Sashe 4
Budurwar Wawa Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dattijuwar ta kalleta sosai, har tana mai ƙoƙarin cusa idanuwanta cikin na Maman kana ta ce,
"In dai wannan gidanki ne to har abada ba zan sake zuwa ba, amma ki sa ni 'ya ai ba ta ki ba ce ke kaɗai, tunda ba ke kaɗai kika samar da ita ba har da ɗana a cikin samuwarta."
"To sai me dan da shi, amma ai ba shi ne ya yi min wahalar haifarta ba ko?"
Dattijuwar ta girgiza kai, tana mai ɗaukar hanyar ficewa daga gidan. Domin ta lura Mama ta yi nisan da ba za ta taɓa jin kira ba.
"As-as Allah ya raka ta taki gona."
Mama ta ce tana mai yarfa hannu.
Ta haɗe fuska sosai tana mai cizon laɓɓanta na ƙasa, kana ta ce,
"Dole in sake takawa wannan taohowar burki."
Ta j tsaki.
"Wato dai ƙiri-ƙiri matar nan hassada take min akan arziƙin da Allah ya ba ni, to a hir ɗinki na fi ƙarfinki walllahi, kuma hassada ga mai rabo taki ce, shi ya sa ga shi nan kullum kina min ni kuma ina sake hawa."
Ta ɗan nisa kana ta sake furta,
"Ga ni nan zuwa gareki, dola ne yau na kawo miki ziyara Lamunde."
*Masu tambayar littafin BIYAYYAH yana nan complete document 500 acc 8085307740 opay Maryam Abdulaziz shaidar biya ta nan 08130266650. Littafin ZAHRAA kuwa yana kan manhajar wattpad @Maryamad856*
Maikosai
08130266650
[4/9, 4:29 PM] My number: https://chat.whatsapp.com/CodXIM9nLOXD1QDmW33svF
BUDURWAR WAWA
©Maikosai
FIRST CLASS WRITERS ASS.
03.
Mai kafu babur ne ya samu damar tsayawa daidai kofar wani gida wanda wacce ke cikin adaidaita sahun ta ba shi izini wato mama. Mayafinta a hannu, fuskar nan a cunkushe, ranta a hasale ta miƙamasa kuɗin tare da shigewa cikin gidan.
Daidai tsakar gidan ta ja tunga ta soma ƙarewa gidan kallo, cike da nazarinsa kafin ta soma rattaba sallama. Mama ke nan, mace mai kimanin shekaru talatin da takwas, mai kyan jiki daidai wa daidai, domin cin daɗi da alatun duniya na sake gyara mata jikinta wanda take samunsu ta hanyar ɗiyarta Zuhra.
Wata mace ce ta fito wacce aƙalla da shekaru kaɗan ta girmi mama. Tana dariya tana makawa Mama harara.
Mama ta yatsina baki kafin ta ce,
"Idan kin gama harara sai ki ba ni wajen zama ko?"
Matar itama ta mai da mata da martanin yatsina bakin kafin ta ce,
"Idan na ƙi fa"
Mama ba ta ce mata komai ba ta janyo tabarma da ta gani jinkine da jikin bango ta shimfiɗa ta zauna.
Ganin hakan ya saka matar zama ita ma.
"In ce dai lafiya ko?" Matar ta ce.
"Ina fa lafiya Lamunde, tatsuniyar gizo ce dai da ba ta wuce ta ƙoƙi." cewar mama.
Lamunde ta yi 'yar ƙaramar dariya kafin ta ce,
"Ai na sani, zancen dai kenan ga shi ke kuma ba kya ɗaukar shawara."
"Wace shawara kuma?" Mama ta ce.
"Akwai shawarar da ta wuce kullum nake gaya miki kizo mu je a kaita wajen boka mai kankat."
Lamunde ta ce tana mai duban fuskar Mama.
Mama ta haɗe girar sama da ta ƙasa kana ta ce,
"Lamunde kenan, har abada ba za ki sauya ba. Ni fa har yanzu ban ga mutumin da zanje wajensa domin ya biyamin buƙata ta ba wallahi,ba a yi shi ba, ba kuma za ayi shi ba, ki barni da kissata da kisisina ta dai, da kuma sauran rashin mutuncina."
