← Book details Budurwar Wawa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 19

Sashe 9

Budurwar Wawa Complete Hausa Novel · about 5 min read

So yake ya yi magana amma babu dama, domin tuni ta shige gidansu, zuciyarta na yi mata zafi. Shi kam yafi minti biyar a tsaye kafin ya bawa ƙofar gidan baya, ji yake zuciyarsa na sake kaɗaituwa da soyayyarta, yana jin kowanne sakan na giftawa da son da yake yi mata, baya jin zai iya rayuwa babu ita ko kaɗan.
Maikosai
08130266650
[4/14, 5:59 AM] My number: https://chat.whatsapp.com/CodXIM9nLOXD1QDmW33svF

BUDURWAR WAWA

Maikosai

   FCW

06.

A firgice ya farka. Kowacce kafa ta silin gashin jikinsa tsattsafo masa da zufa take yi. Hannunsa ya ɗaga da ƙyar ya kai saman goshinsa ya shiga katse gumin da ya sami matsuguni a saman goshin. Ya sake runtse idanuwansa da son sake cin karo da abin da ya gani cikin baccin nasa. Sai dai ya gaza yin haka, ya gaza tuno da komai, illa kawai ihu da kururuwar muryoyin mutanen ƙauyen na su da ke ratsa magudanar saurarensa. Babu abin da zuciyarsa ke alamta masa illa kawai ya san yadda zai yi ya fice daga cikin gidan kurkukun ya tafi izuwa ƙauyensu don ceto rayuwarsu.
Ba ya jin zai sake runtsawa duk kuwa da irin tarin baccin da ke ɗawainiya da shi. Miƙewa ya yi tsaye a hankali kan madogaransa, zuciyarsa na yin tsallen bugu, tsoro na sake sababa tarin fargaba a cikin ransa.
Har abada ba zai taɓa mancewa da azzalumin mutumin da yake farautarsu ba. Duk da ya san ko kaɗan ba shi da wata dama da zai iya hukunta shi, tunda shi ba kowane face karan kaɗa miya. Haka ya dinga kai kawo cikin ɗakin tamkar wani mai ɗawafi. Tsawon tarin awanni ya ɗauka yana mai tufka da warwara, kafin ya iya kai mazaunansa ya zauna bakin gefen gado wanda a haka har assalatu ta riske shi.

Ya so a ce ya yi wa Abubakar zancen mafarkin da ya yi jiya, sai dai ya rasa ta in da zai faro masa. Sai yake ganin kamar ma yin hakan ba shi da wani alfanu, wannan dalilin ya sa ya ja bakinsa ya guntse.
  "Ya na ga kamar kana cikin damuwa?" Abubakar ya watso masa tambaya bayan ya zauna kusa da shi.
Murmushin gefen baki Salisu ya yi kafin ya iya bawa Abubakar amsa cikin tambaya,
"Damuwa kuma?"
  "Ƙwarai kuwa! Ai duk wanda ya yi tozali da fuskarka zai gane lallai kana cikin damuwa, domin labarin zuciya a tambayi fuska."
Salisu ya yi wata guntuwar dariya kafin ya kai ga furta,
  "Ko da wasu za su tambaye ni bai kamata a ce kai ka yi tambayar ba."
  "Ko me ya sa?" Cewar Abubakar.
  "Saboda  ka saba gani na a cikin tandun damuwa."
Dariya Abubakar ya ɗan yi, kana ya ce,
  "Ai ba a san maci tuwo ba sai miya ta ƙare. Duk da cewa kusan koyaushe ina ganinka cikin tasko da ƙaƙaniya na damuwa, amma haka ba zai sa na kasa bambancewa ba. Na tabbata damuwar da kake ciki yanzu ta yi hannun riga da wacca ka yi a baya shi ya sa na tambayeka."
   "kadakatar da hasashenka, domin kuwa ni ƙalau nake," faɗin Salisu da son danne damuwar da yake ciki.
  "Ba ka ba ni labarinka ba." Abubakar ya yi furucin don kawar da maganar da suke yi yanzu don ya lura sam ba zai gaya masa ba.
Yayin da Salisu ya ji tamkar ya buga masa guduma ne a tsakiyar kansa, wani abu ya taso ya yi masa babakere a maƙoshi. Bai san me ya sa yake son tilasta shi akan ala dole sai ya sanar da shi ko shi waye ba?
"Me ya sa kadamu da ka san ko ni wane ne? Me ya sa ka zautu da ka san abin da ya ruftowa rayuwata?"
  "Kawai ina son sani ne. Ko haka yana da ɗingimemiyar matsala ne?" Abubakar ya tambaya.
"Ba zance ba. Sai dai tabbas duk lokacin da ka yi mini tambaya a game da ni nakan ji zuciyata na yi mini barazana, nakan ji ƙwaƙwalwata na hautsinawa, haka lissafin ko waye ni da dalilin samuwata anan kan ruguza mini wasu lissafi da nake shiryawa."
  "Ka yi haƙuri. Ban so duk cakalkala maka lissafinka ba, sai dai ina so na sani ne saboda na san ta wace hanya zan bi na soma ganin na taimaka maka. A baya na ji ka ce na yi haƙuri a madadin mutanen wancan ƙauyen ko me ya sa?"
  "Saboda ina da kyakkyawar alaƙa da kuma dangantaka da mutanen ƙauyen domin su ahlina ne," Salisu ya ba shi amsa.
"Ke nan kana nufin kai ɗaya daga cikin ahlin ƙauyen can ne?" Abubakar ya tambaya yana mai kafe Salisu da wani mayataccen kallo.
  "I haka nake nufi," Salisu ya ce.

