maka rashin mutunci Kai maza ka bace daga wajannan Ni kake hadawa da mace ka kwasan wana Hali Mata suka jefani Kuma shine zaka zo kana bani wannan muguwar shaawar akan mace Kai maza kabace a idona

Jiki nabari yabar wajan

Finah na gefe du abinda yafaru tsakaninsu akunnanta da I danta ga taji labarin auran da yayi kishine ya rufeta afili tace in dai Ina raye nabil se kazama nawa se mun koma Abu Daya da Kai muzuba mu gani Ni da kai

Shatuwa ce kwance Kan makeken gadan nabil tana ta kuka idanta ya kunbura sosai sabo da kuka

Amina ce Tai sallama ta shiga tace kanwata har yanzu kukan kike tayi Baki hakuraba nanmafa gidane Babu abinda ze sameki kinji Kuma bawani dadewa zakiyiba za a Mai da ki wajan iya Kuma naji baffah na cewa da iya zata dawo Nan gidan gaba Daya da Zama saboda ke

Murna shatuwa ta fara tace dagaske kike

Kai Amina ta daga Mata

Nan Amina tasamu tafara janta dahira har tasaki jikinta Nan tasamu ta fara yi Mata tambaya Akan karatu

Shatuwa tace nifa Babu wata makaranta da nake zuwa iyace makarantata itace me koya min karatu Kuma iya tahana asani ako wace makaranta Dan bataso adakeni Nima Kuma banasan karatun Bari na biya Miki abinda iya ke koyar Dani kiji

Kema Kya karamin daga in da na tsaya
Chapter 10 · 0% Book details