Lamunde ta nisa kaɗan kafin ta ce,
"To ai shi kenan. Amma ki sa ni tabbbas kina tare da wahala yasin, ki je ki yi tunani a kan maganata ita ce kawai hanya mafi sauƙi da za ki kawar da ita ba tare da kin sami gargada ba."
Mama ta sake haɗe fuska ta yi kicin-kicin kafin ta ce,
"Za ki sake sawa na sake rabuwa dake har abada, yadda idan na tafi ba zan sake waiwayarki ba wallahi Lamunde. Har abada ina faɗa miki babu wani ɗan adam da zai iya ɗaukemin buƙatuna har ya biya min su."
"Shi kenan ai, ayi ma ga ni. Idan fitsari banza ne to kaza ta yi mu ga ni mana."
Lamunde ta ce.
"Za kuwa ta yi har ta lashe kayanta." Mama ta ce.
"Rai dai wai an cirewa fara kai, na tabba da kanki wata rana za ki dawo gareni da son kai ki wajen bokan." Lamunde ta ce.
"Allah ya tsari gatari da saran ice wallahi." Mama ta ce.
Ganin ba ta sami abin da ta zo nema ba ya sa ta miƙewa tsaye tare da faɗin,
"Ni bari na koma in da na fito."
"To a sauka lafiya"
Cewar Lamunde.
Tana fita Lamunde ta cizi yatsanta ɗaya tana mai furta,
"Tabbas zan yi iya iyawata wajen ganin na karkato da akalarki wajensa, zan yi aiki a kanki yadda za ki sake buɗewa 'yarki ido har ta soma bin maza da kanta yadda za a keta haddinta a tarwatsa rayuwarta."
Ta saki wani ƙayataccen murmushi mai cike da munanan ma'anoni kala-kala.
Mama na isa gida rataye gyalenta kawai ta yi a igiyar dake ɗaure tsakar gidan ta ciro wayarta dake cikin aljihun siket ɗin ciki ta danna lambar wayar Zuhra.
Bugu ɗaya Zuhra ta ɗaga, Mama cikin faɗa-faɗa ta soma faɗin,
"Sam ko kaɗan bana so ki dawomin gidan nan hannu rabbana, bana son ganin ƙananun kuɗi a hannunki kin ji dai na gaya miki ko?"
"Mama meke faruwa ne? Me ya faru?"
Zuhra ta shiga jefa mata tambayar.
Ba ta bata amsa ba, ta katse kiran tana huci sai ka ce wata zakanya.
***
Kano ta dabo tumbin guiwa. 2021
Riƙe take da jakar kayanta wacce ta kammala shiryawa tsaf ta tafiyar da zata yi bikin ƙawarta kuma aminiyarta, duk da wani sashe na zuciyarta bai san tafiyar to amma yaya zata yi ita kanta ba zata iya gafartawa kanta ba muddin ba je bikin ba, domin iya halacci Na'ima ta yi mata a rayuwa. Shigowar wani kyakkyawan matashin saurayi ne falo ya sanyata murmusawa, sosai take sake jin soyayyarsa cikin ranta, yadda take sake ratsa kowacce kafa ta magudanar jininta.
"Gaskiya ba daban Na'ima ta yi mana halacci ba da babu inda za ki je hubbyna."
Far ta yi da idanuwanta, kafin ta ce
"Ni kaina ba a son raina zan yi tafiyar ba sai dai kawai babu yadda zanyi ne, amma ko kaɗan bana so na tafi na barka da kewata."
"To yaya zamu yi? Abu ne da ya zama dole mu ramawa kura aniyarta."
"Hakane kam"
"Yanzu sai Kaduna ko?" ya ce yana kai hannu saman fuskarta yana shafawa.
"Eh mana yallaɓai kodai in fasa tafiyar nan ne?"
