← Book details Budurwar Wawa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 19

Sashe 15

Budurwar Wawa Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwananta biyu tana jinyar jikinta, babu wanda ya leƙota daga shi azzalumin har wanda yake kawo mata abinci. Ji take tamkar zata bar duniyar, ita da a ce tana da damar bawa rayuwarta zaɓi to da tuni ta bata zaɓi akan tana so tabar duniyar ko ta huta, ji take ina ma mutum na da damar gayyato mutuwa da ta gayyaceta tazo ta yi wuff da ita tun kan lokacin wa'adinta ya yi, duk da dai tana da buri guda ɗaya wanda shi ne ta nemi yafiyar mutune ukun da ta san haƙƙinsu ne ke bibiyarta, tabbas kuwa babu tamtama duk wanda ya yi da kyau zai ga da kyau kamar yadda mahaifiyarta take yawan shaida mata.

Wallahi da ace tana da damar dawo da komai da ya shuɗe mata da ta jima da dawo da shi ko dan ta samu sa'idar rayuwa, ko dan ta bi umarnin iyayenta waɗanda suka yi sanadin kawota duniya.

   "Na cuci kaina, na san ba zan taɓa samun rahama a wajensu ba wayyo Allah!"

Ta yi maganar tana rushewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya.

Ko da wasa bata taba kawowa reshe zai juye da mujiya haka ba, bata taɓa tsammanin cewa akwai ranar da zata tsinci talatarta a laraba, sai ga shi tun ba aje ko ina ba ta fara girbe yaɓanyar da ta shuka da hannunta.

***
'Yar ƙaramar takardar da Abubakar ya ba shi da suna yin sallama a ɗazu ya ɗakko ya buɗeta tare da kafeta da idanu. Ba komai ne a ciki ba face jerin lambobin waya da ke rubuce a jiki, 'zan tafi ga lambata nan idan ka fito ka nemeni ta nan. Sannan ka tuna da sharaɗinmu da ke tsakani.' Ya tuna kalamin Abubakar lokacin da yake ba shi takardar.

Jin kansa na juyawa tamkar fanka ya saka shi miƙewa tare da fita daga ɗakin. Baya son yawan sanya kansa cikin damuwa da yawaita tunani a yanzu saboda maganar da Abubakar ya gaya masa a ɗazu, 'Ka rage yawan tunani Salisu haka zai iya janyo maka tawaya a game da ɗaukar fansar da kake son yi.'  Idan kuwa har haka ne to tilas ne a gare shi ya rage dilmiya cikin ɗumbin tunani tunda haka zai iya haifar masa da matsalar da za ta iya kawo masa togaciya har ya gaza nemawa ƙauyensu 'yancin da yake son nemar musu. Tunanin haka ya sa jefi-jefi kan yi watsi da damuwar da ke nuƙurƙusarsa da son bijirewa ƙwaƙwalwarsa wajen yin tunani.

Yau saura kwana uku ya rage masa cikin wannan gida ya fita ya koma ƙauyensu. Yana zaune yana tunanin da ba zai iya haƙuri da shi ba. Tsulum! Tamkar an jefo ɗan shila gabansa haka ya ga dattijon nan tsaye ƙiƙam a kansa sai kuma ya ji ya tuntsire da yi masa dariyar shaƙiyanci.

  'Ikon Allah! Wai sauro da dakon giwa. Shi kuma babu abin da ya iya sai dariya?' Salisu ya tambayi kansa da yin maganar duk cikin zuci.

Ya ɗaga idanunsa yana mai bin dattijon da kallo. Yayin da shi kuma ya sake ɓarkewa da wata dariyar shaƙiyancin. 'An kuma wai mace ta haifi mace,' Salisu ya sake faɗin haka cikin ransa.

Dattijo ya jima yana ɓaɓaka dariya kafin ya kai ga furta,  "Yaro bar murna karenka ya kama zaki.  Kada ka yi tunanin don ka kusa fita daga gidan nan zai sa ka fita daga cikin shafin baƙin kundun tarwatsa rayuwarka da mai gida ya shirya maka shi babi-babi. Ina mai yi maka bushara da cewa yanzu ma wasan ya soma."

