← Book details Budurwar Wawa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 19

Sashe 2

Budurwar Wawa Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zuhra ta yi far da idanuwanta kana ta ce,
   "An gama Mama"

Ta juya tana mai shirin fita daga gidan, mahaifiyarta ta tsayar da ita ta hanyar furta,
   "Kullum dai ina sake jaddada miki ban da masu Babura, ƙaramar mota wacca kuɗinta bai wuce kuzo mu ga ni ba. Idan an zabaro mai jirgin sama ma ai shi kogi baya ƙi daɗi ba, kullum cikin neman abin da zai cika kansa da shi yake."

Zuhra ta murmusa kana ta ce,
  "Kai mama, sam ba ki da matsala fa, in dan wannan ne an gama, ki kwantar da hankalinki tamkar maye ya tsinci haƙori."

Ta fice da sauri daga gidan tana mai murmusawa.

"Shi ya sa nake sonki ɗiyata, muddin ina raye ke da auren jinin talaka sai dai in a lahira, ke a lahirar ma idan an bani damar hanawa to lallai babu shakka zan datse igiyar da za ta sada ki da shi. Mijinki Ɗawisu ne da yake wahalar samuwa."

  Mama ta yi furucin tana mai komawa ɗakin da ta fito.

****
Duk da yanayin da yake ciki, bai hana shi son tilastawa tsamurarren jikinsa ƙarfafawa wajen ganin ya tsaya kan madogaransa ba. Hannayensa biyu zube cikin ƙarafen da suka zamo masa ƙyauren ƙofar ɗakin. Tabbas! Kowace nasara tana ga zuciyar nema, wacca ta kasance mai matsanancin haƙuri da juriya, to amma shi tasa nasarar neman silalewa take yi tamkar yadda maciji ke silalewa izuwa cikin raminsa saboda raunatuwar da ɗanyar zuciyarsa ta yi.
Maƙoshinsa a matuƙar bushe yake, yadda ko yunƙurin magana ya yi azaba ce ke ratsa maƙwallatonsa. Wannan ya sa ya kasa saɗaro ko da wata guntuwar kalma izuwa ga shimfiɗar harshensa ta ratso laɓɓansa biyu har ya iya fitarwa, ko ya samu sauƙi na daga raɗaɗin dake addabar raunatacciyar zuciyarsa. Sai dai tilas ne agareshi da ya ƙarfafi kansa ya samo ƙwarin guiwar da zai yi amfani da ita. Tilas cikin ɗayan biyu dole ya zaɓi ɗaya. Ko dai ya yada makaman yaƙinsa ya saduda wajen neman ƙwato musu 'yancin da yake fafutukar yi; ko kuma ya sake ƙarfafa zuciyarsa ta yadda za ta sake yin ƙaimi wajen fafatawa da maciya amanar ƙasar da yake cikinta, mutanen da suka gaza tsayawa ƙauyensu har suke fafutukar yada zango a nan ta ƙarfin tsiya.

  To amma ta ina zai fara? Ita ce tambayar da ya amayar da ƙyar saboda zafin da busasshen maƙogwaronsa ke yi. Har yau baya manta ko shi ɗin wane ne? Da kuma babban dalilin da ya farauto shi izuwa nan. Babbar damuwarshi guda ɗaya yadda yake garƙame a nan tsawon kwana ashirin bisa wani jirkitaccen dalilin da bai san tushensa ba sai dai yaɗuwarsa.

  "Zamanka bai kamata a nan ba Salisu. Ya kamata a ce kana a gaban ahlinka waɗanda ake son tozartawa ake neman ƙwace musu gonakinsu da kuma 'yancinsu."

Wani sashi na daga bigiren zuciyarsa ya tunasar da shi haka, da yadda yake son ankarar da shi wasu abubuwan da suka riga suka shuɗe, wasu kuma suna nan har yanzu ba su gushe ba. Ƙarshen tika tika tik ma masu hannu cikin al'amarin na zaune cikin kwanciyar hankali saɓanin ƙauyen nasu, suna watayawarsu duk yadda ransu keso saɓanin su da aka wofantar, gwamnati ta kasa taɓuka komai an ballagazantar da su.

