← Book details Budurwar Wawa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 19

Sashe 8

Budurwar Wawa Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A'a my bash bana son na dinga wahalar da kai, kuma ka san dai ana ta jiranka ko? Hakanma ai ya wadatar abin da ka min ba zan iya biyanka ba, ka sauke ni a nan zan hau napep sai na ƙarasa, sannan kuma zan ma fara biyawa ta gida don ana buƙatar wasu abubuwan."

   "Ba dan raina yaso ba, amma dai banji daɗi ba, ki isar min da gaisuwata wajen mama kafin nazo na duba jikin nata."

  "Godiya nake my bash."

Nan ya sauketa tare da tsarar mata mai napep wanda zai kaita har gida.

   "Ki kula min da kanki my babyta" yace yana kashe mata ido ɗaya.

****
Dundu kaka ta kaiwa Faiza yarinyar da ta shigo ta isketa na kuka.

   "Wallahi anyi raguwa ke kuwa, to bari kiji wallahi idan baki nutsu ba sai na mayar da ke ƙauye."

   "Ƙauye kuma kaka?" tayi maganar tana turo baki.

"Ƙwarai ko kina musu ne? Yo ni za ki zo kina yiwa shaƙiyancin banza da wofi.?

Tuni ta soma malalar da ruwan hawaye, ta durkushe a wajen tana kuka tamkar wata karamar yarinya.

***
Ganin irin yadda Salisu ya kafe shi da idanunsa sai ya sake shiga halin tsarguwa.

  "Ba ka yarda da ni ba ne?" Cewar Abubukar cikin sigar tambaya da son bagarar da irin kallon da Salisu ke yi masa. 

   "Me ka ga ni?" Salisu ya ba shi amsa shi ma cikin siga ta tambaya.

"Babu komai. Sai dai duban da kake yi mini yana sa na ji tamkar kana zargina ne da wani abu wanda har sai ya sa na ji tamkar ban cancanta da na zama wani ɓangare a gareka da nufin taimakonka ba. Zai sanyayar mini da ƙwarin guiwata da nake saka rai da ita har na rasa sanin da wace hanya ya kamata na taimaka maka kamar yadda kake da buƙata."

  "To ka cire haka daga ranka. Ta wace hanya ce zan iya ankarar da mutanen wannan duniyar har su san a wane hali tamu duniyar ke ciki?" Salisu ya yi tambayar.

   "Kamar yaya?" Abubakar ya ce da son neman ƙarin bayani.
"Ina so ka ɗorani akan hanyar da zan yi amfani da ita domin na yi kira ga mutane waɗanda ba su farga da halin da muke ciki ba su ankara. Ina so ƙuncinmu da baƙincikinmu ya dinga yi musu amsa kuwwa a dodan kunnuwansu ta yadda har za su ji cewar ba su da wani buri face su taimaka mana."

Abubukar ya zube idanunsa kan Salisu da ke magana, yana yi masa wani irin kallo tare da yin shiru na wasu adadin sakanni.
    "Ka yi shiru, ba ka ce komai ba," Salisu ya ce.

Abubakar ya ɗan nisa kana ya ce, "Hanyoyi biyu ne a tunani na."
  "Waɗanne ne ke nan? Sanar da ni su."

"Ko dai ta'ammali da babbar waya wacca za ta iya sadakada kafafen sadarwa kamar su fezbuk, watsaf da sauran wuraren sadarwa. Ko kuma ka kasance ɗan jarida."

  "Mene ne aikin ɗan jaridar? Ta yaya zan iya zama shi?"

