← Book details Budurwar Wawa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 19

Sashe 16

Budurwar Wawa Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin furucin Salisu ya sanya liman kamo hannunsa ya shiga jansa kamar raƙumin da ake jan akalarsa suka shige cikin ɗakin da ya fito.

  Tuni ya shiga kokawar jan numfashinsa da ƙyar saboda barazanar barin jikinsa da yake son yi,  ƙafafuwansa kuwa so suke su bijirewa ɗawainiyarsa sababin ganin mahaifinsa kwance tamkar gawa in da fuskarsa gefen dama ya tawaya ya yi wani irin muni. Sosai yake jin wutar tashin hankali na sake ruruwar masa sam ya gaza tsayuwa, a take ya silale izuwa ƙasa kamar mesa.

   "Ka yi haƙuri Salisu! Komai ya yi farko yana da ƙarshe," cewar liman.

A hankali yake rarrafawa kamar ƙaramin yaron da ke koyan rarrafe har ya isa gaban gadon kabar da mahaifinsa ke kwance, ya ɗora hannunsa daidai fuskar mahaifin nasa in da ya sami tawaya cikin raunin murya da karyayyiyar zuciya ya soma furta,
  "Me ya sa meka baba? Me ya faru da kai bayan ba na nan?"
Liman ya dafa kafaɗar Salisu yana mai matse ƙwallar da ta tarar masa cikin kurmin idansa.

  "Sun ƙwace mana komai, Sun ƙone mana tushen arziƙinmu, sun tagayyara rayukanmu, maza da mata; yara, manya, tsoho, makaho, gurgu, kuturu, duk ba su ƙyale ba. Tun bayan tafiyarka gidan yari muke fuskantar barazana, sanin babu mai iya mana sai Rabba ya sa muka mayar da komai wajensa domin a duniyar nan indai kai talaka ne to sai dai ka rungumi littafin ƙaddararka. Mun shigar da ƙara amma saboda ba mu da galihu aka kori ƙarar saboda babu gamsasshiyar hujja, saboda kawai suna da kuɗi, saboda bambancin suna su masu kuɗi mu talakawa. Kullum da fargabar abin da zai zo mana muke kwana, yau kwana shida ke nan da rusa mana komai domin kawai neman abin da suke da muradi. Ganin mahaifinka cikin wannan halin kuwa na da nasaba da aika-aikar da azzaluman suka yi mana na ta'addanci, sun babbake komai tamkar gobarar daji haka wuta ta dinga cinye gonakinmu," liman ya ƙarasa cike da rauni har yana mai shatatar da ruwan hawaye. Cikin sauri ya saka hannunsa guda ya shiga sharce ruwan hawayen da suka sami matsuguni a saman fuskarsa.

Tamkar iza wutar murhu haka ya dinga jin tashin hankali na sake izuwa cikin kansa. Ji yake yi munana nan kalaman liman na son tarwatsa masa sauran rayuwarsa 'kodayake me ya yi saura kuma ba cin rayuwar tawa ma ta ƙare,' ya ce cikin zuciyarsa. Kalaman liman sai yi masa amsa kuwwa suke yi a cikin masarrafar kunnuwansa. Tunda yake yana da yaƙini tun wanzuwarsa a duniya bai taɓa jin tashin hankali makamancin wannan ba. Da ace rayuwa zaɓi ce, to da ko labudda shi zai zaɓawa kansa irin rayuwar da yake son yi, sai dai kash! Bakin alƙalami ya riga ya bushe. 'Me haka yake nufi da shi? Ke nan duk abin da yake yi tufkar makaho yake yi ta gaba, ta baya na warwarewa?'

  Ji ya yi, ya yi zaman 'yan bori a ƙasa yana sakin wani gigitaccen kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. Liman kam bai hana shi ba, bai kuma nemi ya dakatar da shi ba har sai da ya ƙoshi da kayansa ya gaji ya bari ta hanyar tsagaitawa.