Tuni Abubakar ya miƙe wuf! Kan dugadugansa yana mai yin nuni da Salisu, gami da son yin magana amma tuni ya sami harɗewar harshe na wucin gadi.
Salisu ya miƙe shi ma, yana mai dafa kan kafaɗar Abubakar da har lokacin ya gagara cewa komai.
   "Shi ya sa na ce ka yi haƙuri a madadin mutanen ƙauyen. Sannan ina fata haka ba zai janyo wani naƙasu daga cikin taimakon da kake shirin yi mini ba?" Ya ƙarasa maganar da tambaya.
Bai ba shi amsa ba ya zauna tare da tanƙwashe ƙafafuwansa kafin ya kai ga cewa,
  "Ba zai janyo komai ba matsawar za ka yarda da sharaɗin zan gindaya maka."
   "Wane irin sharaɗi ne?" Salisu ya ce cike da tambaya.
Abubakar ya yi wani irin murmushin gefen baki ba tare da ya kalli Salisu ba ya ce,
  "Duk abin da kaga na yi ko na aikata shi ko kuma ka gan ni tare da shi kada ka kuskura ka ce za ka tambaye ni dalili,shi ne kawai sharaɗin. Idan har ka amince to ni ma a shirye nake da na taimaka maka kai da mutanen ƙauyenku," Abubakar ya ce.
   "Na amince," Salisu ya ba shi amsa da haka, ba tare da ya yi tunanin komai ba.
Abin nema ya samu, matar falke ta haifi jaki. Tsananin sanyin farinciki ya ratsa tsokar zuciyar Abubakar jin yadda lokaci guda ba tare da Salisu ya yi tunanin komai ba ya amsa masa, tabbas ya kusa fita daga sarsarin da aka jefa shi.
"Na amince," Salisu ya sake maimaitawa, da tunanin ko Abubakar ɗin bai ji ba.
  'Yaro bai san wuta ba sai ya taka. Babu shakka tabbas da ɗan gari akan ci gari!' Abubakar ya ce cikin ƙasan zuciyarsa.
"Shi ke nan haka ya wadatar" Abubakar ya ba shi amsa yana mai miƙewa tsaye.
"Muje cin abinci ko?" Ya faɗi haka ga Salisu.
Ba tare da Salisu ya musanta masa ba ya miƙe suka fice daga ɗakin.
Chapter 9 · 0% Book details