" Na san ba za ka kasa sanin abin da kalmar ɗan jaridar ke nufi ba? Kodayake, ɗan jarida na nufin mutum mai samo labarai yana yaɗawa a gidajen talibijin, rediyo ko kuma jaridu. Suna yin bincike ne da hira da mutane da tambayoyi wajen rubuta labaru da rahotanninsu. Ƙarin daɗawa kuma shi ne; samun cancantar ilimi, samun ƙwarewar da ta dace, shiga horo kan aiki da takaddun shaida da samun nasara shi ke saka wa mutum ya zama ɗan jarida. Sai dai ka sani da yawa 'yan jarida na samun kawunansu a haɗura, musamman ma wajen da ake samun rikicin ta'addanci ko fagen yaƙi. Sannan akwai rashin samun 'yancin yin aikin samo wasu rahoton a wasu ƙasashe. A wani binciken kwamiti mai kare 'yan jarida da na ci karo da shi a shafin internet ya yi rahoto in da yake bayyana cewa daga ɗaya ga watan Disamba, na shekarar dubu biyu da goma(01/12/2010) akwai 'yan jaridu ɗari da arba'in da biyar(145) da ke ɗaure a faɗin duniya. Ƙasashe goma waɗanda aka fi samun 'yan jarida a gidan kurku daga cikinsu akwai: Turkiya, Iran, da Ethopia. Wannan shi ne ɗan jarida da kuma irin hatsarin da yake fuskanta wanda gane hakan sai shi kansa ɗan jarida."

   "Ina son zama cikakken ɗan jarida. Tsawon wani lokaci zan ɗauka kafin na zama haka?" Salisu ya ce.

"Kana son zama ɗan jarida duk da haka Salisu?" Abubakar ya tambaye shi cike da fuskar mamaki.

  "Ƙwarai ina son zama ɗan jarida, domin ta nan ne kawai zan iya bayyana wa al'umma irin baƙin halin da muke ciki."

"Ba zan ce maka haka ba shi da kyau ba. Domin kyakkyawan tunani ne mai bayar da kyakkyawan gobe. Sai dai ina so ka sani kafin ka zama ɗan jarida cikakke wataƙila annobar da ke damunku ta nashe duka ƙauyen naku. Zai fi maka kyau ka fuskanci gobenka kawai ba tare da ka janyo sauran reshen da zai ƙarasa jijjige sauran rayuwarku ba."

Wani irin kallo Salisu ya jefa wa Abubakar kafin ya kai ga furta,
"Me kake nufi da haka? Kana nufin na daina abin da nake yi na son taimakon 'yan'uwana ?"

"A'a ko ɗaya. Ina nufin dai ka ajjiye batun zama ɗan jarida ka riƙe waya wacca ta nan ma za ka iya aiwatar da abin da kakeso ka kuma gina kyakkyawar gobenka." 

"Ta ina zan fara? Ta ina kuma zan soma? Duk da cewa ni fankan fayau ne..."

  "Mene ne kuma fankan fayau?" Abubakar ya katse shi ta hanyar cilla masa tambaya.

   "Jahili mana wanda bai da sanin komai. Duk da cewa ban gama zamtowa duka ba. Sai dai yanzu na sake gasagata cewa 'ilimi hasken rayuwa ne', na sani da ace ina da cikakken ilimin da na yi nutso cikinsa da tabbas zan gina ingatacciyar rayuwata da ta 'yan ƙauyenmu. Ta yaya zan soma? Alhalin ban taɓa riƙe babbar waya ba? Na san kuma dole sai da ita haka zai kasance."

Abubakar ya saki wani guntun murmushi kana ya ce,  "Idan har ka aminta da haka to ina mai tabbatar maka da cewa duk wannan mai sauƙi ne, zan nuna maka komai." 

"Duk da haka ina son na yi karatu ko don na yi fatali da jahilcin da ya yi mini ƙawanya," cewar Salisu yana sake kallon Abubakar.
"Hakan yana da matuƙar kyau Salisu."

Babu wanda ya sake cewa da ɗan'uwansa komai. Hasalima tuni Salisu ya dulmiya cikin kogin tunanin da ya zame masa tamkar numfshinsa da idan bai shaƙa ba zai iya samun tasgaro. kowane lokaci jinsa yake idan bai yi tunani game da ƙauyensa ba ba zai sami nutsuwa kota misƙala zarratan ba.