****
  "Kaka a zubo tuwon yanzu?" faɗin Fa'iza bayan ta kammala girkin daren.

   "A'a barshi Fa'iza sai na yi sallah tukunna, kema ki wuce kije ki yi sallar ko"

    "To kaka"

~Bayan mintuna goma sha biyar.~

Al'adarsu ce bayan magrib sukan zauna su ɗan yi hira kafin kowacce ta wuce makwancinta.

   "Kaka kin san me?"

Kaka dake ƙoƙarin kai lomar tuwo bakinta ta ɗan dakata tare da faɗin,

   "Ina fa zan san me ni ba akuya?"

'Yar dariya Fa'iza ta yi, kafin ta furta,

  "Kai kaka!"

"A'a yo to ni ina zan san wata me kawai ki tafi kaitsaye ga abin da ke cin zuciyarki."

  Shagwaɓe fuska ta yi kamar zata yi kuka.

  "Au to riƙe kayanki idan ta rube miki a ciki ta fashe ai na ji ko"

Ɗan turo baki tayi kafin ta ce,

  "Da man fa ɗazu ne da kika aikeni nazo zan wuce na ga Abdullatif shi da yaya Nasir kin san abokinsa ne."

Zuru kaka ta yi tana binta da ido, lallai wannan al'amari na yarinyar nan da girma yake.

   "Waye kuma shi haka?" kaka tayi tambayar da son gwasaleta akan maganar da ta yi.

  "Kai kaka shi ɗin ne baki sani ba, alhalin har sunansa kin haddace fa."

  "Ni ban haddace sunan kowa ba saboda ba sunan Annabi ne ko sahabi ba. Kin ga wallahi ba ki fita idona ba sai kin tattara duk wasu kayanki kin bar gidan nan, don tsohonki yaushe kika girma har kika son wata soyayya."

Tuni kaka ta shiga zazzage mata, ta inda take shiga bata nan take fita ba. Ita kuwa ta yi tsuru da ita ta kasa motsawa, ko kaɗan bata son ta ji ana ambatar mata ƙauye, bata son rayuwar ƙauyen tun da har Allah ya sa ta baro shi, to tana fata ta bar shi ke nan har abada duk da dai ta san akwai ahali biyu na jikinta da suke rayuwa acan. Tuno da hakan ya sa babu shiri ta haɗiye abin da ke cinta ta mayar da shi ciki, sai dai fa duk wani faɗa da kaka ke yi mata a banza wai an mintsini kakkausa domin shiga yake yi ta kunnen damanta ya fita ta hagunta.

  "In tambayeki mana?" ta ji kalaman kaka. Bata iya amsa mata ba, hakazalika ita ma bata damu da amsawar tata ba ta ɗora,

  "Yaushe za ki daina son maso wani ne Fa'iza? Ke fa kika nuna min baya sonki hasalima ke bakya gabansa"

   "Wallahi kaka yana sona, kawai dai na san yana ja min aji ne."

  "To ke a matsayinki na ɗiya mace me yasa ba za ki ja masa ajin ba, ko so kike a dinga kiranki da ballagaza mai bin ɗa namiji."

  "A'a" tayi furucin tana girgiza kanta.

"To daga yau kar na sake jin ko da sunansa a bakinki balle wata soyayyarsa kin ji ko?"

Kai ta ɗaga mata alamar to, tuni ta shiga tunani da neman mafita don ta tabbata zuciyarta ba zata iya daina son Abdullatif ba.

Maikosai
08130266650
[4/16, 6:23 AM] Maryam Abduul(Maikosai): BUDURWAR WAWA

©Maikosai

FIRST CLASS WRITERS ASS.

011.

Ya ɗago da jajayen idanuwansa da suka rune sosai suka yi ja tamkar jan gauta ya dubi liman da har lokacin ya gaza tantance a wace duniyar yake ya gaza cewa komai har tsawon wasu daƙiƙu. Da ƙyar ya iya buɗe nauyayyen bakinsa da ya yi masa nauyi wanda yake jinsa tamkar an ɗora bulo inci tara akai ya ce,
  "Me ya sa ko kaɗan ba su da tausayi ne malam? Me ya sa mutane suka cika da tsantsan son kansu?  Me muka aikata musu haka da zafi da zasu zartar mana da wannan ɗanyayyen hukuncin? Me ya sa malam?" Sai kawai ya sake kecewa da wani irin kukan da ya kuɓce masa tamkar kubcewar sauro idan an kai masa duka.

