← Book details Dan Minister Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 22

Sashe 1

Dan Minister Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

DAN MINISTER

Written by *Husba'ahfama*

*IG officiall_husba'ahfama*
Facebook *Real Husba'ahfama*

Follow me on Wattpad *@ Real Husba'ahfama*

*Bismillahir Rahamanir Rahim*

Dasunsn Allah meraha mejinkai

1-2

Wasu motocine masu numfashi da Rai da lfy masu bakin gilass guda bakwai suke gudu Akan titi kamar zasu tashi sama kowa kaucewa yake inyagansu musamman masu tafiya akasa gudun Kar abugesu abuge banza masu motama kaucewa suke bere masu babur da Keke ko jamian tsaro da suke Akan titi insunga wayannan motoci nazuwa Suma korar mutane sukeyi su tsaida kowace mota harse wayannan motocin sunshige ga wani mahaukacin kida dayake tashi acikin motar da tafi kowace mota acikin motocin guda bakwannan Kyau da haduwa kidan da yake tashi acikinta kamar agidan rawa haka kidan ketashi suna zuwa wani Dan kareran gida suka Danna Kan motarsu zuwa gidan dagudu masu gadi suka bude musu geat suka shiga ga jamian tsaro da bindigogi atsantsaye akofar gidan da cikin gidan dagudu wani Jami,in tsaro yazo yabude murfin motar da kidannan yake tashi wani matashin saurayine meji da kansa Dan kimanin shekara ashirin da biyar kyakkyawa ajin farko fari kamar balarabe kanshi yasha wani irin aski ga yaraba kalar gashin kannashi biyu Daya Baki Daya Jah wuyanshi dauke da wasu sarkoki awuyanshi ga hannunshi wasu manya manyan zobuna ga farcanshi na karshan hagu da dama yayi tsawo sosai gawani mahaukacin gajeran wando irin na zamaninnan da matasa sukesawa ajikinshi kafarsa dauke da wani bakin takalmi metsada gawani bakin gilass yasha a idanshi hannunshi dauke da wayoyi masu tsada fuskarnan tashi ahade Kai bazakace Yana dariyaba daga ganinshi kasan nera tazauna ajikinshi Dan gatane yanaji da kuruciya dakyau da kudi Daya motar matasane saanninshi suka fito amotar Suma du shigar tasu Babu ta arziki ma aikatan gidan se gaishesu sukeyi wasu sunzube akasa suna gaisheshi kamar wani sarki dokarsace du wani maaikaci na gidan in sunganshi su durkusa har kasa sugaisheshi Kuma karsu tashi seyabar wajan wannan dokarsace inba hakaba ranka yabaci kokuma abakin aikinka Banda sojojin da suke gadin gidan sune dokar Bata hau kansuba saboda bazasu yardaba subi irin wannan dokarba Kuma baya amsa gaisuwar kowa daga cikin maaikatan Kuma Dole inkaganshi ka gaisheshi duda baze amsaba Yana cikin tafiya zeshiga falan gidan yaikaro da wani maaikacin gidan bekula da tahowar wannan matashin saurayiba da zugar abokansa Babu zato Babu tsammani wannan maaikaci yaji saukar mari afuskarshi cikin tsawa da gadara matashinnan yafara yiwa maaikacinnan fada

yace Kai Kai waye mahaukacine dazaka hada hanya Dani sannan ka bugeni ko baka gani Kai waye da bazakabi dokataba dangidan waye Kai waye yatsayama kazami irinka talaka kawai har Ina hada jiki dakai zaka gogamin kazanta danhaka nasamuku doka in kunganni awaje ku durkusa har se nabar wajan wato Kaine metaurin Kai da bazakabiba to yau zanga waye yatsayama kaje ansallameka daga aiki ko harabar gidannan karka Kara dawowa inbahakaba Rai zebaci Kuma wata yazo karshe baka da albashi fice kabarmana gida Wawa kawai

Durkusawa maaikacin yayi Yana rokar wannan matashin yallabai Dan Allah katemakeni karufamin asiri karka koreni wlh bansan katahoba Dan Allah kayi hakuri daaikinnan dashi nadogara dashi mukecin abinci ni da inalina nasha wuya kannasamu aikinnan in kakoreni bansan yazanyiba zanshiga wani Hali Ni da iyalina