***
  ZUHRA

Daidai ƙofar gidansu mai napep ɗin ya sauketa. Tana ƙoƙarin shiga ta ji saukar muryar da ko kaɗan bata ƙaunar jinta cikin kunnuwanta ta yi mata dirar mikiya babu shiri ta faɗa magudanar jinta.

   "Maraba lale da zuwa gimbiyar mata"

Tsuke fuska tayi, ta ɗaureta tamau tamkar magaribar ɗinya, murmushin da ke wanze saman fuskata tuni ya ƙaurace mata, cike da gadara da izgilanci take binsa da wani ƙaskantaccen kallo.

  "Wai kai wane irin maye ne haka? Wace iriyar daƙiƙiyar ƙwaƙwalwa gareka da bata ɗaukar abin da aka kitsa mata? Na tabbata ko dusa tafi ka ja, domin ita idan an shanya zata bushe kai kuwa ko kaɗan baka gane abin da ake nufi da kai, ban san yaushe zaka gane bambancin da ke tsakanina da kai da nake ƙoƙarin sanar maka ba? Ko da yake ba laifinka ba ne laifin wannan annakiyar dauɗar talaucin dake jikinka ce, domin babu shakka ita ce ta haifar maka da makakkiyar dauɗar dake cikin ƙwaƙwalwarka wacce tasa ta toshe fahimtarka da ganewarka da har sai an ta maimata maka kalamai ko da yaushe."

Ta ɗan zuƙi numfashi, ba tare da ta ba shi damar magantuwa ba ta yi saurin sake furta,

   "Wallahi! Wallahi summa tallahi ka fice daga harkata idan ba haka ba sai na sa ka kasa gane bambancin da ke tsakanin maɗi da zuma, kuma sai na saka an maka lahanin da sai ka gwammaci kiɗa da karatu."

Sam ko kaɗan ko kusa kausasan kalamanta bai sa yaji wani ɗar a zuciyarsa ba, balle ko a saman shimfiɗar fuskarsa hakan ya nuna. Sai ma murmushin da ya sake suɓuce masa saman faffadar fuskar tasa. Kyakkyawane sosai zubin fulani, ba shi da wata makusa illa kawai halin ƙaƙaniyar da suke ciki shida iyayensa na rashi, sai dai duk da kyawun da Allah ya zuba masa bai sa hakan yayi tasiri a zuciyar Zuhra ba balle ta kalle shi a matsayin wanda za ta so har ma ta aura, don tace kyau babu kuɗi banza ne a banza.

  "Idan har a haka kike kallona to ki ci gaba da kallona a haka, domin na riga na zama kurma akanki na kuma zama makaho bana ji bana gani, ba na gane duk wasu zantukanki ni dai abu ɗaya na sani shi ne ina sonki Zuhra kuma har abada ba zan daina sonki ba ko tantama bana yi zan mutu da soyayyarki don Allah ki soni ko da ba har cikin zuciyarki ba ne." Ta tsinkayo kalamansa daf da zata faɗa cikin gidansu. A ƙufule ta juyo, ta soma zabga masa harara, cikin yatsina baki tamkar wacce tayi arba da ɗanyen turoso ta soma magana,

  "Tur da bauɗaɗɗen halinka wallahi, tur da tosasshiyar ƙwaƙwalwar da ke wanze cikin kwanyarka, ka riƙe soyayyarka ko kaɗan bana da muradinta, sanin kankani ni ba kalar 'ya'yan malam shehu ba ce, bari ka ji ka san Allah da na aureka gwara na mutu banyi aure ba, gwara na ƙare rayuwata a haka, koda ace zaka zame min ƙarfen ƙafa sai na san yadda na yi na yi jifa da kai gefe guda, ba zan taɓa bari ka rusa min mafarkina ba, ka je can ka nemi daidai kai amma ba Zuhra ba."
Chapter 8 · 0% Book details