   "Ka yi haƙuri Salisu! Allah yana ganin komai yana sane da duk halin da muke ciki.  Ko shakka ba na yi tabbas zai yi mana kyakkyawan sakamako, za mu samu kyakkyawan tagomashi na abin da suka yabanya mana, su kuma da sannu za su amshi mummunan sakamakon abin da suka yabanya da hannunsu, za su girɓe baƙar makoma da sai sun gwammace kiɗe da rawa, kada kadamu Allah yana sane da mu."
Cikin rashin kuzari Salisu ya miƙe tsaye daga zaman daɓaron da yake. Ya kalli liman da ke tsaye cikin ƙunan rai da zafin ƙuncin zuciya ya soma magana,
   "Wallahi! Wallahi!! Wallahil azim Malam ba zan ƙyalesu ba, ba za su taɓa cin bulus ba. Kada su ma taɓa tunanin duk abin da suka yi suke da riba domin na rantse sai na saka su sun gane cewa bakin rijiya ba wajen wasan makaho ba ne! Sai na sa sun gane cewa kowa ya ci ladan kuturu sai ya yi masa aski! Sai na sa sun gane duniya ba aljanna ba ce, sai na sa sun ɗanɗani ɗacin da na sani a saman harshinansu."

Liman ya jinjina kansa kafin ya kai ga furta, "Haƙurin dai za ka yi Salisu domin bamu da ikon da zamu iya yin jayayya da su, kowa yayi nagari ai kansa. Sam-sam ba na so ace wani abu ya sake aukuwa a garemu ko kuma kai don Allah!" Ya ƙarasa cike da roƙonsa.

Salisu kam da yake santsin zuciya na kwasarwa wajen son bijirewa haƙurin da yake son samin matsuguni cikinta sai ya kai dubansa ga liman ya ce,  "Ka yi haƙuri malam don Allah! Bana jin zan iya yi musu afuwa, domin kuwa yin shirun da ake yi musu ne ya sa suke duk abin da suka ga dama, ya kamata mu nuna musu cewa ba tsoronsu muke yi ba, shiru-shiru ba tsoro ba ne, ja da baya ga rago ba tsoro ba ne shirin yaƙi ne." ya ƙarasa yana kautar da idanunsa ga kallon liman.

   "Ni ma ina goyon bayanka Salisu, ta yaya za mu yi musa su girɓe abin da suka shuka ɗin da hannayensu kamar yadda ka ce?" Lauwali ya tura tambayarsa ga Salisu.

  "Ban sani ba, amma akwai wanda ya ce zai taimaka mini, indai har ya yi mini haka na san ba ni da matsala da haka. Ni dai damuwata ɗaya ce a yanzu halin da babana yake ciki."

Liman ya kaiwa matashin saurayin wani irin sakaran kallo, kafin ya ce, "Kai Lauwali bana son shashanci."

Kana ya ɗora da,
"Tun aukuwar al'amarin har yanzu bai buɗe idanunsa ba. Bai kuma sake motsa gaɓɓan jikinsa ba, idauwansa a rufe suke ruf! Sai dai yana raye wanda na gane haka ne ta hanyar fitar da wani irin amon numfashi kaɗan-kaɗan idan ka kara kunnenka saitin hancinsa za ka iya ji."

Salisu ya sauke dogowar ajjiyar zuciya yana mai durƙushewa ba tare da ya ce da liman komai ba. Ya saka hannu ya dafe kansa da yaji ya soma sara masa da tsanani, hawaye na ziraro masa zuwa kan kuncinsa ya runtse su take wani majigi mai ƙarfi ya haska a idanunsa in da ya shiga dawo masa da wasu watanni.

Watanni Uku Baya
Chapter 16 · 0% Book details