Kenan su Manoma ba su da wata daraja ne? Me ya sa ba'a mutunta manoma? Ya ƙare da tambayar ta sanya shi zubar da hawaye masu zafi bisa kan dandamlin fuskarsa. Sai dai ya sani gaskiya za ta yi halinta ko ba daɗe ko ba jima, domin shi 'ciki da gaskiya wuƙa bata taɓa huda shi' Sai dai rashin sanin taƙaimaiman zuwan lokacin ya saka shi jingina da jikin ƙofar yana mai rumtse idanuwansa da suke masa radaɗi da azaba tamkar wanda aka watsa barkono ciki.

  "Ka yi haƙuri. In dai gidan nan ne babu abin da za su iya yiwa mutum wajen ganin ya sami waraka na daga cutar da ke nuƙurƙusarsa" Ya jiyo sautin wata murya na sanar da shi haka tare da san haƙurƙurtar da zuciyarsa. Abin da ya tilasta masa barin jikin ƙofar kenan ya yi tattaki izuwa inda yake yana mai zama.

  "Wai me ka yi ne aka kawoka nan? Me ya sa kake yawan yin kuka?" Muryar ta sake yi masa amsa kuwwa cikin sigar tambaya.
Da ƙyar ya kai maganansa izuwa kan saurayin dake kusa da shi, idanunsa sun kumbura sun haye sunyi suntum! Tamkar wanda aka sanya wa curin ƙasa a ciki.
Da ƙyar ya iya kalato amsar da yake son ba shi.

  "Ni ma bana ce ba. Sai dai na san tsantsar zalunci ne hakan. Amma babu komai Allah yana ganin komai" Ya ce yana mai sharce ruwan hawayen da ya sake biyo wanda ya zubo.

  "Kana nufin ba ka san laifin da ka aikata ba har aka kawo ka nan aka jefar da kai?"

  "Ba zan ce ban sani ba, sai dai babban dalilin yin hakan ne ban sani ba." Ya ba shi amsa.

  "To me ya sa suka kawoka nan?"

"Zalunci da son zuciya" ya faɗa yana mai cusa kansa cikin matsematsin cinyoyinsa. Ko kaɗan baya san abin da zai sake tariyo masa da rayuwarsa ta baya. Duk da abin da zuciyarsa ke wassafa masa na ya tashi ya ƙwato haƙƙinsu amma shi kam yanzu yafi ganin kawai ya yada makamansa ko ya samu ya kuɓuta daga wannan ɓakin gidan.
Ganin haka ya saka mai tambayar gimtse bakinsa, sai dai cikin zuciyarsa tambayoyi ne fal a cikinta. Amma ganin Salisu ya zura kansa cikin matsematsin ciniyoyinsa ya sanya shi yin shiru, domin ya lura ko kaɗan baya son damuwa, ba kuma ya son hayaniya. Duba da tun farkon shigowarsa ɗakin babu wanda ya kula balle ya ce masa kanzil.
Shi kam Salisu babu abin da yake yi face jayayya da zuciyarsa da son bijire mata akan abin da take son saita shi akai.

Baya taɓa mantawa ranar ashirin da shida ga watan nuwambar da ake ciki shekarar dubu biyu da ashirin da biyu (26 November, 2022.) ita ce ranar da aka ƙwamuso shi aka miƙa shi gaban alƙali har ya yanke masa hukuncin zaman gidan waƙafi na wata guda.

Ranar da suka tashi cikin farin ciki bisa nasarar da suka yi a zamansu na ƙarshe a koto kan azzaluman da suke son tarwatsa lissafin rayuwarsu. A cikin ƙauyensu, a kuma ƙofar gidansu, kana a gaban idanun mahaifinsa da yake matuƙar jinsa cikin zuciyarsa a ka ƙwamuso shi. Kuma duk yadda yaso ya ji laifinsa a station ɗin abin ya ci tura, har sai da aka je koto wanda a nan ne yake jin dalilin da ya sa suka kamo shi. Sai dai yana sani, yana kuma da tabbacin su kaɗai ne suka san babban dalilin da ya sa suka shirya masa wannan gadar zaren.

