Sashe 12
Budurwar Wawa Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ƙwarai ma kuwa! Domin rashin bacci zai shafi duk wani ƙoshin lafiyar mutum kuma babban hatsari ne ga kamuwa da cututtuka da dama ciki har da ƙwaƙwalwa. Haka kuma illolin rashin bacci sun haɗa da: jefa mutum cikin ciwon tsananin damuwa, idan ya yi muni yana sa mutum ya kashe kansa ko ya halaka wani. Yana jefa mutum cikin fargaba da kasancewa cikin tsoro. Yana sa ciwon zuciya, hawan jini zai ƙaru, ciwon suga na iya tsanani. Mutum kuma zai kasance cikin fushi, yana saka rashin gani sosai. Haka nan mutum kan iya fara shaye-shaye idan an saba da shan maganin bacci. Ga matuƙin mota kuwa zai iya janyo masa hatsari. Hatta da wayar salula na iya haddasa rashin samun bacci saboda yawan yin amfani da ita a lokacin da ya kamata ace ana bacci. Domin kamata ya yi mutum ya bambance lokacin bacci da kuma lokacin amfani da wayarsa. Shaƙuwa da wayar salula kan janyo illoli sosai ga al'adar mutane, kuma matsalar ta shafi yara da manya. Wani lokaci rashin bacci na kasancewa silar rikicin da ake samu na zamantakewa tsakanin iyali da kuma abokin aiki."
"Tirƙashi! Amma likita ta yaya mutum zai iya kaucewa waɗannan abubuwan? Ta yaya mutum zai iya samun isasshen bacci duba da na ji ka ce 'shan maganin bacci shi ma na iya janyo wata matsalar' kamar dai ta shaye-shayen da ka ce?"
Likita ya nisa kana ya ce, "Ya yawaita yin bacci, ya tabbatar yana samun wadataccen bacci. Idan ya zamana mutum na fama da rashin bacci to rama wannan baccin da ya rasa shi ne maganin fatarar bacci ba wai ya sha wasu ƙwayoyi don samun bacci, domin aikinsu na ɗan lokaci ne kuma zasu iya tarwatsa al'adar baccin mutum. Idan har mutum ya kasance ya kwashe watanni bai samu isasahen bacci ba dole ne ya tsara yadda zai biya bashin baccin. Mutum zai iya ƙara awanni a lokacin baccinsa domin rama wannan baccin da yake kansa."
"Ke nan idan har Salisu na son gujewa wannan cuta da ke barazanar son kama shi dole ne ya riƙa samun wadataccen bacci? Kuma dole ne ya rama baccin da ya rasa? "
"Wannan haka yake. Domin yawan tunanin da yake yi da rashin samun isasahen bacci kan iya haifar masa da tarin matsaloli."
Abubakar ya nisa cikin zuciyarsa na matuƙar tsananin tausayin Salisu. Yayin da wani bigire na zuciyarsa ke ankarar da shi irin tarin baƙincikin da mutanen ƙauyen ke ciki. Tabbas abin da yake shirin yi shi ne mafitarsa, to yaya zai yi ma bacin shi ma duk da haka tilas ce ta sanya shi yin haka? To amma yaya zai yi da halin da abokinsa ke ciki? Ya san muddin ya bijirewa mai gida to kashinsa ya bushe, ba shakka alƙiyamarsa ce za ta tsaya.
Jin shirun da ya yi ya bawa likita damar furta, "kada kadamu in sha Allahu zai sami waraka."
Abubakar ya yi firgigit kana ya ce, "Na gode sosai likita. Kuma ni ma in sha Allah zan yi ƙoƙari wajen ganin an yi wa tufkar hanci."
"To madalla! Wataƙila zuwa anjima ko gobe idan na ga yanayin jikinsa zai iya komawa cikinku."
"To likita, mun gode." Abubakar ya ce.