Tuni Salisu ya miƙe wuf! Kan dugadugansa, cikin nutsuwa ya fuskanci dattijo har suna iya shaƙar numfashin juna ya ce, "Ban san ko kai waye ba? Ban san kuma wane ne shi wannan mai gidan da kake ta ambato mini ba? Sai dai ina so ka sani zuciyata da ƙwaƙwalwata sun jima suna wassafa mini cewa zalunci baya taɓa ɗorewa, ko ba daɗe ko ba jima lallai wata rana asirinku Allah zai tona shi ga idan duniya. Ka sani faɗa da aljani baya da kyau don haka ka je ka ka shaida wa mai gidan naka cewa ya shiryawa tarar aradu domin wannan karon ba irin aradun da ya sa ba tara ba ce, da sannu zansa ya fige kazar wahalarsa da kansa, da sannu zan sa ya tsinci talatarsa a laraba, da sannu zan sa yalashe amon da ya yi, ka gaya masa cewa ruwan da ya tafasa baya tsoron ƙuna!"

Baki galala a buɗe dattijo ke bin Salisu da kallo. Har Salisu ya zagaye shi ya bar wajen bai iya mayar wa da Salisu martani ba. Daga ƙarshe sai ya hau naɗe tabarmar kunya da surutan banza da wofi.

Salisu kuwa da ma zama shi kaɗai ne baya so shi ya sa ya fito daga ɗakin tunda ba shi da wani abokin hira yanzu. 'Waye mai gidan da dattijon ke magana a kansa?' Ya shiga tambayar kansa.

  'Waye kuwa? Ban da wanda ya wuce mutumin da ya zalunceku, ya ke son fatattakar ƙauyenku don ya yi amfani da shi.' Wani sashi na zuciyarsa ya ba shi amsa.
Tamkar wanda ƙwai ya fashewa a ciki ya miƙe a hankali ya soma yin tattaki cikin ɗakin. 'Bai san me ya sa ya mannewa rayuwarsu ba? Bai san me ya sa ya kafe akan ƙauyensu ba? Lallai su ne kaɗai suke da ruwa a yankinsu da zai kafe sai su? Me ya sa yake son ya dinga illata zuciyoyinsu da tsauri haka?  Shi kam wane abu yake so haka da ba zai ƙyalesu su yi rayuwarsu cikin daɗi ba?  Me ya sa ya takura musu? Me ya sa nan ɗin ma? Me ya sa?...' Haka ya dinga jerowa kansa tambayoyi ba tare da ya samu amsarsu ba.
Wasu siraran hawaye suka shiga ziraro masa daga cikin kurmin idanunsa zuwa kan shimfiɗar dandamalin fuskarsa.

Kwanansa biyu baya iya cin komai ba. Ko ya je ɗakin cin abinci ya amsa baya iya ci, ɗoki da son ganin ya kusa fita ya hana shi yin komai.

  Kwana ukun da suka rage masa ya fita ya yi sune a cikin wani irin hali. Ya yi sune a cikin halin ƙunci da ɗimautar yanayi. Yana jinsa tamkar wanda ya haɗiyi rashin walwala da rashin rabo, da tsananin ciwon kai ya kai wayewar garin ranar da zai bar gidan. Sai dai ɗoki, tsananin farinciki da son hanzarin ganin ya isa ga mutanen ƙauyen na su ya dakusar masa da jin zafin ciwon, yana jin shi kamar wanda aka yi wa bushara da shiga gidan aljanna. Tunani, damuwa, tsoro duk sun yi na su wuri, yayin da ya yi fatali da baƙincikin da ke cin ransa, alla-alla yake kawai yaga ya isa ƙauyensu.

Tunda ya fito yake jinsa cikin nishaɗi da annushuwa. Buri da maitar son ganin ahlinsa suka sake mamaye zuciyarsa, duk da cewa a wani bigire yana jin bugun zuciyarsa na tsawaita.