Kokulashi beyiba Daya dameshi kafa yasa ya Shure mutumin yasa jamian tsaransa sufita da mutumin yanaji Yana gani wannan maaikaci yarasa aikinshi

Cikin bacinrai yashige falan gidan Yana kwalawa mahaifiyarshi Kira mommy mommy

Atsorace tafito tana amsawa tace lfy nabil kaidawa

Yace nida wayannan mahaukatan maaikatan gidannanne wlh zandau mataki akansu gabadaya zankoresu nazuba wasu

Kafin mahaifiyarshi tayi mgn muryar mahaifinshi sukaji Yana mgn yace kamin dedai nabil du Wanda yabatama Rai Ni nabaka dama da doka kakoresu asa wasu kome kace Dana dashi zaai anfani Dan banasan bacin ranka du Kuma Wanda yabatama Rai ko waye shi se nadau mataki akanshi indai kudi naaiki amatsayinka na Dan MINISTER Kuma jinin masu kudi gaba dabaya kana da ikwan taka du Wanda kakeso akasarnan Nina tsaya maka mumuke da kasarnan mumuke da doka ahannunmu indai akankane wlh Zan iyayin abinda baazataba saboda irin kaunar da nake maka Dana Kai kadai Allah yabani dana namiji har yanzu bansamu waniba dolene naji dakai da duwani Abu da kakeso Kaine magajina ko bayan Raina ko da Raina dukiyata takace seyanda kayi da ita kayi abinda kakeso kataka du Wanda kakeso katemaki du Wanda kakeso ko nawa zaka kashe na tsayama nabil yanzu yakakeso ayi wayeshi Wanda yabatama rai acikin maaikatan gidannan yanzu adau mataki kanshi

Nabil yace daddy ai nadau mataki akansa har na koreshi daddyna danhaka nakesanka da irin gatan da kake nunamin da San da kakemin Nima inasanka daddy inakuma jidakai yanzu sonake ajawa du wani maaikaci nagidannan kunne daga Kan namiji zuwa mace Kai musu mgn Akan dokokina duka kasansu daddy Ni bani da lokacin da Zan tsaya da Yan aiki Dan Basu da matsayin da zantsaya dasu har nai musu mgn Dan baajina bane su nafisu da komai

MINISTER yace angama Dana nabil Dole abi abinda kace shi zaayi Bari yanzu yanzu a aiwatar da abinda kace

Nabil yace ok daddy yauwa daddy inasan kudifa najiya da kabani yakare Kuma banaso naje naciro a ATM bani da lokaci ga abokaina zanbasu kudi zasu Wala suyi bushasha inasan miliyan biyu Dan yau muna da bushasha Ni da abokaina

MINISTER yace ok nabil ai ba matsala kaje dakina kadauka ai kasan inda nake ajje kudi kaje kadauka ko nawa kakeso bakomai inkanasan kudi na fadama base kafadaminba nabaka izini kanazuwa kana dauka dagani se Kaine mukasan lambobin da ake anfani dasu na maajiyar kudina nagida ko Fatima mahaifiyarka batasaniba se kai nabil danhaka du sanda kakeso kaje kawai kacira kaji Dana