Cike da zallar tausayin Salisu Abubakar ya koma ɗakin, ya soma bin Salisu da kallo sai kawai ya ji ƙwalla ta tarar masa cikin idanunsa, sam sai ya ji kwata-kwata bai kyautawa kansa ba. Me ya sa yake cutar da mutumin da ya aminta da shi ɗari bisa ɗari? Kuka ya kubce masa ya yi hanzarin toshe bakinsa. Ya shiga rera shi tamkar babu gobe, yana yi yana tsinewa kansa bisa son zuciyarsa da ya yi har ta kai shi ga ya shiga zaluntar Salisu.
Maikosai
0830266650
[4/15, 3:15 PM] Maryam Abduul(Maikosai): https://chat.whatsapp.com/CodXIM9nLOXD1QDmW33svF
BUDURWAR WAWA
Maikosai
FCW
07.
Da ƙyar ta miƙe ta shiga bayi don watsa ruwa da ɗauro alawa, komai cikin sanyin jiki take yinsa, gaba ɗaya kuzarinta ya kau bata jin zata iya aikata komai a yanzu don ta fison zaman kaɗaici zaman da babu abin da zata yi illa tunanin yayarta ta.
27-01-2021
Rana ce da ta kama ranar asabar, ranar bata da lecture a makaranta, tana kwance a ɗaki tana chart ta ji muryar yayarta ta da alama ba ta jima da shigowa gidan ba. Da sauri ta yi jifa da wayar ta fice daga ɗakin tana dariya, jikin Asma'u taje ta ɗane tana mata oyoyo tamkar ƙaramar yarinya.
"Ke dalla ɗagani ke dai kullum ci ma baya bakya girma ko? Gaskiya momi kina fama wallahi har yanzu bata canza hali ba." cewar Asma'u tana murmushi.
"Kin ganta nan, gata nan ina ta fama da ita, ita kaɗai a gida amma duk da bi ta isheni ta dameni yadda kika san nayi kyautarta na huta." cewar momi.
"Aikuwa da kin huta sosai momi, don dai yasin fitinarta ta isheni ni ma, kullum mutum baya sanin ya girma."
Turo baki tayi kamar zata ɓarke da kuka kafin ta ce,
"Wai saboda Allah idan ban dameku ba suwa zan dama, ku kaɗai nake da ku fa. Duk randa na rasa ɗaya daga cikinku ina ga haukacewa kawai zanyi wallahi."
"Kin ji shashanci ko" cewar momi tana nuni da Asma'u.
Asma'u ta yi dariya kaɗan kafin ta janyo Falmata jikinta ta ce,
"Ni ma idan na wayi gari babu ke haukacewa zanyi koma na rasa rayuwata in biyoki kawai"
"A haf! Kice kema dai har yanzu babbar kwaboce" faɗin momi.
"Ni bari in shiga daga ciki, wannan haukan naku ba da ni ba." Ta sake furtawa tana miƙewa zuwa shigewa ciki.
A hankali ta sake sakin wani marayan kuka san da ta kammala wannan tunanin, tana jin ƙaunar yayarta ta na sake dawo mata sabuwa. A lokacin da take da buƙatarta sai ga shi mai rabawa ta rabasu. Wayarta ce ta hau ruri sai dai ko takanta bata bi ba ta haye kan gado ta yi lamo da ita tana lumshe idanuwanta. Ƙarar wayar ce ta cika mata kunne hakan ne ya bata damar janyo wayar don ta kashe, sai dai ganin sunan da ke yawo kan gilashin wayar ya sa ta amsa kiran tare da saka wayar a amsa kuwwa.
"Hello sweety ya jikin naki?" ta ji sautin muryarsa.
Da ƙyar take iya furta,
"Da sauƙi"
"Kin ci abinci, kin yi wanka?" ya jero mata tambayoyin.
"Eh!" ta ba shi amsar a taƙaice. Kafin ta ji ya sake furta,
"Ki yi hakuri kin ji sweeti addu'a zamu yi wa aunty ita tafi dacewa da ita, ta riga ta tafi saura mu kuma, fatan mu Allah ya sa mu dace."