"A'a ni na isa, kar kisa Na'ima ta yo min hayar sojoji" ya yi maganar yana dariya, itama dariyar ta yi kafin takai idanunta kan agogon dake ɗaure saman taintsiyar hannunta. Tsaki ta ja, kafin ta ce,
"Ka ga yarinyar nan ko? Wallahi zan tafi in barta."
"Sorry wataƙila bata kammala shiryawa ba ne, ki dinga yi mata uzuri mana please hubby."
Tsaki ta sake ja, cike da jin haushin yadda yake mayar da ƙanwar tata kullum yarinya ta ce,
"Duk kai kake sake sangartata wallahi kuma na faɗa maka bana so, domin wannan sam ba gata kake nuna mata ba. Ni fa shi yasa na so ta tattara komatsanta ta koma gaban su umma don ta san ƙarya take ta dinga wannan son jikin wallahi acan."
"Yarinya ce ita fa hubby, shi kuma yaro sai da rarrashi ko?"
"Ka ji da shi kuma. Ni ka ga muje ka saukeni idan ka kaini tashar ka dawo ka kaita makarantar." Ta yi maganar a ƙufule.
"Yanzu duk wannan lokutan da muka shafe ace ba zamu iya haƙuri da jimirin tsayata na 'yan wasu daƙiƙu ba, haba hubby kin fiye rigima wallahi."
"Haka ka ce" tayi maganar tana jan akwatinta da nufin barin falon, da sauri ya sha gabanta yana kama kunnuwansa daidai nan Falmata ta fito daga wani ɗaki dake kallon falon, cikin sauri ta yi hanyar fita. A hanzarce Asma'u yayarta ta janyo mayafi jikinta tayo baya har tana shirin faɗuwa.
"Don ƙaniyarki wato ga sa'arki ko, ki gama shanyata sannan ki fito ko haƙuri baki iya badawa ba ki zari ƙafa da nufin barin falon."
Turo baki Falmata ta yi, kafin ta ce,
"To ni aunty ni me nayi ne?"
"Iyye! Wato wuyanki ya isa yanka da har kike kallona kike tambayata ko? Za ki mayar da wannan tsinin bakin ko sai na fasa shi, shashashar banza shi ma da yake goya miki baya duk zan haɗa na yi maganinku bari na je na dawo wallahi gida za ki tattara ki koma."
"Haba hubby wai me ya sa ne haka? Ki dinga..."
Cike da hanzari ta ɗaga masa hannu kana ta ce,
"Na tabbata da ƙanwarka ce ba zaka shagwaɓata ba ko dan gudun lalacewarta, me ya sa ba za ka dinga son gaskiya ba ka koyi take ƙarya. Ka sani idan yau Falmata ta lalace ba da kowa za ayi kuka ba sai ni, domin a gidana take a gabana kuma take."
"Yanzu fisabilillahi me yakawo wannan maganar hubby, na ga dai tarbiya daidai gwargwado tana da ita, ke da kanki kina yabon halinta da ɗabi'unta kuma kina mata fata na gari, to ki cigaba da hakan don Allah ki cire duk wani wasi-wasi game da Falmata."
Bai bata damar magana ba, ya sake furta,
"Ke kuma wuce muje tun da ba za ki iya bata haƙuri ba kina ɗora min laifi."
Sai a sannan Falmata ta ɗan sunkuyar da kai tana sosa ƙeya ta ce,
"Ki yi haƙuri auntyna ta kaina." ta fice daga falon tana jan trolly ɗin yayarta ta.
Tafiya ce da zata yi daga Kano zuwa Kaduna bikin ƙawarta wacce tun suna makaranta suka zama tamkar 'yanuwan juna, kasancewar makarantar kwana ta yi tun daga ƙaramar sikendire har zuwa babba. Sai dai har ga Allah har cikin zuciyarta ba wai tana jin son tafiyar ba ne, kawai dai zata yi tane don babu yadda zata yi. Su kansu tamkar karsu rabu haka suke jin junansu.
"Wallahi aunty bada ban jarrabawar nan da zamu yi ya ba da binki zanyi mu tafi tare, ni fa ko kaɗan bana so na ga kin yi min nesa."