   "Dan su koreka su fatattaki ƙauyenku mana." Zuciyarsa ta raya masa haka.

  "Ko ka manta da gonakinku da suke hari? Gonakinku da suka tsokane musu ido" Ta sake raya masa haka a karo na biyu.

" Ɗaki na saba'in da biyu(72) mai lamba ashirin da tara(29) ya sha maganin ƙwari dan ya mutu"
Kunnuwansa suka naɗo masa wasu kalamai da ya sa suka sanya kwanyar kansa hautsinewa. Tuni ya dafe kai da nutsawa cikin tunani gami da zaƙulu wani furuci makamancin hakan da ya soma ji cikin mazirarin kunnuwansa, wanda aukuwarsa a cikin ƙauyensu ne. Idanunsa suka shiga hasko masa irin yanayin da ya riski ɗan ƙauyen nasu cikin mawuyacin hali dalilin shan maganin ƙwari da ya yi a yunƙurinsa na san kashe kansa. Wanda hakan ya haddasa masa samuwar wani nauyayyen ciwon kai.

  "Lafiya kuwa? Meke damunka?" Saurayin ya shiga tambayarsa. Ganin babu amsa ya sanya shi isa ga bakin ƙofar ɗakin da suke ciki, ya shiga nemarwa Salisu taimako ta hanyar kiran gaggawa da yake yiwa ma'aikatan gidan yarin.

*Masu tambayar littafin BIYAYYAH an gama shi? E, an kammala za ku iya tura kuɗin littafinku naira #500 ta wannan asusun 8085307740 opay Maryam Abdulaziz ko kuma ga waɗanda basa da damar ganin opay sai su tura a wannan 2413122913 zenith bank Maryam Abdulaziz sai a tura shaidar biya ta wannan lambar 08085307740 da zarar kin biya zaki samu littafin BIYAYYAH complete ɗinsa, na gode.*

Albishirinku littafin ZAHRAA yananan kan Wattpad kuje ku duba an kammala shi complete ɗinsa,madalla.

Maikosai
08130266650
[4/8, 8:30 AM] My number: https://chat.whatsapp.com/CodXIM9nLOXD1QDmW33svF

BUDURWAR WAWA

Maikosai

    FCW

02.

Zuhra na fita bakin titi, ta zaro wayarta da ke cikin jaka ta hau latsa kiran wasu lambobi.

Bugu ɗaya biyu aka ɗaga.

  "Hello! Babyna na fito fa"

Ta faɗa cikin wata iriyar siga da narkar da murya.

  "Ok ga ni nan."
A ka ce daga ɗaya ɓangaren.

Ba su wani yi mintuna masu tsawo da gama wayar ba, wata haɗaɗɗiyar mota ta faka gabanta. Sauke gilashin motar aka yi tare da hasketa da wani ƙayataccen murmushi, kafin daga bi sa ni a buɗe mata murfin gaban motar.

****
   "Assalamu alaikum"

A ka shiga kwaɗa sallama cikin tsakar gidansu Zuhra.

Dattijuwar mace ce  mai kimanin shekaru sittin da biyu, Ba tare da ta jira an amsa mata ba ta janyo kujerar tsugunon dake ajjiye a tsakar gidan ta zauna da mazaunanta .

  "Wai ba kowa ne a gidan ne? " Ta shiga tambaya da son samun amsa.

Mama da ke kwance tun shigowarta idonta biyu tana kuma jinta ya sakata miƙewa tana jan wani zaren tsaki ta fito bayan ta ɗage labulen ɗakin.

  "Maraba da zuwa, ashe ke ce"

Ta faɗa tana ƙoƙarin ɗaura ɗankwalin dake hannunta.

  "I! Ni ce dai gani ko ba kya son zuwan nawa ne?"

Dattijuwar ta afka mata tambayar tana mai kafeta da idanuwanta.

"Ni ban ce ba, ka da akai ni gaba. Amma dai da za ki ragi zuwan da  zai fi miki alheri, dan ke na lura sam ba kya zuwa gidan nan da alheri a bakinki,duk san da kika zo  ba kya faɗin komai sai tsiya."

Mama ta ce, tana mai jingina da jikin bangon ɗakin.
Chapter 2 · 0% Book details