Yace ok daddy angama yashige yana fito Yana wata irin tafiya

Mahaifiyar nabil hajiya Fatima tace agaskiya alhaji baka kautawa bakayiwa yaranka adalci kaima bakawa kanka shima kansa nabil basanshi kakeba wlh cutarsa kake wana irin gatane wannan zaasa yaro amuguwar ahanyar da bazata doreba sedai takaishi ga halaka karfa kamanta da maganar Yan Karin mgn sukace kaso naka duniya takishi kaki naka duniya tasoshi Kuma ai bashi kadai bane danka Yana da Yan uwa Mata ko danshine namiji ayaranka kake nunamasa irin wannan mugun gatan katunafa Allah Amana yabamu akan yaranmu Kuma zetambayemu akansu sukuma sauran yaranka Mata nagidan miji Basu da hakki akankane Kuma angayama basajin haushin abinda kakewa nabil su baka musu da namiji haukane ko Dan shine auta Kuma namiji guda daya ayaranka dagashi baka Kuma haihuwaba kake nunamai irin wannan gatan kagafa abokansa ko darajar gaisuwa bamasamu insunzo gidannan haka zasu shigemu kamar zasu bangajemu kaga shigarsu dagasu har nabil Babu ta arziki kamar ba yayan musulmaiba Kuma Babu Wanda ya Isa yayi mgn akai kahau mutane dafada yanzu asati yarannan miliyan nawa yake kashewa shishi kadai ga daukan hakkin mutane bayin Allah da yakeyi musamman talakawa Kuma Babu Wanda ya Isa yayi mgn daga Yan uwa zuwa abokai har yanzu an ganeka in mutun nasan kudinka kuma kasoshi sedai yaso nabil dadu wani abinda yakeso kowa haushinka yakeji akan irin sangarta yarannan da kakeyi Amma Babu damar mgn kullin da bakincikin irin halin da nabil yake ciki nake kwana nake yini nimafa uwace Ina kaunar yarannan Amma ba irin wannan muguwar kaunarba Ni nake Masa kaunar da zatasa ya Gama da duniya lfy yahadu da Allah lfy nake Masa kaikuwa wuta kakeso ka kaishi besaniba gani Yake gata kake nuna Masa nikuma nice yake gani makiyiyarshi wlh kokadan banso kasamu wannan mukamin na MINISTER fetir ba bakuma bakinciki nake dshiba ko Daya tarbiyar Dana nake tinani sabo ko da Yaya tarbiyarsa takare saboda kudin da kake dashi da bushashar da kake Masa nakudi bare yanzu da kudinka ya nunku Akan da kwata kwata bahalinmu dayaba alhaji kafin tacigaba da mgn

MINISTER yace ya Isa ya Isa Fatima ko Dan Kinga namiki shuru Ni wlh bantaba ganin matar da take bakinciki da kishi akan dantaba seke haba Fatima kemafa inasanki meye najin haushi haka Dan Allah inbamu hadu munnunawa nabil kaunaba waye zenuna masa shikadaifa Allah yabamu namiji sauran yarana Mata da kike mgn akai ai Suma inasansu Kuma yanzu sunbar hannuna sunkoma karkashin mazajansu Kuma nabasu ilimi tarbiya nazaba musu mazaje nagari meyarage nai musu Kuma duka mazajansu nada dukiya Babu karamin maaikaci acikinsu Kuma ko nawa sukace min sunaso inabasu Kuma haka kawai wani lokacin inamusu kyautar kudi har yanzu kinki wayewa narasa meyasa ke da faffahna bakinku Daya kuntsani nabil ke uwace agareshi Amma bakyasanshi faffah kakane agareshi shima baya,sanshi abinnan nakonamin Rai wlh narasa yazanyi daku kullin faffah cikin kirana yake Yana min fada akan nabil abin har mamaki yake bani kodai wanine yaimuku asiri yarabaku da jininku Kinga illar rashin addu'a ko da ke da faffahna Kuna addu'a sosai wlh Dabaa muku asiriba Akan jininku Kuma inhar bazaki Fadi alheri ba Akan nabil to karki Kara mgn daga yau inbahakaba ranki zeyi mugun baci ke Zan iya hanaki saboda akarkashina kike faffah kuwa mahaifinane ban Isa naimai fadaba Akan nabil Nima akarkashinsa nake tinda shi yahaifeni ficewa yayi ranshi abace ko sallama bemataba

Tana tsaye takaici ya isheta nabil yazo yashigeta shi da abokansa suna wake wake ko kallo Bata ishesuba sukasa Kai suka fice wani hawayan bakincikine yafara zubo Mata

Tace Allah Allah yashiryeku Allah yashiryamin Kai nabil kagane hanyar gaskiya kagane Ni da mahaifinka waye mesanka da kaunarka Allah kasan halin da nake ciki kaimin mgnin abinda yadameni kaikace arokeka Kaine me maganin kowace matsala Allah kaganar da mijina uban yarana alhaji

Daki tashige takwanta saboda kanta da taji Yana ciwo

Iyace take kwallawa shatuwa Kira ke shatuwa bazaki fito kije kiyomin karaba daganan kikaimin nikan tuwanba kinsanfa nayi fishi da iyayanki akanki yanzu da kaina Zan nayin girkina tinda basa sanki basasan abinda nakeso fito Yar jikalleta takwarata Yar gatata maza fito kitafi
Chapter 1 · 0% Book details