Yana isa farkon cikin ƙauyen nasu ya sake jin zuciyarsa na sake tsananta kakkauran bugu. Komai na ƙauyen ya sauya masa, gani yake tamkar ma ba ƙauyen na su ba. 'Kai kam wata ai ba kwana ba ne' wani sashi na zuciyarsa ya tunasartar da shi haka. A hankali yake ajjiye ƙafafuwansa duk in da suka samarwa da kansu matsuguni. Bin ƙauyen yake yi da kallo mai cike da tambaya sai dai babu giftawar mahluƙi da ya gani balle ya tambaya ya ji abin da yake wakana. Da tunanin ina 'yan ƙauyen suke? Me ya ɓoye ɗuriyarsu haka? Ya ƙarasa bakin ƙofar gidansu cike da ɗokin yin tozali da fuskar mahaifinsa.

  Tashin hankali, ba a saka masa rana. A wannan taƙin Salisu ya ji hankalinsa ya kai maƙurar ƙololuwar tashi sa'ilin da ya yi tozali da gidansu tamkar kangon da ya shuɗe tsawon shekaru ba a dube shi an agaza masa ba. Sam ba za ka taɓa cewa an zauna a cikinsa ba. Ya zame jikinsa a hankali ya sulale tamkar maciji da ke shiga cikin raminsa ya zauna ƙasa ya jingina jikinsa jikin katangar ƙofar gidan, yana mai kafe kansa da jikin bango tare da lumshe idanuwansa. Ji ya yi kawai hawaye masu ɗumi suna kwaranyo masa tamkar ruwan da ke zubowa daga cikin indararo.

   'Shi ke nan ta faru ta ƙare, an yi wa mai dami ɗaya sata' ya ayyana haka a ransa.

  'Me ya faru da mahaifina?' Ya yi wa kansa tambaya ba tare da ya sami amsa ba.

   "Salisun baba Haladu!" Ya tsinkayo wata murya na kiransa.  Ya soma buɗe idanuwansa da suka soma yi masa nauyi a hankali ya kai ganinsa kan matashin saurayin da ke tsaye gabansa. Kallonsa yake yi babu ko ƙiftawa tamkar wanda ya warke daga cutar makanta.

   "Ina mahaifina?" Ya ji tambayar ta suɓuto masa ta fito.

     "Baba Haladu?" Saurayin ya mayar masa da amsa cikin siga ta tambaya.

Da ka kawai Salisu ya iya ba shi amsa. Ganin haka ya saka saurayin faɗin, "Biyo ni muje."

Salisu ya miƙe da ƙyar domin duk jikinsa jinsa yake a ɗaɗɗaure ya soma tattakawa yana mai marawa saurayin baya.

Ba wata doguwar tafiya suka yi ba kafin saurayin ya kutsa kansa cikin wani ɗan ƙaramin gida madaidaici. Lura da haka ya sa Salisu shi ma zungura kansa cikin gidan.

"Yana cikin gidan nan," Saurayin ya ce daidai lokacin da suka ƙaraso tsakar gidan.

"Baba!" Ya kira sunan tare da sake furta, "Salisun baba Haladu ne, ya dawo."

Cikin sauri wanda aka kira da baba ya ɗaga labulen ɗakin da yake ciki yana mai faɗin, "Yana ina? Salisu kana ina?"

Shi dai Salisu zuru ya yi yana kallon mutane biyun da yake ji tamkar ya san fuskokinsu.

"Ɗan halak ka ƙi ambato. Allah mai yadda ya so. Salisu kai ne? Yaushe ka fito?" Mutumin ya cillawa Salisu tambayoyi yana mai taɓa jikin Salisu.

Ganin kallon da yake yi musu ya saka shi sake tambayarsa da,
   "Ka gane ni kuwa Salisu? Shin ka shaida mu?" Liman ne da Lauwali? Ya yi masa tambaya ya kuma ba shi amsa.

Sai a sannan Salisu ya iya tuno da in da ya san fuskokinsu, da ƙyar ya iya saɗaro kalmomin da ya furta, "Ina mahaifina yake?"
Chapter 15 · 0% Book details