"Amin" kawai ta iya ce masa ta silale ta sake kwanciya tana kashe wayar, don yanzu sam bata ƙaunar jin wata murya cikin kunnenta...
***
A hankali Salisu ya shiga ba shi labarin ko shi waye, tun daga tasowarsa da yarintarsa, da girmansa da ƙaunar da ke tsakaninsa da iyayensa, da kaf mutanen ƙauyen, da abin da ya ke son sabauta ƙauyensu da kuma abin da ya turke rayuwarsa a nan.
Abubakar ya sauke wani gauron hucin numfashi kana ya ce,
"Tabbas ka cancanci a tausaya maka. Domin ba ƙaramin matuƙar zalunci aka yi muku ba. Kuma babu makawa ko tantama bana yi lallai da akwai wata ƙulalliya cikin lamarin amma sanin cewar 'sanin gaibu sai Allah' kaɗai ya isa mu watsar da komai domin shi zato zunubi ne ko da kuwa ya kasance gaskiya. To amma wace mafita ka yanke yanzu?"
"Ita ce abar da na jima ina nema. Kullum lalube nake yi cikin duhu, rayuwata ta jima daga fita daga duniyar haske zuwa duniyar duhu Abubakar"
Abubakar ya zauna sosai yana mai sake fuskantar Salisu kana ya ce,
"Amma kai me kake tunani akan wannan mayafin sharrin da suka lulluɓa maka?"
Sai da Salisu ya nisa kana ya iya faɗin,
"Abu ɗaya zuwa biyu ne. Ko dai su tashi ƙauyenmu gaba ɗaya su yi yadda suke so da shi, ko kuma su ƙwace gonakin da suka tsoka ne musu idanuwa su yi abin da suka ga dama son ransu."
"Ƙwarai! Haka zai iya faruwa. To amma a ganina bai kamata mu zauna haka ba"
"Me ya kamata mu yi?" Salisu ya tambaye shi cike da zaƙuwar jin amsar da za ta fito daga bakinsa.
"A gani na, kamata ya yi mu sanar da hukuma wannan cukurkuɗaɗɗen bahagon al'amarin," faɗin Abubakar.
"Hmm!" Salisu ya ce, yana mai sauke idanunsa ƙasa tare da kafe wajen da kallo tamkar mai nazartar wani abu.
"Yaya na ji ka yi shiru?" Abubakar ya tambaye shi.
"Karfa ka manta a labarina da na baka na shaida maka cewa hukuma ta shiga lamarin amma ba ta yi komai ba, domin a ƙasar nan cin hanci da rashawa ya yi katutuwa a cikin zuƙatan jama'a."
"Ai ba duka a ka taru a ka zama ɗaya ba Salisu! Me zai hana mu sake jarrabawa mu gani sai da gwaji akan san na ƙwarai. Kuma ba ka ce mini ita hukumar ta karɓo muku wani haƙƙi na ku ba?" Abubakar ya ce.
"Don Allah mu ƙyale wannan zancen. Domin ko da ace duk jikina kunnuwa ne ba za su taɓa gamsuwa da tarin hujjojin da kake son kafa min su ba a game da sha'anin hukuma, na jima da gamsuwa da cewa 'duka kanwar ja ce' Babu wani abu da za su iya yi mana sun sanya girman mai kuɗi fiye da kukan talaka a kansu, sun fifita buƙatun mai kuɗi fiye da buƙatun talaka to me za su yi mana a yanzun? Tun da a baya ma mun nema ba su yi ba? Shi wannan haƙƙin da ta ƙwato mana to sai da muka biya cin hanci sannan muka same shi. Na yi faɗi tashi sosai da shiga gwagwarmaya kafin na iya samo lauyen da ya tsaya mana wanda muka damƙa masa wani abu sannan ya tsaya mana, a koto kuma har da shaidar ƙarya guda ɗaya tal! Lauyanmu ya gabatar duk da bamu so haka ba, amma ya ce mana dole sai da haka za ayi nasara."
"Cab! To Allah ya kyauta, dama ita rayuwar wannan duniyar haka take."